dailytrust

Sulhun Iran da Saudiyya da rawar da China ta taka

Aranar 10 ga watan Maris 2023 ne qasashen Saudiyya da Iran suka sanar da amincewa su sake qulla hulxar diflomasiyya sakamakon shiga tsakani da qasar China ta yi. A qarqashin sulhun, Riyadh da Tehran sun amince su sabunta haxin gwiwar tsaro da suka rattaba wa hannu a 2001 da kuma na kasuwanci da tattalin arziki da saka hannun jari da suka rattaba wa hannu a 1998.

Haka kuma za su buxe ofisoshin jakadanci da tura jakadunsu nan da wata biyu. Ana sa ran Riyadh za ta cire takunkumin da ta qaqaba wa Iran da qulla kasuwanci da kuma hana Isra’ila kai hari kan masana’antar nukiliyar Iran.

Hakazalika, ana sa ran sulhun zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma yayyafa wa tarzomar da ke faruwa a Yemen ruwa, duba da cewa Iran ta amince za ta daina iza wutar harin Houthi a kan Saudiyya da yankin, musamman a Siriya da Lebanon. Yaqin sunquru tsakanin qasashen guda biyu ya yi mummunan tasiri a kan Yemen sakamakon tallafin soji da Saudiyya ta ba ta, lamarin da ya haifar da tavarvarewar al’amura a qasar.

A ranar 3 ga Junairun 2016 ne qasar Saudiyya ta yanke alaqar diflomasiyya da Iran, bayan lalacewar alaqar da ke tsakaninsu sakamakon mamaye Ofishin Jakadancin Saudiyya a Tehran da masu zanga-zanga suka yi saboda kisan da Riyadh ta yi wa mutane 47 saboda samunsu da ta’addanci waxanda suka haxa da malamin Shi’a, Nimr al-Nimr da kuma mai aqidar alqa’ida Fares al-Shuwail

Sulhu da dawo da alaqar sun biyo bayan tattaunawar da aka yi a ranar 6 zuwa 10 ga Maris 2013 a Beijing. Sai dai an ci gaba da aiki tare da rattaba hannu bayan shafe shekara biyu ana tattaunawa.

Sakatare Janar na Majalisar Xinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi maraba da sulhun, inda ya yaba wa qoqarin qasashen da suka taka rawa, musamman qasar Oman da Iraqi. Su ma qasashen Faransa da Jordan da Pakistan da Kuwait da Bahrain da Turkiyyya sun yi maraba da sulhun.

Ita ma Fadar White House wadda ta sha zargin nuna halin ko-in-kula a kan abin da yake gudana a Gabas ta Tsakiya, inda ta ba wa Beijing damar qulla kyakkyawar alaqar diflomasiyya a yankin, ta ce qoqarin China na ‘‘daqile qaruwar hatsaniya’’ a yanakin bai yi hannun riga da buqatar Amurka ba.

Sulhuntawar tana da matuqar muhimmanci, saboda ba iya taimakawa wajen kawo qarshen hatsaniya da daidaita al’amura a yankin za ta tsaya ba, qasashen biyu za su haxa qarfi da qarfe wajen sake fasalin sayar makamashi ta yankuna da kuma wadatuwar makamashin da ke da muhimmanci a cikin buqatun da ake da su a duniya.

Rawar da China ta taka wajen sulhunta Iran da Saudiyya ta nuna cewa, China ta tashi daga matsayin mai tasiri a yanki zuwa ta duniya. Haka kuma dama ana jin tasirinta daga Afirka zuwa Kudu da Tsakiyar Asiya da Gabas ta Tsakiya da kuma Latin Amurka.

A bayyana yake cewa, China tana amfani da dabaru wajen jawo hankalin qasashe gare ta ba amfani da qarfi ba da sauransu, inda ta zama mai qima kasancewarta na mai sasantawa ba mai qarfa-qarfa ba.

Yin wannan muhimmin sulhu a tsakanin qasashen biyu masu bambancin aqida da manufofin yanki, China ta ciri tuta a Gabas ta Tsakiya a matsayinta na babbar mai shiga tsakani, inda hakan ke nuna qwarewarta duk kuwa da cewa wuri ne da Amurka take da tasiri

Jaridar Aminiya na yaba wa China bisa sulhunta waxannan qasashe da kuma nuna cewa akwai hanyoyin warware matsaloli baya ga yaqi. Don haka, muna kira ga qasashen su kiyaye sharuxan wannan sulhu. Ya kamata su yi amfani da sulhun wajen tabbatar da cikakken shiri maimakon baya-baya da juna. Sannan ya kamata China ta tabbatar kowace qasa ta cika sharuxxan sulhun.

Idan ta yi haka, to tabbas ta ci nasara wajen da Amurka ta gaza. Saudiyya ita ce babbar qasar Larabawa da ke abota da Amurka, yayin da ita kuma Iran ita ce babbar abokiyar adawa a yankin.

Jaridar Aminiya tana kira ga Saudiyya da Iran su yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da sulhun

Mu ma muna maraba da ci gaba da aiki tare, domin kuwa sasanta manyan qasashen yankin zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya sannan ya yi naso a sassan duniya.

Haka kuma, dole ne Saudiyya da Iran su fahimci cewa, su ne fa shugabannin Musulmin duniya, sannan nasarar ci gaba da wannan mu’amala zai taimaka wajen rage rabuwar kai tsakanin Shi’a da Sunni a Gabas ta Tsakiya da kuma duniya baki xaya.

Muna kira ga manyan qasashen duniya su kawo qarshen rashin jituwa ta hanyar yin sulhu maimakon xaukar vangare, lamarin da ke rura wutar tashin hankali kamar yadda ya faru da tashin hankalin da ke faruwa a Ukraine.

Dole ne China ta tabbatar ba ta yi irin kuskuren da manyan qasashen duniya suka yi ba, ta hanyar shiga siyasar Gabas ta Tsakiya, kamar yadda Yankin Fasha ya zama babban wurin da manyan qasashen duniya suke gasa.

Wataqila wannan shi ne lokacin da Amurka da sauran manyan qasashen duniya za su koyi darasi xaya zuwa biyu daga China, musamman wajen shiga tsakani da yin sulhu. Saboda China tana da kyakkywar alaqa da kowace qasa da ke Gabas ta Tsakiya, wanda hakan ya sa kowace qasa ke zaman lafiya da Beijing.

A xaya vangaren kuma, Amurka na da alaqa ta musamman da wasu qasashen, yayin da kuma ba ta ga maciji da wasu (kamar Iran). Wannan ya sa masu adawa da juna suka kasa sulhutawa.

WASANNI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282110640856311

Media Trust Limited