dailytrust

Ozil ya yi ritaya daga qwallo

(BBChausa)

Tsohon xan qwallon ayarin Jamus, Mesut Ozil ya sanar da yin ritaya daga taka leda. Tsohon xan qwallon Real Madrid da Arsenal ya rataye takalmansa ne yana da shekara 34 a duniya.

Ozil ya fara taka leda a Schalke 04 daga nan ya koma Werder Bremen, sai dai ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya da aka yi a 2010. A wasan ne ya fito da kansa, inda Jamus ta ci Ingila 4-1 a wasan Kwata-Fainal, hakan ya sa Real Madrid ta xauke shi.

A shekara ukun da ya yi a Spain ya dauki La Liga a qarqashin Jose Mourinho, daga nan Arsenal ta saye shi a matsayin mafi tsada a Emirates a shekarar 2013.

Ya taka rawar gani a qarqashin Arsene Wenger, amma sai Unai Emery bai samu dama ba, inda ya rasa gurbinsa a qarqashin Mikel Arteta.

Ozil wanda ya buga wasa tare da Arteta a Arsenal ya koma Fernerbahce a 2021.

Bayan wasa 32 da ya yi sai ya koma Istanbul Basaksehir, wadda ya yi wa karawa huxu kacal.

Ozil ya lashe Kofin Duniya a ayarin Jamus a 2014, sannan ya yi ritaya daga buga wa qasar wasa a 2018, bayan wasa 92 da ya yi mata.

WASANNI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282076281117943

Media Trust Limited