dailytrust

Nazari da sharhin littafin Tarihin Annabawan Musulunci

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

AThe Prophets of Islam

Sunan Littafi:

Sunan Marubuciya: Hauwa Yusuf Kazaure

Kamfanin Wallafa: Refirst Shekarar Wallafa: 2023

Yawan Shafuka: 34

Farashi: Naira 3,000

rayuwar xan Adam, babu wani abu da ya kai qimar ilimi, domin kuwa da shi ne ake gudanar da kowane al’amari na duniya. Da ilimi ne ake samar da abinci da sarrafa shi, da shi ake mu’amala tsakanin mutum da mutum kuma da shi ne ake mulki, ake samar da duk wasu abubuwan da ke taimakon xan Adam ya rayu. Ilimi ne ke jagorancin sarrafa tunanin mutum, yadda zai zama mai amfani ga kansa da sauran al’ummun duniya.

Saboda muhimmancin da ke tattare da ilimi, shi ya sa Allah Ya umurci manzonSa Muhammadu (saw) da ya nemi ilimi (karatu), musamman ma shi ne umurni na farko da ya fara ba shi, ma’ana ita ce aya ta farko da aka fara saukar masa. Shi ma Manzon Tsira, ya yi ta sanar da al’umma muhimmancin ilimi da neman sa.

Haka ma muhimman mutane da suka yi fice a duniya, duk ta sanadiyar ilimi ne kuma dalili ke nan suka yi ta bayyana tasiri da muhimmancin ilimi a lokuta daban-daban na rayuwarsu. Misali, da yake bayyana muhimmancin ilimi, Malcolm X yana cewa: “Ilimi shi mabuxin nasarar rayuwar gobe, domin kuwa nasarar mutum a gobe tana hannun waxanda suka shirya mata a yau.”

Ita ma fitacciyar ’yar jarida, Oprah Winfrey ta ce: “Ilimi shi ne mabuxin da ke buxe qofofin duniya. Shi ne kuma katin shaidar samun ’yanci.”

To amma ta yaya ake samun ilimi? Babu shakka, babbar hanyar da ake samun ilimi, ita ce ta hanyar karatu. To tun daga wane lokaci ya kamata mutum ya fara neman ilimi? Ilimi ana neman shi ne tun daga zanen goyo har zuwa qarshen rayuwa. Dalili ke nan ma aka ruwaito Manzon Allah (saw) yana cewa: “Hadda (neman ilimi) ga yaro, kamar rubutu ne bisa dutse amma hadda (neman ilimi) ga babban mutum, kamar rubutu ne bisa ruwa.” Wannan ke nuna mana cewa mutum tun yana yaro qarami ya kamata a ladabtar da shi da neman ilimi, domin idan aka bari ya girma, sannan zai nemi ilimi, to zai fuskanci matsala.

Muhimmancin ilimi da bunqasa shi ga al’umma, na daga dalilan da suka sa Malama Hauwa Yusuf Kazaure ta rubuta wannan muhimmin littafi na Tarihin Annabawan Musulunci. Ta rubuta shi musamnman domin inganta tarbiyyar yara, domin su tashi daxabi’ar karatu - neman ilimi. Haka kuma ta zavi maudu’i mai muhimmanci tarihin annabawa. Sanin kowa ne cewa Allah Ya aiko annabawa ne ga al’umma domin su zama jagorori, masu shirya mutane zuwa ga hanyar qwarai.

Wannan littafi na The Prophets of Islam, an tsara shi da inganci, xauke

da tarihin mashahuran annabawa goma sha huxu, daga cikin guda 25 da Allah Ya ambata a cikin Alqur’ani mai girma. Haka kuma, an yi amfani da kalmomi masu sauqin fahimta, musamman ga yara, kamar kuma yadda aka inganta dukkan shafukan littafin da hotuna masu kyau, xauke da kaloli mabambanta.

Da farko, marubuciyar ta fara kawo tarihin mutum na farko da Allah Ya fara halitta, wato Annabi Adamu (as). Ta bayyana dalilin halittar sa da wurin da ya fara zama, kafin a sauko da shi duniya da kuma dalilin ma da ya sa Allah ya sauko da shi duniya. Haka kuma ta bayyana yadda aka yi ya hayayyafa har ta kai ga a yau mutane suka mamaye duniya.

Tarihin annabi na biyu a littafin, shi ne Nuhu (as), wanda ya shekara xari tara da hamsin yana wa’azi ga al’ummarsa amma qalilan ne suka yi imani. Wannan yana koya wa yara illar kafirci da kangarewa daga gaskiya, kasancewar tun a duniya Allah Ya hukunta su, ta hanyar saukar masu da mamakon ruwa, ya halaka su.

Na uku, shi ne Annabi Hudu (as), wanda aka aiko ga al’ummar Adawa, waxanda suka kasance masu qarfi, masu dukiya, sai dai kuma sun cika girman kai da kuri da tsaurin ido. Wanda haka ya sa Allah Ya halaka su da guguwa. Wannan tarihi yana jan hankalin yara da su kasance masu sauqin kai, masu biyayya, domin kauce wa fushi da azabar Allah.

