dailytrust

Farashin kaya tsakanin kuxi hannu da taransifa a Katsina

Daga Ahmed Kabir S/ Kuka, Katsina

Tun daga lokacin da aka bayar da sanarwar canjin launin wasu takardun kuxi a Najeriya jama’a suka shiga cikin wani halin quncin rayuwa, ba ma kamar a Jihar Katsina wadda ke fama da matsalar tsaro ta fuskoki biyu. Fuska ta farko ta varayin daji sai kuma fuska ta biyu daga jami’an tsaro kasancewar jihar tana iyaka da Jamhuriyar Nijer. Baya ga rashin samun kuxin hannu, sai ga shi an wayi gari hatta bankunan da ake zaton samun kuxin abin ya gagara. Kamar yadda wasu daga cikin masu neman kuxin daga bankuna suka shaida mana, bankunan ne suka yi bayanin cewa babban bankin qasar ne CBN bai kawo masu kuxin ba duk kuwa da batun hukuncin kotun qoli akan ci gaba da amfani da tsofaffin kuxin. Wannan batu ya qara ta’azzarar da al’amurra musamman ga masu harkokin kasuwanci bama kamar na abinci domin an samu ragowar sayen kayan qyale-qyale da sauran kayan da ba wajibi ba.

‘Yan kasuwa sun raba farashin kayan su zuwa kashi biyu. Misali, masu sayen shinkafar waje idan kuxi hannu ne kuma sabbin da aka kawo, to za’a sayar da buhu akan Naira dubu 27,amma idan taransafa ne, Naira dubu 32. Batun su gero ko masara da sauran irin su, ba kowane xan kasuwa ne zai amshi taransafa, sai dai kuxi lakadan. Ganin ana musayar kuxin sefa na Nijer, in za’ayi canjin kuxin, ana sayar da jikka guda ta sefa akan Naira xari 7 wani lokaci da hamsin. Amma idan taransifa zaka yiwa mutumin can Nijer, to duk jikka guda akan Naira dubu da xari 120 har zuwa da xari 2. Wani abin da ya qara xaurewa masu sayayya ta hanyar banki kai ita ce, injin POS na xan kasuwar ne, amma kuma idan kayi sayayya sai ya qara wani caji acikin jimlar kuxin da kayi sayayyar wai da sunan cajin POS.

Daga cikin matsalolin da ake fuskanta, za a iya yin sayayyar Naira dubu 5 har zuwa 10 amma ka ce xan kasuwar ya ba ka Naira dubu ko xari 5 abin ya gagara saboda rashinsu.

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282024741510391

Media Trust Limited