dailytrust

Kiwon fakara a zamanance don neman riba

Daga Yakubu Liman

Fakara tsuntsuwa ce mai qaramin jiki wacce kuma ake kiwo kamar yadda ake kiwon kaji da kuma zabi. Kiwon wannan tsunsuwa da wasu ke kira Salwa ma’abociyar daji, yana da fa’ida da kuma riba idan an yi shi yadda ya kamata, domin tsuntsuwar na buqatar kulawa kamar kajin gidan gona da Talatalo da kuma Agwawa.

Za ka iya soma kiwon Fakara a lokacin zafi ko sanyi, ko kuma da rani ko damina, babu wanda zai zama matsala ga lafiyarta, ba kamar wasu nau’in tsuntsayen gida da ake kiwo ba.

Naman Fakara da qwanta nada daxi, kuma za su taikawa musu fama da cutar sukari watau diyabetis. Qwan Fakara shi kaxansa ya fi na kaza amfani a jikin xan adam, saboda yana xauke da sindarin furotin da fosforus da ayon da bitamin A da B1 da kuma B2 fiye da qwan kaza.

Kiwon Fakara ba ya buqatar kuxi mai yawa da zai xaga wa farin shiga hankali. Za ka iya kiwon Fakara tare da Kaji a lokaci guda domin samar da qwai ko nama

Yanayin halittar Fakara ba ta girma

Fakarar da ta kai matuqa a girma ba ta wuce nauyin giram 150 zuwa 200, qwanta kuma ba ya wuce nauyin giram 7 zuwa 15.

Macen Fakara na soma yin qwai ne daga makwanni 6 zuwa 7 da haihuwa, ta kuma cigaba da saka qwai a kullum.

Ta kan yi qwai 300 a shekarar farko na rayuwan, daga baya kuma sai su yi 150 zuwa 175 a shekara ta biyu. Sai kuma sakin qwan ya ja baya a hankali a bayan shekara ta farko na fara yin qwan.

Qwan Fakara na da matuqar amfani ga lafiyar dan adam, saboda yana xauke da kashi 2.47 ragi na kitsen da ke cikin qwan kaji. An kuma yi ittifaqin cewa qwan na maganin kamuwa da hawan jini kuma yana taimkawa masu fama da fama da cutar sukari.

Fakara ba ta qyanqyasar qwanta, sai dai kai ka qyanqyashe da inji ko kuma ka sa wa kaza ko awagwa mai kwanci ta qyanqyashe.

Yanayin rayuwa

Tsawon rayuwar Fakara ba ya wuce shekaru uku ko huxu. Fakara mai shekaru da yawa bata wuce nauyin giram 150 zuwa 200. Ba kamar qwan sauran tsuntsaye ba, qwan Fakar na da kyan gani saboda adon da Allah Ya yi masa qawa na dabbaredabbare, kum haske na sa Fakara ta riqa yin qwai a kai, a kai. Hakan nan kuma Fakara na yin qwai ne da maraice, kuma qwan kwana 17 kacaal ya ke yi a qyanqyasa.

Wurin zama

Kula da Fakara yayin kiwonta mai sauqi ne, kuma shirya musu wurin kwana abu ne mai sauqi, tun da tsuntsaye ne marasa girman jiki, za a iya

haxa su dabbobi da kuma wasu tsuntsaye dabbobin na kiwo. Za kuma ka iya ajiyesu don sha’awa saboda suna da kyau wajen kallo da kuma sa nishxi.

Hakanan kuma Fakara bata buqatar wuri mai faxi, saboda yanyin halittarsu idan aka kwatanta su da kaji, za ka iya kiwonsu a wani xan wuri karami a bayan gidanka, ko kuma cikin xan lambun gidanka da ba zai yiwo a yi kiwon kaji ba.

Wurin da za ka saka Fakarar da ka ke son kiwo na da matuqar muhimmanci don haka yana da kyau ka yi la’kari da waxannn shawarwari yayin tunanin inda za ka yi kiwonsu a sarari ne ko a keji.

Za ka iya kiwon Fakara a cikin keji da kuma a killace a fili. Sai dai kiwon nasu a keji ya fi kiwon nasu a fili. Domin a cikin Keji za ka iya ba su kulawar da ya kamata, kuma da akwai qarancin yiwuwar kamuwarsu da wata cuta.

Ka tanadar musu da hanyar da za su riqa samun isasshiyar iska da kuma haske a inda ka tanada.

Za ka iya zuba Fakara kimanin 50 a wuri xaya, sai dai wurin kar ya gaza santi mita 120 a tsawo, santimita 60 a faxi, kar kuma tsawonsa ya gaza santimita 25.

Yi amfani da raga ta waya a kejin da za ka zuba su, awon ragar kuma ya kasance milimita 5 tsawo da kuma faxi.

Kejin roba shi ya fi dacewa da kiwon Fakara domin riba.

Keji ya kasance yana inda wata dabba ba za ta iya cimma musu ba.

