Sojoji sun kashe mayaqan ISWAP a Yobe
Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu Super Tucano.
2023-05-26T07:00:00.0000000Z
2023-05-26T07:00:00.0000000Z
Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281556590197728
BABBAN LABARI
Wasu hare-hare da jiragen yaqin sojojin saman Najeriya suka kai sun qashe mayaqan ISWAP da ba a tantance adadinsu ba a yankunan Turo da Ambiya na Qaramar Hukumar Gujba da ke Jihar Yobe. Majiyar tsaro ta ce, sojojin saman da suke sintirin leqen asiri sun samu nasarar kashe ’yan ta’addar ne a yammacin ranar Litinin bayan jirgin saman yaqin ya kai hari a matsugunnin mayaqan. Majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, mai sharhi kan yaqi da ta da qayar baya da harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa an kai harin ne ta sama bayan binciken da sojojin suka gudanar. A cewar Makama, binciken ya nuna wasu manyan motocin masu xauke da bindigogi guda takwas na jigilar mayaqa zuwa wani wuri da ake kyautata zaton hari suke da qudirin kaiwa. Bayanai sun ce, da yawa daga cikin mayaqan sun hallaka sakamakon harin ta sama da sojin suka kai musu da sababbin jiragen yaqi na
ha-ng