dailytrust

Gurgun da ke bara xauke da Naira miliyan 37 a aljihunsa

Wani gurgu da aka yanke wa qafa, kuma yake tafiya da qafar roba da taimakon sandan guragu ya shiga hannun ’yan sanda sakamakon kama shi da aka yi yana bara xauke da tsabar kuxi Dala 81,000 (kimanin Naira miliyon 37.3) a cikin ƙafafun robar da yake tafiya da su.

Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba da kuma qasar da ya fito, ya shiga hannun ’yan sanda ne a birnin Dubai, ya kuma shiga Haxaxxiyar Daular Larabawa ce da takardar bizar ziyara, inda aka kama shi a ranar Alhamis 16 ga Maris 2023 xin da ta gabata, yana bara a masallatai da wuraren shaqatawa kamar yadda jaridar Gulf News ta ruwaito.

’Yan sandan suna zargin mabaracin gurgun da yin qarya, kasancewar an samu tarin kuxin voye a cikin qafarsa ta roba duk da yake yana nuna cewa shi mubuqaci ne da ke neman taimakon jama’a.

Rundunar ’Yan sandan Dubai da ta yi kamun ta gargaxi jama’a da kada su ruxu da mabarata da suke qirqirar dabaru daban-daban don neman tausayawarsu.

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281998971706615

Media Trust Limited