Muhimman kayan aiki

Kamar sauran dabbobi, ita ma Fakara na da buqatar wasu abubuwan da zai sa su ji daxi. Ga wasu daga cikin muhimman kayayyakin buqatun da zai su taimaka wajen nasarar lafiyar abin kiwonka

Mazubin ruwa

Fakara na buqatar qaramin muzubin ruwa, la’akari da girman jikinsu. Kar kuma mazubin ya zama mai zurfi ko kuma mai girma. Ya kasance wanda za su iya shan ruwan ba tare da haxari na faxawa ciki ba. Sannan ka tabbata ruwan na tsafta.

Mazubin abinci

Ka ajiye mazubin abinci isasshe daidai da yawan Fakarar da ka ke kiwo ta yadda za su iya kai wa ga mazubin abincin da kuma ruwa ba tare da wahala ba. Qananan shuke-shuke Ka samar da wasu ‘yan tsirrai a cikin inda ka ke kiwon Fakara wani abu ne mai kyau, idan kiwon a keji ka ke yi, ko kuma a sararin da Fakarar take. Idan a sarari kake kiwon, zai taimaka musu sosai, kasancewar Fakarar mai son kai-komo ce, waxannan tsirrai za su taimaka musu qara sakin jiki da jin daxin yanayin da yayi kama da inda suka saba na halitta. Amma a tabbata cewa tsirren ba masu guba ba ne da ka iya cutar da su.

Wajen vuya

Yana da kyau Fakarar da ka ke kiwo su sami wani xan wurin vuya, za ka iya sa musu wani xan bututu ko mazurari a cikin keji ko sararin da ka ke kiwo. Hakan zai taimaka musu qwarai wajen samun walwalar wasan vuya da suka saba.

Rairayi

Xaya daga cikin abubuwan da za su taimaka wa Fakarar da ka ke kiwo shine ‘xan rairayin da za su riqa burgima ciki lokaci zuwa lokaci. Samar da wannan a inda ka ke kiwo a sarari ko kuma keji, zai taimaka matuqa wajen yin maganin quma da sauran qananan qwarin da ke addabarsu, wanxand ke sa su yi burgima a rairayi a bisa al’ada domin magani. Sai dai yana da kyau a nesanta wurin burgimar da mazubin ruwa ko na abinci, saboda zu su iya vata wurin matuqa da ruwa ko abinci.

Tsaftar keji

Yana da kyau a riqa tsaface Keji ko kuma wurin da ake kiwon Fakara aqalla a sau xaya ko biyu a mako. Tsaftace kejin ko sararin da ake kiwon zai yi maganin qwayoyin cuta manya da qanana da ka iya haddas rashin lafiya. A wanke shimfixar kejin da mazubin abinci da kuma na ruwa. Sannan a sake musu rarayin da suke birgima a ciki da kuma ruwa da abincin da suka daxe a cikin mazuban nasu. Sannan a tabbatar da wadataccen haske ga tsuntsayen.

Fakara na buqatar wadataccen hasken da ya kai na sa’oi 15 a rana. Haka kuma Fakara na buqatar isasshen barci idan ana so su zauna cikin qoshin lafiya. Sannan yana da kyau ka kashe wutar kejin bayan kimanin waxannan sa’oi, ko a matsar da su zuwa wuri mai duhu domin su samu su yi barci idan lokaci yayi yadda ya kamata.

Hayaniya da hauragiya

Yi qoqari ka samarwa Fakarar da ka ke kiwo yanayi maras hayaniya. Wannan ya haxa da kawar da dabbobin gida irin su karen mai yawan haushi da kuma awaki da tumaki masu koke-koke, idan a xaki ne, ko makamncin haka saboda kar su takura musu da koke-koke da haushi.

Xibar qwai a kullum

Domin ka riqa samun qwai lafiyayye, kamata ka riqa kwashe qwan da suka yi a kullum musamman a ranakun da ake cikin yanayin zafi. Za ka iya jiye qwayyen a cikin firinji ko kuma a cikin kwali ka kuma ajiye su a wani wuri daban. Amma ajiye qwan a cikin firinji zai sa su kasance cikin lafiya da inganci na tsawon lokaci. Za ka iya samun qwayaye 5 ko 6 a kowanne mako daga tamatar Fakara.

Kiwon lafiya

Yana da kyau ka sa ido akan lafiyar Fakararka akai-akai. Idan ka ga kiwonka da wata baquwar xabi’a, ko kuma ba sa cin abinci yadda ya kamata, babu mamaki babu lafiya ne. Sai ka yi qoqari ka yi maganin matsalar da kan ka, ko kuma idan ba za ka iya ba, ka nemo likitan dabbobi.

Ruwa

Baya ga samar da abincin da ya dace kuma mai inganci ga Fakararka, ka tabbata ka samarwa kiwon naka isasshen ruwa mai tsafta kuma wadatacce a duk lokacin da suke buqata.

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282016151575799

Media Trust Limited