dailytrust

Za a riqa tsayar da wasan Firimiyar Ingila domin buxa baki

Hukumar Qwallon Qafar Ingila ta sanar da cewa za a riqa tsayawa ana tsaka da wasa domin ba ’yan wasa Musulmi dama su yi buxa baki. Akwai ’yan wasa Musulmi da dama da suke taka leda a gasar, ciki hard a Ngole Kante na Qungiyar Chelsea da Mohammed Salah na Liverpool da Ikay Gundogan na Manchester City da sauransu.

Sai dai ba wannan ba ne karon farko, a wani wasa da aka fafata tsakanin Leicester City da Crystal Palace a kakar 2021 ma an yi hakan, inda rafaren wasan ya dakatar da wasan domin ’yan wasan su yi buxa kafin a cigaba.

WASANNI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282071986150647

Media Trust Limited