dailytrust

Mabiya Zakzaki sun koka kan rusa gidaje da makarantunsu a Kaduna

Gine-gine da aka yi ba bisa qa’ida ba muka rusa—KASUPDA

Daga Muhammad I. Yaba, Kaduna

Acikin dare a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa makarantu da gidajen mabiya Malam Ibrahim Zakzaky a wasu unguwanin Kaduna.

Aminiya ta ziyarci gidajen a unguwannin Rigasa da Kawo da Maraban Jos da Badarawa da kuma Tudun wada.

A Rigasa makarantu biyu aka rusa da asibiti xaya. Sai a Badarawa aka rusa wani gida, a Kawo ma haka an rusa wani gida. A Maraban Jos kuwa makarantar Faudiyya aka rusa sai a Tudun Wadan, Layin Qosai an rusa makaranta.

A cewar ’yan Shi’a mabiya Zakzaky, aqalla gidaje 48 nasu gwamnatin ta ware za ta rusa ba tare da sun aikata wani laifi ba, sai dai kawai saboda aqidarsu.

Idan ba a manta ba Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta ayyukan Qungiyar IMN ta mabiya Zakzaky a

faxin jihar kuma ita qungiyar take qalubalanta.

Sai dai xaya daga cikin shugabanin Makarantar Faudiyya a Maraban Jos da aka rusa Umar Abdullahi ya ce lokacin da aka je rusa makarantar babu kowa a cikinta.

“Babu wanda ya kawo mana takarda cewa za a zo a rusa domin babu abin da ake yi a nan sai karatu. Don haka muna da magabata kuma za su xauki matakin da ya kamata na shari’a,” in ji shi.

Shi ma Malam Musa

Usman Maraban Jos wanda aka rusa wa gida a Kawo ya ce sun iso gidansa da misalin qarfe 3 na dare ne.

“Ko da na fito, suka ce sun zo su rusa gidan ne sai na ce masu su rusa,” in ji shi, sannan ya ce gidansa ba makaranta ba ce amma an rusa masa, inda ya ce zai je kotu don neman haqqinsa.

Gine-gine da aka yi ba bisa qa’ida ba aka rusa -KASUPDA

Da yake bayani kan rusa gine-ginen, Kakakin Hukumar Tsara Birane da Ci-gaban Jihar Kaduna (KASUPDA), Nuhu

Garba Xan-Ayamaka, ya ce alhakin hukumar ce ba da izini kafin a yi gini.

“Ba wai maganar makaranta ko wani gine ba ce, ita wannan hukuma tana xaukar mataki ne a kan duk wani gini da aka yi ba bisa qa’ida ba. Kana iya tambayar waxanda suke da qorafe su kawo takardun izinin gini da wannan hukumar ta ba su. Wannan hukumar tana gudanar da aikinta ne ba tare da la’akari da ginin na wane ne ko ba na wane ba ne, ko na wata qungiya ba. Idan ka je yankin da aka gudanar da wannan aiki za ka ga gine-gine da dama da aka yi wa maki. Wasu an huda wasu kuma an ba su takardar umarni.

“Ya danganta ne da yadda dokar ta tanada ba wai ta rusa gini don wata qungiya ba ce, a’a duk wanda ya cika qa’ida wannan hukumar babu ruwanta da shi,” in ji shi.

Game da cewa hukumar ta sha alwashin rusa gidajen ’yan Shi’a 48 sai ya ce, “Ba ni da masaniyar cewa za a rusa musu gidaje 48 ba.

Game da ko akwai diyya da za a biya sai ya ce “A’a babu wata diyya duk wanda ya karya doka qa’ida ma idan mutum ya karya doka kamata ya yi a ci shi tara.”

Game da cewa ba a ba masu gidajen takardar kashedi ba, sai ya ce “Akwai aikin gaggawa da in ya taso ba mu jira mu ce za a ba da takarda. Muna ba da takarda ce inda ya kamata.”

Mun garzaya kotu don neman haqqinmu-Mabiya Zakzaky

Shugaban Xaliban Zakzaky a Jihar Kaduna, Malam Aliyu Umar Tirmizi ya shaida wa Aminiya cewa makarantu shida aka rusa da asibitin sai gidaje biyu. Kuma ya ce babu wata takarda da aka ba su cewa za a rusa.

“Maganar cewa ba mu da takardu. Muna da takardunmu domin su suka ba da C of O.

“Kamar Layin Qosai akwai C of O, haka na Kawo ma akwai takardun da suka bayar. Sannan na makarantar Rigasa tana da rajista da sauran makarantu kuma ana biyan haraji da komai.

“Saboda haka kawai sun yi amfani da damar da suke da ita ce da kuma matakan da suke xauka a kan wanda ba sa so ne kawai, ba maganar takarda ba,” in ji shi.

Ya ce, “Matakin da za mu xauka shi ne da farko mun yi addu’ar Allah Ya bi mana kadi. Sannan mun garzaya kotu don mu nemi haqqinmu.”

Ya qara da cewa tun kafin zuwa kotu sai da suka rubuta takardar koke suka aika ofishin Gwamna da Kwamishinan ’Yan sanda da ofishin DSS da kuma na Shugaban Majalisar Dokokin Jihar.

Zan ci gaba da rusau da korar ma’aikata har qarshen wa’adina

-El-Rufa’i A makon jiya ne Gwanna Nasir El-Rufa’i ya sha alwashin ci gaba da rusa duk wasu wurare da yake ganin ba su kamata ba a jihar. Sannan ya ce zai ci gaba da korar ma’aikacin da bai cancanci aiki ba har qarshen wa’adin mulkinsa.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281573770066912

Media Trust Limited