dailytrust

Yadda ake shirye-shiryen tarbar Buhari a Daura

Daga Tijjani Ibrahim da Ahmed Kabir S/Kuka, Katsina

Garin Daura, mahaifar Shugaban Qasa Muhammadu Buhari mai barin gado, na cikin shagali mai kama da na jajibirin bukukuwan Sallah, inda mazauna garin ke shirin tarbar xansu wanda wa’adin mulkinsa na shekara takwas zai qare a gata Litinin 29 ga Mayu.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci Daura a qarshen mako, an ga Sarkin Daura Dokta Farouq Umar Farouq a cikin wani yanayi na murna, inda yake dubawa da kuma bibiyar shirye-shiryen da ake yi kafin ranar 29 ga Mayu, 2023 domin tabbatar da dacewar tsare-tsaren da ake yi sun yi daidai da yadda ake buqata don bikin wannan tarba.

“Idan ba ku san Sarki ko abin hawansa ba, ba za ku san cewa shi ne ke zagayawa don ganin yadda abubuwa suke gudana ba. Wannan shi ne ya nuna irin muhimmancin da Mai martaba Sarki ke ba wa wannan zuwa na Shugaba Buhari gida,” kamar yadda wata majiya mai tushe daga masarautar ta bayyana.

Hawan Daba da sauran al’amuran al’ada da ake shiryawa

Domin tarbar Shugaban, Aminiya ta samo bayanai kan irin tanadin da Majalisar Masarautar Daura take yi, sannan a gefe guda, tana gudanar da wani gagarumin shiri na Hawan Daba don karrama Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado, kuma Bayajidda na II, tare da gudanar da sauran al’adun gargajiya irin su dambe da kokawa da sharo/ shaxi. Sarkin Daura Dokta Farouq Umar Farouq ya fara ba da labarin shirin Bikin Dabar a lokacin da Gwamnan Jihar Katsina mai barin gado Alhaji Aminu Masari ya kai masa ziyarar ban-kwana a fadarsa a makon jiya.

“Ina so in sanar da Mai girma Gwamna cewa, muna shirin gudanar da gagarumar daba domin tarbar xanmu kuma shugabanmu, Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, Bayajidda na II. Don haka ana gayyatar ku ko dai ku shiga a matsayin mahaya dawaki, kasancewarka mai riqe da sarautar Matawallen Hausa ko kuma a matsayin baqo na musamman,” in ji Sarkin.

Baya ga tsare-tsare da Majalisar Masarautar ta yi, Aminiya ta gano cewa gamayyar qungiyoyi na yin nasu tsarin, musamman tarba da kuma raka Shugaban zuwa gidansa.

Alhaji Aliyu Daura, Shugaban Qungiyar Ci -gaban Masarautar Daura (DEDA) ya ce, yawancin

’ya’yan qungiyar za su jira ayarin Shugaban Qasa a qauyen Xannakola, yayin da wasu manyan mutane za su kasance a filin jirgin sama na Umaru Musa ’Yar’aduwa, Katsina, domin tarbar Shugaban.

“Kamar yadda kuka sani idan Shugaban Qasa ya isa Katsina, mai yiwuwa ya yi amfani da jirgi mai saukar ungulu zuwa Daura, yayin da ayarinsa za su karvi baquncin ’ya’yan qungiyoyi daban-daban a Xannakola. Wasu kuma za su kasance a filin saukar jirgi mai saukar ungulu a nan Daura, inda Shugaban Qasar da iyalansa za su sauka domin raka su gidansa a ranar 29 ga Mayu, yayin da kuma za a gudanar da taron da masarautar ta shirya washegari,” in ji shugaban qungiyar.

Kamar yadda Aminiya ta samu takardar tsarin shirye-shiryen, za a fara shirin Hawan Daba ne da qarfe 8:00 na safe a ranar Talata 30 ga Mayu a Dandalin Kangiwa da ke Qofar Fadar Sarkin Daura. Mahalarta Hawan Dabar sun haxa da hakimai da dagatai da masu unguwanni da sauran mahayan dawaki, inda za su isa wurin da qarfe 8:00 na safe, yayin da Sarki da fadawansa za su kasance a zagayen qofar Sarki Abdurrahman da qarfe 8:30 na safe.

Ana sa ran dukkan manyan baqi za su halarci wurin da misalin qarfe 9 na safe. Wanda aka shirya wa taron, wato Shugaba Muhammadu Buhari, zai zauna da qarfe 10 na safe sannan za a fara gudanar da taron da qarfe 10 da minti 15 na safe har zuwa qarfe 12 da minti 15 na rana kamar yadda aka tsara.

Yadda aka sabunta gidan Shugaba Buhari

Bisa al’ada, shugabanni suna da zavi na inda za su zauna bayan sun bar mulki, inda za a iya gina musu sabon gida. Sai dai kuma a wajen Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, tsohon gidansa na Daura ne kawai aka yi masa fenti ba tare da gina wani sabon gini a ciki ba.

