dailytrust

Mutumin da ya qi karvar kyautar miliyoyi da lambar zinare

Lambar yabo ta Sarki Faisal tana xaya daga cikin lambobin yabo masu daraja a duniya, inda kowa ke burin samu, musamman malamai da musu aikin da’awa a faxin duniya. Lambar ta marigayi Sarkin Saudiyya Faisal bn Abdul’aziz, baya ga tsabar kuxi da ake ba wanda ya same ta, tana da qima da daraja da martaba a idon duniya.

Wanda ya aka tava ba wannan lambar yabo ya kuma qi karba a tarihi shi ne Sheikh Muhammad Hamidullah Al-Haidar

Abady Al-Hindy wani malami xan aslin qasar Pakistan, wanda mutane sama 40,000 suka musulunta a hannunsa a qasar Faransa da kewayenta, a shekara 50 da ya yi a cikinta.

Shehun malamin yana jin harsuna 22, harshe na qarshe da ya koya shi ne harshen Thai na qasar Thailand, a lokacin yana da shekara 84 a duniya.

Wani abin mamaki dangane da malamin shi ne bai tava yin aure ba a rayuwarsa, ilimi kawai ya aura da kuma kiran mutane zuwa ga addinin Musulunc, sai Allah ya yi wa aikinsa nasa albarka; saboda ya rubuta litattafai sama da 450 a harsuna daban-daban, kuma ya fassara litattafai da maqaloli sama da 937 daga harsuna daban- daban.

A rayuwarsa ta duniya ya nuna ba ya buqatar matar da za ta yi masa hidima. Domin da kansa yake yi wa hidima don biyan buqatun kansa na yau da kullum, kamar wanke kayan sawa da kwanukan cin abinci da sauransu, bai yarda wani ya yi masa haka ba, ko cikin xalibansa duk da irin ilimi da xaukakar da Allah Ya ba shi a wannan yanki.

A lokacin da ya samu kyauta da lambar yabo mafi qololuwa ta Pakistan, daga hannun marigayi Firayi Minista Muhammad Ziya’ul Haq, kan gudunmawar da ya bayar a vangarori da dama musamman vangaren addini da tarihi, kai-tsaye ya bayar da kyautar kuxin da ya samu ta hanyar lambar yabon ga wata makarantar koyar da ilimin addinin Musulunci a Islamabad, a lokacin kuxin sun kai kimanin Rupee miliyan xaya, a lokacin ne ya faxi wata magana mai qayatarwa wacce tarihi ya taskace ta, inda ya ce: “In na karvi wannan kyautar a wannan duniya mai qarewa, ban san me zan samu na lada kuma a wancan gida na Lahira ba, wanda yake matabbaci ba.”

Haka ma a 1994 da aka ba shi kyautar gimamawa da lambar yabo ta Sarki Faisal shenun malamin qin karva ya yi, yana mai cewa “Ni ban rubuta abin da na rubuta ba, face saboda Allah, ku qyale ni kada ku lalata min addinina.”

Sheikh Muhammad Hamidullah Al-Haidar Abady Al-Hindy, ya rasu a shekara ta 2002, yana da shekara 94 a duniya.

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282007561641207

Media Trust Limited