dailytrust

Tsarin Kashles ya jefa masu kiwon kaji a mawuyacin hali

Daga Hussaini Isah, Jos

Ayayin da al’ummar Najeriya suke ci gaba da fuskantar wahalhalu, sakamakon shirin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na sauya fasalin takardun kuxi tare da taqaita amfani da takardun kuxin (Kashles), Aminiya ta binciki gidajen kiwon kaji inda ta gano cewa masu gidajen kajin sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon wannan shiri.

Aminiya ta gano cewa, a halin yanzu masu gidajen kajin ba sa samu masu sayen qwan da suke fitarwa, don haka da dama ba sa iya sayen abincin da suke bai wa kajin.

Da yake zantawa da Aminiya, Alhaji Abdullahi Baba mai gidan kiwon kaji na Strong Confidence Poultry Farm (SCPF) da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna ya ce, suna da kaji sama da dubu 10 a gonar da suka buxe a 2021.

Ya ce, a yanzu suna fuskantar babban qalubale, sakamakon shirin kashles a qasar nan.

“A yanzu mu masu kiwon kaji, mun zama abin tausayi saboda rashin abinci. Kajinmu sun zama ababen tausayi domin kamar yadda xan Adam yake ramewa, sakamakon yunwa haka kajinmu suke yi. Wannan abu ya faru ne sakamakon wannan sauyin kuxi da kuma takaita amfani da takardun kuxi.

Masu sayen qwai yanzu abin da za su ci shi ne ya dame su,” in ji shi.

Alhaji Abdullahi Baba ya yi bayanin cewa, aqalla a kowace rana kajinsu suna cin masara buhu 40. Kuma idan kajin suka yi qwai yau, shi ne za a xiba a sayar a saya masu abincin da za su ci.

“Yau kwananmu 10 ba mu sayar da qwai ko kiret xaya ba, sakamakon rashin ciniki da ake fama da shi. Waxanda muke sayen abincin kaji a wajensu, suna tausaya mana su ba mu bashin abincin kajin. Yanzu ta kai ga mun qure su, kajin sun

cinye musu jari. Muna neman wanda zai zo ya sayi qwai ko bashi ne, amma ba mu samu. Idan wannan abu ya ci gaba, nan da kwana 10 ko mako biyu kajin za su fara mutuwa saboda yunwa.

A yanzu mun zuba wa sarautar Allah ido kan halin da muke ciki. Don haka muna kira ga gwamnati ta dawo da kashi 60 na takardun kuxin, su riqa zagawa a tsakanin jama’a ana walwala, domin mu riqa samun abin da za mu saya wa kajin abinci,” in ji shi.

A zantawa da Aminiya, wani mai kiwon kaji mai suna Alhaji

Gambo Mai Kaji Saminaka ya ce, su masu kiwon kaji, suna ganin kamar don su aka fito da wannan shiri na taqaita amfani da takardun kuxi a Najeriya.

Ya ce, tun da suka fara wannan gona ba su tava shiga mawuyacin hali irin haka ba. Qwan da kajinsu suke yi, suna da wuraren da suke kaiwa su raba wa masu sayarwa, amma yanzu ta kai duk wuraren da suke kai qwan, sai su tarar su ma suna da qwan saboda rashin ciniki. Kuma babban abin da yake ba su matsala shi ne qwai abu ne da yake lalacewa.

Ya ce, “A yanzu mun tara qwai mun rasa yadda za mu yi da su. Ga shi yanzu ana yawo da shi a gari, kiret har Naira dubu xaya ana sayarwa, abin da muke sayarwa a da Naira dubu biyu. Wasu gonakin har sun fara kwashe kajinsu suna sayarwa”.

Alhaji Gambo ya ce, ciyar da kajin da suke kiwo ya zama dole kuma vangaren abincin kajin shi ma babu sauqi domin farashinsa bai sauka ba, wannan ya sa suke cikin tsaka-maiwuya.

Ya ce, “Yanzu farashin buhun masara kuxi a hannu ya kai Naira dubu 17 zuwa 18. Idan za ka tura kuxi ta banki ya kai Naira dubu 20 zuwa dubu 21 kuma babu yadda za a samu kuxi a hannu. Yanzu kamar ni, ban san yawan bashin qwan da nake bi ba.”

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282050511314167

Media Trust Limited