dailytrust

Shin an samu magadan Ronaldo da Messi?

Mbappe da Haaland:

Daga Isiyaku Muhammed

Afarkon kakar bana ce Qungiyar Manchester City ta xauko xan wasan gaba, Erling Haaland daga Qungiyar Dortmund ta qasar Jamus.

Yadda xan wasan ya yi kaca-kaca da Qungiyar Manchester United a makon farko da zuwansa Ingila ne ya sa magoya bayan qungiyar suke cewa lallai kakarsu ta yanke saqa, domin matsalarsu ta rashin zura qwallaye ta qare.

Tun lokacin Haaland ke ci gaba da cin kasuwarsa babu qaqqautawa a qungiyar, inda yake ta zura qwallaye yadda yake so.

A makon jiya ne ya zura qwallo uku rigis a ragar Qungiyar Burnley, inda qwallayensa suka kama 42 a wasa 37 da ya buga wa Qungiyar Manchester City, ciki har da qwallo biyar da ya zura a ragar Qungiyar RB Lepzig a wasan Gasar Zakarun Turai.

A qasarsa ta Norway kuwa, xan wasan ya zura qwallo 21 a wasa 23 da ya buga tun shekarar 2019 da ya fara wakiltar qasar yana xan shekara 19.

A vangaren Mbappe kuwa, xan wasan yana tashe matuqa, wanda hakan ya sa kocin qasar Faransa, Didier Deschamps ya naxa shi a matsayin kyaftin xin qungiyar yana xan shekara 24 duk da cewa akwai manyan ’yan wasa a gabansa.

Daga cikin ’yan wasan da suke gaban xan wasan, akwai Griezman, wanda yanzu rahotanni ke nuna cewa zai bar taka wa qasar leda saboda ba Mbappe kyaftin.

Xan wasan ya zura qwallo 36 a wasa 66 da ya buga wa qasar Faransa tun shekarar 2017 da ya fara buga wa qasar ciki har da qwallo uku rigis da ya jefa a ragar Qungiyar Ajantina a wasan qarshe na Gasar Cin Kofin Duniya.

A vangaren wasannin qungiya, tun a kakar 2017 da ya je Qungiyar PSG a matsayin aro, xan wasan yake jan zarensa, inda zuwa yanzu yake da qwallo 138.

Wannan ya sa yanzu duniyar qwallo ta fara komawa kan ’yan wasan biyu. Sai dai tambayar da ake yi ita ce shin za su iya zama magadan Ronaldo da Messi? Shin za su iya daxewa suna jan zare irin nasu?

An daxe ana tafka muhawara a kan tsakanin Ronaldo da Messi wa ya fi wani, inda ake amfani da Kalmar GOAT wato Greatest Of All Time wajen bayyana wanda ya fi. Amma ko tantama a kan su biyun suna gaba da kowa ba a yi, domin an kasa samun wanda zai dusashe tauraronsu har ma ta kai ana tunanin ba a tava samun ’yan wasa ba kamar su a tarihin tamaula.

A baya, an yi zaratan ’yan wasa, tun lokacin su Johan Cruyff da Michael Platini da su Pele da Mardona har zuwa lokacin su Zinedine Zidane da su Ronaldo na Brazil da Figo da Rivaldo da suransu. Amma a tarihin qwallo ba a tava samun waxanda suka daxe suna zamani ba kamar Ronaldo da Messi musamman a shekara goma sha zuwa 20 da suka gabata domin da wuya ka ga xan qwallo ya yi shekara 10 tauraronsa bai dusashe ba ko kuma aqalla ya rage haske, amma su abin qara gaba yake yi, sai a kakar bara da aka fara ganin alamar sun fara yin qasa.

Alamar sanyinsu

Ronaldo ya bar Qungiyar Manchester United ya koma Qungiyar Alnassr ta Saudiyya, inda duk da cewa yana jan zarensa a gasar qasar, ana ganin alamar sanyi domin bai kamata ya koma taka leda a wajen Turai ba.

Haka ma rahotanni sun nuna cewa sai dai ya rasa babbar qungiyar da za ta xauke shi ne ya yanke shawarar tafiya Saudiyya.

A vangaren Messi, duk da ya lashe Gasar Kofin Duniya da Ajantina, ana ganin komawarsa Qungiyar PSG ta Faransa ba ta haifar da xa mai ido ba.

Kafin zuwansa qungiyar, suna lashe Gasar Ligue 1 ta qasar, inda babban burinsu shi ne lashe Gasar Zakarun Turai, amma ko a kakar bana a wasan farko na zagaye na farko ne aka yi waje da su.

’Yan wasan da Ronaldo da Messi suka hana tashe

Daga cikin waxanda tashen Ronaldo da Messi ya danne su, inda suka kasa lashe kyautar gwarzon xan wasa duk da cewa sun qware, akwai Xabi da Iniesta da Suarez da Torres da Buffon da Riberry da sauransu. Shi kansa Kaka, ba don Ronaldo da Messi da ya lashe sama da xaya.

Akwai kuma irin su Neymar da Griezman da su ma sun nuna qwarewa, amma yanzu shekarunsu sun ja ba tare da sun lashe kambin ba, har sun fara tunanin ritaya, alhalin su Messi da Ronaldo suna ci gaba da taka leda.

WASANNI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282084871052535

Media Trust Limited