Tun kafin zavensa a 2015, Shugaba Buhari ya yi ta safa da marwa a tsakanin gidansa da ke Daura da na Kaduna, wanda ake kyautata zaton marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa ne ya ba shi. Haka kuma an yi gyara tun daga hanyar zuwa gidan nasa zuwa gidan da ke titin Sultan a Kaduna.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan na Daura, ya ga gidan ya yi kyau saboda sabon fenti da aka yi. Duk da cewa jami’an tsaron da ke qofar gidan sun hana shiga gidan da xaukar hotuna, wasu daga cikinsu sun tabbatar da cewa babu wani gagarumin gyara da aka yi a gidan sai fenti.

“Mun karanta a cikin rahotanninku (kafofin watsa labarai) cewa an ga ana kwashe manyan kaya a cikin manyan motoci daga fadar Shugaban Qasa zuwa nan gidan. To, ba mu gan su ba, wataqila har yanzu suna kan hanya,” in ji xaya daga cikin masu tsaron gidan ( ya faxa cikin zolaya).

Sai dai Aminiya ta lura cewa, an xauki wasu matakan tsaro domin kare unguwar Shugaban Qasar yayin da aka sanya shinge a dukkan hanyoyin da ke shiga gidan.

Dalilin da ya sa muke murnar dawowar Buhari gida - Jama’a

Wasu mazauna garin Daura sun bayyana farin cikinsu da kuma shirye-shiryen dawowar Shugaban Qasar gida a qarshen wa’adin mulkinsa.

Wani xan kasuwa, Alhaji Labaran Maiyadi Daura ya ce, “Muna godiya ga Allah Maxaukakin Sarki da Ya nuna mana qarshen Gwamnatin Janar Buhari cikin nasara da kwanciyar hankali.

“A gaskiya mun yi farin ciki kuma mun shaida abubuwan da suka faru ba a nan Daura kaxai ba, har ma a sauran wurare, kuma sama da komai, zaman lafiya ya dawo ga al’umma.’’

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya ji daxin, Maiyadi ya ce: “Mutum ne da ya yi rashin lafiya a lokacinsa na farko, ya tafi qasar waje neman magani, inda wasu suka yi fatar ya mutu a can, amma Allah cikin rahamarSa Ya dawo da shi da rai, har ma ya qara masa wani wa’adi wanda yake kammalawa cikin nasara.

“Abin da muka yi a wancan lokacin shi ne addu’a a gare shi, ba a nan Najeriya kaxai ba, har ma da maqwabtanmu a Jamhuriyar Nijar, sun yi masa addu’ar samun lafiya. Muna godiya gare su, domin na yi Sallar Juma’a da dama a Nijar inda suka yi addu’o’in samun lafiya.”

Shi kuwa Aminu Muhammad Daura ya ce, xaukacin garin na farin ciki da dawowar Buhari, inda ya ce Shugaban ya yi ayyuka da dama domin ci gaban garin. Ya ce, a yanzu Daura na da duk wani abu da iyalan Shugaban Qasa suke buqata domin su rayu cikin kwanciyar hankali, ta fuskar tsaro da sauran abubuwan more rayuwa. Kuma ya ce zai iya jira ya yi wannan murnar dawowar Shugaban Qasar.

Lawal kuwa cewa ya yi, “Tunda aka kafa Daura shekaru da dama da suka gabata har zuwa yau, tsohon birnin bai tava ganin sauye-sauye irin wanda aka samu a zamanin mulkin Buhari a matsayin Shugaban Qasa ba. Idan ka xauki kowane vangare a Qaramar Hukumar Daura, za ka ga an samu wani sabon abu a qarqashinsa.”

Wasu muhimman ayyukan da aka yi a Daura a zamanin Shugaba Buhari

A wa’adinsa na shekara takwas, Daura ta samu Jami’ar Sufuri da Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya (Federal Polytechnic) da Asibitin Sojojin Sama na Qasa (Nigerian Air Force Reference Hospital) da Asibitin Mata da Yara da Makarantar Naqasassu da Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (Air Wing) da hanyoyin gari da magudanun ruwa da ayyukan ruwa.

Sauran sun haxa da Bataliya ta 171 ta Sojojin Najeriya da sansani na musamman na sojojin Najeriya da ingantawa da faxaxa filin wasa na Daura da Cibiyar Samar da Dabarun Ci-gaba Mai Xorewa da kammala madatsar ruwa ta Sabke da ke samar da ruwa ga Daura da maqwabta da samar da layin wutar lantarki mai tsawon kilomita 73 da qarfin .9$ daga Katsina da taransfoma biyu 30 da 40 09$ domin inganta wutar lantarki da kuma layin dogo na Kano zuwa Maraxi da ke bi ta cikin garin Daura.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281522230459360

Media Trust Limited