dailytrust

Dalilin da mutane suka fara ‘hukunta’ masu qwacen waya a Kano sanda

Ba daidai ba ne—’Yan

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

An xauki kimanin shekara biyu al’ummar Jihar Kano suna fuskantar matsalar qwace ko fashin waya inda vatagari waxanda yawancinsu matasa ne masu qananan shekaru suke tare mutane suna qwace.

Rahotanni sun ce ba wai qwacen waya waxannan matasa ke yi ba, sukan yi amfani da makamai masu wajen raunata mutanen da suka qwace wa wayar kafin ko bayan sun qwace musu. A wasu lokutan ma sukan kashe mutanen.

Duk da cewa masu qwacen wayar sun fi gudanar da mummunan aikinsu a cikin dare akan samu ire-iren wuraren da ake gudanar da qwacen wayar da rana ido na ganin ido.

Wannan matsala ta zama ruwan dare domin zai yi wuya a samu iyalin da ba su tava xanxanar wannan abin takaici na qwacen waya ba. Idan kai ba a yi maka ba to an yi wa wani naka.

Kuma masu qwacen wayar suna da salo-salo kan yadda suke gudanar da aikinsu inda wasu ake qwace musu waya a yayin da suke tafiya wasu kuma a qwace musu wayar a lokacin da suka hau keken nan mai qafa uku.

Aminiya ta ruwaito yadda mutane da dama suka sha da qyar a hannun masu qwace wayar, inda suka tsira da raunuka.

‘Yadda aka qwace mana waya’

Wata mai suna Zainab Yusuf ta ce tana kan hanyarta ta zuwa aiki sai ta ga wani keke mai qafa uku ya zo kamar zai wuce ta kusa da ita. “Ban yi aune ba, sai na ji an fisge jakata. Sai na kai hannu zan karve jakar sai xaya daga ciki ya sa wuqa ya sare ni a hannu. Nan na faxi cikin jini kafin daga bisani jama’a su kawo kin xauki inda aka kai ni asibiti,” in ji ta.

Wani da ya tava shiga hannun ’yan qwacen wayar ya ce, “Ina cikin keke mai qafa uku, to na samu wasu a ciki. Ban sani ba ashe tare suke da direban. Muna cikin tafiya sai direban ya riqa yin wani irin tuqi. Sai ya zama muna yin sama da qasa. Ya zama ni da wanda ke kusa da ni muna haxuwa da juna. Ashe ban sani ba a wannan lokaci wanda ke zaune kusa da ni ya sa hannu a aljihuna ya xauke min waya. Sai da na sauka ina qoqarin xauko kuxi in ba wa direban sai kawai na ga ya ja keken cikin sauri. A lokacin na gane cewa sun xauke min waya.”

A baya-bayan nan

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya ce ’yan sanda za su riqa gurfanar da waxanda aka kama da laifin qwacen waya a matsayin ’yan fashi da makami.

Kuma a ranar Talatar da ya faxi haka ne aka samu wasu matasa sun qone wani babur xin masu qwacen wayar bayan da suka tsare wasu mutane suka karve musu waya.

Wata ganau ta shaida wa

Aminiya cewa, “Masu qwacen wayar sun taho ne daga titin Rijiyar Zaki, bayan da wani daga cikin mutanen da suka qwace wa waya ya yi ihu ne mutane suka yi qoqarin kama su inda suka cika wa wandonsu da iska suka tsallake suka bar babur xin.”

Kwamishinan ya yi haka ne domin samun sauqi lamarin ta hanyar firgita matasan, domin zaman gidan yari mai tsawo ne laifin fashi da makami.

Me ya sa aka fara xaukar doka a hannu?

Sai dai duk da wannan furuci na Kwamishinan ’Yan sandan da kamen da ’yan sanda suka riqa yi, matsalar tana ci gaba da ci wa mutane tuwo a qwarya, wanda hakan yake fusata mutanen gari.

A kwanakin baya an riqa sanya hotunan waxanda masu qwacen waya suka kashe, inda

Aminiya ta ga hotunan sama da 20 da ake yaxawa a Facebook, sai dai Aminiya ba ta tantance sahihancin hotunan da lokacin da aka kashe su ba.

Sai dai waxannan hotuna sun qara tunzura mutane, inda suka fara cewa ya kamata a fara xaukar doka a hannu ana hukunta su.

A qarshen makon jiya wasu matasa a Unguwar Qofar Kabuga suka qone wani babur mai qafa uku a qoqarinsu na xaukar fansa a kan wasu matasa da suka yi qoqarin qwacen waya a hannun wani matashi bayan matasan da ake zargin sun tsere.

Xaya daga cikin matasan Qofar Kabuga ya shaida wa Aminiya cewa, “Waxannan matasa sun yi qoqarin qwace wayar wani matashi a nan unguwar, Allah Ya sa ya yi ihu, hakan ya ja hankalinmu muka zo wurin don kai masa xauki, sai dai kafin mu zo sun riga sun gudu sun bar babur xinsu a wurin. Hakan ya sa muka qone babur xin.”

