dailytrust

2023: Zave ya qare!

Muna godiya ga Allah Maxaukakin Sarki da Ya nuna mana wannan lokaci lami lafiya. Alhamdulillah an yi zave an gama, tun daga na Shugaban Qasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Qasa da aka gudanar mako uku da suka gaba da kuma na gwamnoni da na majalisun jihohi da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Kafin zaven an yi ta fargabar tashin hankali zai iya varkewa a lokaci da bayan zave, amma cikin ikon Allah da qaddarawarSa, ko da aka gudanar da zaven Shugaban Qasa babu wani rahoton tayar da hankali da ya nuna sakamakon zaven ya bar baya da qura na jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sai dai abu ne sananne cewa jama’a da dama ba su samu fitowa zaven ba. Wataqila wannan na da alaqa da yadda aka riqa bayar da rahotannin cewa za a iya samun tashin hankali yayin zaven a wurare da dama. Idan muka dubi adadin mutanen da suka yanki katin zave da adadin waxanda suka yi zaven, za mu ga cewa mutane da dama ba su fito zaven ba. Da a ce dukkan waxanda suka yanki katin zave sun fito sun jefa quri’a wataqila da wasu da suka ci zave a yanzu ba su zasu yi nasara ba. Amma galibi mutane masu shekaru a kusan ko’ina ba su fita zave ba, matasa da samari ne suka yi zave a kusan ko’ina a Najeriya.

Wannan kuma dalili ne da ke nuna cewa har yanzu akwai sauranmu a siyasa. Domin zaven nan ba a sake yin sa sai bayan shekara huxu, lallai al’umma su sani wannan zave shi ne yake nuna sauyin gwamnati a kawo shugabannin da za su jagoranci wannan qasa, kuma su ne suke da wuqa da nama da alhakin tafiyar da harkokin ilimi da kiwon lafiya da batun noma da kiwo da tsaftar muhalli da uwa- uba tsarawa da inganta batun tattalin arziki a Najeriya. Don haka batun shugabanci ba abu ba ne na wasa da za a bar shi a hannun matasa kawai, muna buqatar dattawa da masu ilimi da za su yi wa al’umma hangen nesa su xora su a kan layin da ya dace.

A rashin samun saiti, ya sa da yawan matasa kawai suna bin rububi ne da yayi. Da farko za su duba su ga wane xan takara ake yayi a inda suke, ko wace waqa ce aka yi wa wani xan takara da ta yi daxi, ko kuma wa suke ganin duk inda ya nufa su ma za su nufa, ko kuma cikakkun ’yan siyasa su ce jam’iyyarsu kawai suke so ta kai labari ko da wa aka tsayar takara. Wannan yana da illa matuqa domin da irin haka ne ake samun baragurbin mutane suke kaiwa ga madafun iko saboda waxanda suka zave sun rufe sun yi zave ba su yi la’akari da waxanda za su iya fitar da jama’a daga cikin mawuyacin hali zuwa kyakkawan yanayi ba. Irin wannan ke sa wasu su zo da jakar kuxi su ci zave, ba tare da sun zauna cikin al’ummar da suke son shugabnta sun san matsalolinsu ba.

A irin wannan lokaci da siyasar take sake yin tsada, su jam’iyyun siyasa ba ruwansu da cancantar mutum, kawai suna duba wa yake da kuxin da zai iya kashewa, ya yi wa jamiyya hidima kuma ya yi wa ’ya’yan jamiyya hidima.

Da dama daga cikin jam’iyyun da doron bayansu ake takawa a kai ga kowane irin mataki, za ka su ma wannan ce manufarsu, ba wai mutum aqili mai natsuwa da xa’a da zai iya cire wa mutane kitse daga wuta ba.

Kodayake yanzu wannan zance da muke lokacinsa ya riga ya wuce, tun da an yi zave an kammala. Abin da ya kamata dukkan zavavvu su mayar da hankali shi ne yadda za a kyautata rayuwar al’umma. Musamman waxanda suka ci zaven gwamnoni, muna kira a gare su da su ji tsoron Allah su sakar wa qananan hukumomi mara kuma su ba su kuxaxensu domin su yi wa al’umma ayyukan raya qasa da za su ciyar da karkara gaba. Lallai wannan shi ne zai ciyar da wannan qasa tamu gaba, a ce kowane shugaban qaramar hukuma yana samun kuxinsa kai-tsaye kuma ya yi sarrafa su yadda ya dace domin ciyar da yankinsa gaba.

Bayan haka, muna kira tare da fata cewa gwamnonin da suka yi nasara za su shirya zaven qananan hukumomi a lokacin da ya dace, kuma su bari a yi sahihin zave, kamar yadda da yawansu zave ne ya kawo su ba qarfa-qarfa ko kama-karya ba. Wannan zai sa jama’a su samu aminci da natsuwa cewa shugabannin za su yi wa al’umma ayyukan da suka kamata domin ganin an hidimta wa al’umma da ayyukan da suka kamata. Sanin kowa ne cewa qananan hukumomi su ne suka fi kowa kusa da al’umm, kuma su ne nan da nan ake gabatar musu da matsalar al’umma su xauki mataki ba vata lokaci, wannan ya sa qananan hukumomi suke da matuqar muhimmanci ga al’umma.

Muna fata a wannan lokacin a dawo daga rakiyar tsohon tunani na cinye-duk da ake yi wa majalisun qananan hukumomi. Wannan ne zai nuna cewa al’umma sun waye kuma dimokuraxiyya ta samu zama da gindinta, domin qarfa-qarfa da kamakarya ke janyo tashin hankali da zubar da jini a siyasa, a koyaushe fata muke a mutunta ra’ayin al’umma mafiya rinjaye, abin da duk mutane suke so ko suke nema shi ya kamata a ba su, domin da a ce qarfa-qarfa da kamakarya suna da hurumi da wasu masu mulkin ba su faxi ba a jihohinsu, da wasu masu mulkin yaransu ba su faxi zave ba a inda suka tsayar da su. Amma masu mulki sun tsayar da ’yan takara an kada su kuma sun karva, to ya kamata Gwamnan da aka zava shi ma ya bayar da dama al’umma su zavi shugabannin qananan hukumomi da za su yi musu aiki kuma suke ganin su ne suka dace da muradunsu domin samar da ci gaba.

Daga qarshe muna fata dukkan mutanen da suka ci zave su xauka ba wayonsu da dabararsu suka ba su ba. Allah ne Ya zave su ba don su ji daxi su fantama su hau sabuwar mota ko sanya sabuwar riga kullum ba, Allah Ya zave su ne domin su yi wa al’umma aiki, idan sun yi abin da ya dace za su kuvuta har gaban Allah, amma idan sun butulce su sani Allah Yana nan Yana jiran kowa a madakata. Allah Ya ba su ikon sauke nauyin al’umma da ke kansu.

WASANNI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282093460987127

Media Trust Limited