dailytrust

Buhari ya buxe titin Kano zuwa Kaduna da Gadar Neja II

Daga Sagir Kano Saleh

Kwana shida kafin saukarsa daga mulki, Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya qaddamar babban titin Kano zuwa Kaduna da kuma katafariyar Gadar Neja ta II da wasu manyan ayyukan raya qasa guda shida.

A ranar Talata Shugaba Buhari ya kuma qaddamar da sabon ginin Hedikwatar Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke Abuja, sannan ya qaddamar da sauran manyan ayyukan guda shida ta Intanet a sassan Najeriya.

Ya qaddamar da manyan ayyukan ne a yayin da yake jagorantar wani zama na musamman na Majalisar Zartarwa ta Qasa a Fadar Shugaban Qasa.

Fitattu da ayyukan da Shugaba Buhari ya qaddamar su ne titin Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 200, wanda gwamnatinsa ta gyara da kuma Gadar Neja ta Biyu, wadda aka fara shekara 16 da suka gabata, kuma aka sanya mata sunansa.

Su biyun na daga cikin manyan ayyuka bakwai da Gwamnatin Buhari ta kammala da suka haxa da gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya guda uku da manyan gadoji uku da kuma aikin titin.

Ginin Sakatariyar Gwamnatin Tarayyar su ne wadda ke Awka, hedikwatar Jihar Anambra da aka fara a watan Disamban 2011.

Sauran gadojin sun haxa da ta Loko zuwa Oweto, wadda ta ratsa Kogin Binuwai ta haxe jihohin Binuwai da Nasarawa; da kuma gadar Ikom da ke Jihar Kuros Riba.

Sakatariya ta biyu ita ce wadda ke Gusau a Jihar Zamfara da aka kammala a watan Nuwamban 2022, sai wadda ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, wadda aka bayar a 2011, aka kammala a watan Nuwamban 2022.

A watan Fabrairun 2023, Buhari ya qaddamar da ginin Sakatariyar Tarayya da ke Lafiya, hedikwatar Jihar Nasarawa.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281565180132320

Media Trust Limited