A cewar matashin da sun samu masu qwacen wayar, “Wallahi da sai mun qone su qurmus. Kuma wallahi ko gobe wasu suka sake shigowa unguwarmu za su qwace mana waya, to wallahi sai mun qone su kamar gawayi,” in ji shi.

Da yake bayyana dalilinsu na xaukar wannan mataki ya ce, “Lura da cewa hukuma ba ta xaukar mataki a kan masu qwacen wayar ya sa muka ga cewa mu da kanmu za mu riqa hukunta su.”

A ranar Litinin da ta gabata ma an samu irin hakan a Kuka

Bulukiya a Qaramar Hukumar Dala inda wasu matasa suka yi wa wasu masu qwacen waya dukan kawo wuqa.

Haka a ranar Talatar da ta gabata an samu rahoton cewa matasa suka qone babur mai qafa uku a daidai Shatalelen Asibitin Nasarawa daidai lokacin da aka biyo su bayan sun yi fashin waya a kan Titin Qofar Kudu, Gidan Sarki.

A qarshe an yi nasarar kama matasan inda aka yi musu dukan kawo wuqa har ana zargin xaya daga cikinsurai ya yi halinsa.

Rahotanni sun ce tuni aka iza qeyar sauran zuwa ofishin ’yan sandan Kano.

Xaukar doka a hannu ba daidai ba ne-’Yan sanda

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce duk da cewa masu qwacen wayar laifi suke aikatawa, amma xaukar doka da mutane ke yi da kansu ba daidai ba ne.”

“Idan mun duba masu qwacen waya laifi suka aikata, amma abin da mutane suka fara yi na xaukar doka a hannu ba daidai ba ne, kuma mu a Rundunar ’Yan sanda ba ma maraba da wannan lamari.

“Idan muka kama duk wanda ya xauki doka a hannu za mu yi masa hukunci daidai da laifin da ya aikata,” in ji shi.

SP Kiyawa ya musanta zargin da jama’a ke yi cewa ba sa hukunta masu qwacen waya, inda ya ce, “Ba gaskiya ba ce mutane su fito su ce ba mu hukunta masu qwacen waya domin al’umma shaida ne kusan kullum muna kama waxannan mutane kuma muna kai su kotu. Kowa ya san yadda ake gudanar da shari’a ba wai kawai daga zuwa ake yanke musu hukunci ba, dole sai alqali ya bi komai daki-daki kafin ya kai ga yanke hukunci. Abin farin ciki shi ne a yanzu Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano ya fitar da doka cewa duk wanda aka kama da qwacen waya to za a yi masa shari’ar masu fashi da makami ne.”

A wani taron manema labarai Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Muhammad Usaini Gumel ya yi nuna wasu matasa kimanin 65 waxanda ake zargi da laifin qwacen waya a jihar. Haka kuma Kwamishina Gumel ya yi baje-koliin wasu makamai kimanin 150 da ya ce an same su ne a hannun matasa masu qwacen wayar.

Xaukar doka a hannu ba zai haifar da xa mai ido ba-Barista Abba Hikima

A bayanin Barista Abba Hikima Fagge, lauya mai fafutikar kare haqqin xan Adam a Jihar Kano ya ce xaukar doka a hannu da mutane ke yi ba abu ne mai kyau ba, kuma ba zai haifar wa al’umma xa mai ido ba.

“Duk da cewa masu qwacen waya laifi suka aikata amma hakan ba zai zama hujja ga al’umma su rama abin da ake yi musu ta hanyar xaukar doka a hannunsu ba, domin hakan ya sava wa doka. Ba zai yiwu a warware laifi da aikata wani laifin ba,” in ji shi.

Malam Usman Abba, malamin addinin Musulunci a Jihar Kano ya ce addini ya yi hani ga mutane su xauki doka a hannunsu.

“A gaskiya addinin Musulunci ya yi hani a kan xaukar doka a hannu. Duk wanda ya yi maka wani abu na laifi kamata ya yi ka kai qararsa gaban hukuma don a bi maka haqqinka. Idan kuma ka xauki doka a hannunka to babu shakka ka aikata abu na laifi,” in ji shi.

Wata qungiya mai yaqi da shaye-shaye a Jihar Kano ta gudanar da taron wayar da kai a kan yadda gwamnati da al’umma za su magance matsalar qwacen waya a tsakanin al’umma.

Shugabar Qungiyar Zainab Nasir Ahmad ta ce, “Dole ne gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shawo kan al’amuran tsaro a faxin jihar. Haka kuma su ma jama’a su daina fito da waya fili a lokacin da suke tafiya a bainar jama’a.”

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281530820393952

Media Trust Limited