dailytrust

Qarin kux in Hajji: Hukumar Hajji ta yi amai ta lashe

Daga Faruq Shu’aibu da Sagir Kano Saleh

Hukumar Hajji ta Qasa (NAHCON) ta lashe amanta bayan alqawarin da ta yi cewa maniyyatan Najeriya ba za su biya qarin Dala 250 da aka samu kan kuxin kujerar Hajjin bana daga aljihunsu ba.

Savanin alqawari da tabbacin da hukumar ta ba maniyyatan a baya, a ranar Litinin ta sanar da cewa yanzu za su biya cikon Dala 100.

Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Hassan Zikrullahi, ta hannun Mataimakin Daraktan Yaxa Labaran Hukumar, Mousa Ubandawaki ya ce, qarin Dala 100 maniyyatan za su biya daga cikin qarin Dala 250 da aka samu, a yayin da gwamnati da kamfanoni jirage kuma za su xauki alhakin cikon.

Ubandawaki ya ce, bayan qarin Dala 250 da aka samu, gwamnati ta yafe musu Dala 55, wanda ya sa kuxin kujerar ya ragu zuwa Dala 195.

“Yanzu kowane mutum daga cikin maniyyata 75,000 zai biya cikon Dala 117,” in ji Ubandawaki.

Amma ya ce, maimakon maniyyata su biya kuxi daga alhjihunsu, hukumar za ta cire Dala 100 daga kuxin guzurinsu a matsayin cikon kuxin kujerar, sai a ba su Dala 700 a matsayin kuxin guzuri.

Ya ce, cikon Dala 17 kuma NAHCON ta roqi kamfanonin jirage su yi wa maniyyatan rangwame, saboda su ma ba yin su ba ne aka rufe sararin samaniyar qasar Sudan.

Ya qara da cewa idan har aka buxe sararin samaniyar Sudan kafin fara jigilar maniyyatan, to za a mayar musu da kuxaxensu da aka cire.

Yaqin da ake yi a Sudan ya hana shawagin jirage a sararin samaniyar qasar, inda kuma ta nan ne jiragen alhazan Najeriya suka saba bi zuwa qasar Saudiyya.

Rufe sararin samaniyar Sudan ya sa dole sai jiragen sun sauya hanya, wanda zai qara yawan sa’o’in da za su xauka da

kuma yawan qasashe da za su bi kafin isa Saudiyya.

A kan haka ne kamfanonin jiragen sama masu jigilar maniyyatan Najeriya suka nemi qarin Dala 500 a kan kowace kujera, amma a qarshe suka daidaita da Hukumar NAHCON a kan Dala 250.

Da farko Hukumar NAHCON ta ce za ta yi bakin qoqarinta wajen ganin maniyyatan ba su biya qarin daga aljihunsu ba. Amma daga bisani ta ce gwamnati ta biya musu wani vangare, za su biya Dala 100, da za a cira daga kuxin guzurinsu, maimakon su yi ciko; yayin da kamfanonin jirage kuma za su yi musu ragin Dala 17.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281548000263136

Media Trust Limited