Kutsen sojoji a Jami’ar ATBU ya bar baya da qura

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281569475099616

BABBAN LABARI

Kutsen da wasu sojoji suka yi ba bisa qa’ida ba a cikin Jami’ar Abubakar Tafawa Valewa da ke Bauchi ya jawo hayaniya har suka mari Shugaban Qungiyar Malaman Jami’o’i na jami’ar. Rikicin ya faru ne da daddare lokacin da sojojin suka zo makarantar suka fara rigima da masu gadin qofar makarantar da suka hana su shiga saboda motarsu tana da gilashi mai duhu, wanda hukumar makarantar ta hana shiga cikin makarantar da irin wannan motar. Lamarin ya faru ne da misalin qarfe 11 na dare inda sojojin da aka ce su shida ne a cikin motoci biyu. Ana cikin haka ne Shugaban ASUU, Dokta Ibrahim Inuwa, ya zo yana tambaya, wanda hakan ya sa sojojin suka mare shi. Har yanzu ba a tantance manufar zuwan sojojin ba, amma wasu sun ce sun zo wajen budurwarsu ce, yayin da wasu kuma suka ce sun zo neman inda za su buga takardu ne. Rahotanni sun ce xaliban sun tare manyan qofofin shiga jami’ar a matsayin ramuwar gayya, inda suka hana sojojin ficewa daga makarantar yayin da suke jifan motocinsu da duwatsu da wasu abubuwa har suka fasa dukkan gilasan motocin biyu, Toyota Camry da Corolla, da suka haxa da fitilu kuma suka lalata tayoyin motocin. Da yake ba da bayanin abin da ya faru, Shugaban ASUU ya ce, “Ina wucewa sai na ga sojoji suna musayar zafafan kalamai da jami’an tsaron jami’ar, sai na shiga tsakani. Na ce da sojoji su kwantar da hankalinsu amma abin ya ba ni mamaki sai suka bar jami’an tsaron suka fuskance ni har ma da mari har sau uku. Kuma ka san ya sava wa qa’idar jami’a su shigo da motoci masu baqin gilashi. Abin da ya faru ya jawo hankalin xaliban da suka yi ta kai farmaki. Kafin mu ce komai, an lalata motocin sojojin biyu.” Sai da wani Birgediya Janar ya shiga tsakani ya roka a sake su. Ya zo ne da ’yan sandan soja, nan take aka kama su. Ya ce uwar qungiyar ta san da faruwar lamarin, don haka suna buqatar bayanansu su rubuta wa Babban Hafsan Soji ya sani.

ha-ng