dailytrust

Amfani da tagwayen wasula da rabin wasali

Salihu Maqera simakera@dailytrust.com

ATagwayen wasula ko masu aure

ci gaba da darasinmu na qa’idojin rubutu, yau za mu duba wasu kurakurai ne da ake yi a lokacin amfani da tagwayen wasula ko rabin wasali a yayin rubutu da Hausa:

A yayin rubutu da Hausa ana amfani da tagwayen wasula ko wasula masu aure. Kuma waxannan wasula guda biyu su ne ‘ai’ da ‘au.’ Sava qa’ida ce a yi amfani da gajeren wasali a madadin tagwai ko wasali mai aure. Kamar yadda (Wurma:2005) ya kawo wasu misalan da za mu iya qari a kai kamar haka:

Kuskure

temako qose kibo nushi meta fefe lema

Daidai

taimako qosai kibau naushi maita faifai laima sheda shaida reni raini tseko tsaiko baca bauca tsotsayi tsautsayi tosayi tausayi sorayi saurayi Shexan Shaixan shoqi shauqi luje lauje tora taura taloci talauci Mero Mairo Megero Maigero kome komai qeqayi qaiqayi Medugu Maidugu meqo maiqo me jego mai jego mareniya marainiya me gemu mai gemu

Akwai misalai irinsu da dama da mai karatu ko mai rubutu zai riqa cin karo da

su a rubuce-rubucenmu na yau da kullum da suka wajaba mu gyara don su dace da ingantacciyar Hausa mai bin qa’idojin da masana suka ajiye.

Amfani da rabin wasali

Baya ga tagwayen wasula ko wasula masu goyo kamar yadda masana suke kiran su. Akwai kuma rabin wasali wanda ake amfani da shi a yayin rubutu da Hausa. Shi ma wannan vangare ana samun masu keta qa’idojin rubutun Hausa a lokacin da suke rubutu, in ma saboda rashin sani ko kuma don neman burgewa.

Wurma (2005) ya ce: “Akwai wasu harrufa masu matsayi biyu, wato baqaqe kuma wasula. Waxannan kuwa su ne, ‘w’ da ‘y.’ Ana kiran su da suna ‘rabin wasula ko kinin wasali’ saboda dangantakarsu da wasu wasula na Hausa guda biyu ta fuskar furuci da kuma aiki. A kan haka ne waxannan baqaqe na ‘w’ da ‘y’ suka yi kama da wasulan ‘u’ da ‘i.’

Dangantaka ta qut-da-qut da take tsakanin waxannan baqaqe da waxannan wasula da kuma tasirin Ingilishi sun sanya waxansu mutake sukan kasa bambance baqaen da wasulan. Ba wannan ma ba, dangantakar ta sanya mutane sun kasa fane wuraren da qa’idar rubutun Hausa ta yarda a yi amfani da waxannan baqaqe da wasula.

Alal misali, daidai ne a rubuta waxannan kalmomi kamar haka: aiki ba ayki ba

MAKARANTA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281968906935543

Media Trust Limited