Annabi na huxu da aka bayyana tarihinsa a littafin nan, shi ne Ibrahim (as), wanda saboda taurin kan mutanensa, suka haxa babbar wuta suka jefa shi ciki, da nufin babbaka shi. Allah da ikonSa ya tseratar da shi. Wannan babban darasi ne ga yara, da su kasance masu tsoron Allah da dogaro da shi, cewa zai kare su daga dukkan wani da ke nufin cutar da su.

Na biyar, shi ne Annabi Isma’il (as), wanda bisa umurnin Allah mahaifinsa Ibrahim (as) ya bar shi da mahaifiyarsa a sahara, babu ruwa ko abinci. Allah Ya kare su daga dukkan matsalar rayuwa kuma Ya huwace masu ruwan Zamzam. Shi ne kuma ya kasance mai biyayya ga umurnin Allah, inda ya amince mahaifinsa ya yi layya da shi. Allah ya fanshe shi da wata dabba, wanda dalili ke nan ma a yau al’ummar Musulmi suke layya da dabbobin ni’ima a kowace Idin Babbar Sallah.

Na shida a jerin littafin nan, shi ne Annabi Yaqubu (as), wanda ya kasance mai ilimi, mai tsoron Allah. Shi ne ya haifi ’ya’ya goma sha biyu kuma dukkansu annabawan Allah. Cikinsu har da Annabi Yusuf (as).

Na bakwai, shi ne Annabi Yusuf (as), wanda aka zayyana tarihinsa mai ban mamaki, yadda ya kasance a kurkukun qasar Misira da yadda ya kasance mai hikima da basirar fassasa mafarki da kuma yadda a qarshe ya samu martaba da xaukaka saboda gaskiya da riqon amana.

Na takwas shi ne Annabi Ayyuba (as), wanda ya kasance attajiri kuma mai cikakkar lafiya kuma mai ’ya’ya amma Allah Ya jarabce shi da karayar arziqi da rashin lafiya. Ya kasance mai haquri mai yawan ibada. Daga bisani Allah ya mayar masa da dukiyarsu da lafiyarsa da kuma yawan ’ya’ya. Tarihinsa na kwaxaitar da yara da su kasance masu haquri.

Na tara shi ne Annabi Musa (as), wanda Allah Ya huwace wa mu’ijizozi. Ya kasance wanda ya raba kogi da sandarsa, ya tseratar da mutanensa, sannan ya yi sanadiyyar halakar Fir’auna, wanda ya kasance azzalumi mai cutar al’ummarsa.

Annabi na goma da aka zayyano a littafin nan, shi ne Dawuda (as), wanda ya yi galaba a kan qaqqarfan mutum, Jaluta, wanda ya riqa zaluntar mutane.

Ya kasance wanda Allah Ya hore wa ilimin sarrafa qarfe da hannunsa.

Na goma sha xaya, shi ne Annabi Suleiman (as), wanda Allah Ya hore wa sarautar da ba a tava ba wani mutum irinta ba. Ya kasance mai sarautar mutane, aljanu da dabbobi da tsuntsaye. Yakan ba kowace irin dabba ko tsuntsu ko aljani umurni kuma dole su bi.

Na goma sha biyu, shi ne Annabi Yunusa (as). An kawo tarihinsa mai ban mamaki, yadda ya samu kansa a cikin kifi kuma ya rayu, Allah Ya kuvutar da shi.

Na goma sha uku, shi ne Annabi Isa xan Maryama (as), wanda aka haifa da uwa amma babu uba. Allah Ya ba shi mu’ijizozi iri-iri, kamar tayar da matattu, warkar da makafi, kurame da kutare da izinin Allah.

Na goma sha huxu kuma na qarshe, shi ne Annabi Muhammadu (saw), wanda shi ne Manzon Allah mafi haquri, mafi soyuwa ga al’umma, wanda ya kasance wanda aka fi ambato. Shi ne manzon da Allah ya aiko wa dukkan al’ummar duniya.

Ina yabawa da jinjina ga marubuciyar littafin nan, Malama Hauwa Yusuf Kazaure, bisa qoqarinta na rubuta littafin nan, wanda ya tsaru sosai kuma aka wallafa shi musamman domin yara. Sai dai duk da haka, na tsinkayi wasu kurakurai da ya kamata a bugu na gaba, a gyara su. Na farko dai ya kamata a samar wa littafin Lambar Littafi ta Duniya (ISBN), haka kuma a sanya lambar shafi, domin kuwa an wallafa shi a matsayin kurma, sai dai mai karatu ya qidaya da kansa.

Babu shakka halayen qwarai na annabawa manyan abin koyi ne ga al’umma. Don haka, littafin babbar taska ce kuma jagora ne ga yara. Ina kira ga iyayen yara da makarantu da hukumomin ilimi da su sayi littafin nan kuma su wadata shi ga yara da xakunan karatu da cibiyoyin ilimi.

TARE DA YAKUBU LIMAN

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282059101248759

Media Trust Limited