dailytrust

An xage zaman qarar zave zuwa bayan rantsar da Tinubu

Kotun Sauraron Qararrakin Zaven Shugaban Qasa ta ɗage zamanta zuwa 30 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron qararrakin da ke gabanta, inda wasu jam’iyyu da ’yan takara suke qalubalantar sakamakon zaven da aka yi a watan Fabrairu, wanda zavavven Shugaban Qasa Bola Tinubu ya samu nasara.

Wannan na nufin za a dakatar da ci gaba da sauraron qararrakin zaven ke nan zuwa bayan an rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Shugaban Qasa a ranar Litinin mai zuwa.

Aminiya ta ruwaito yadda bayan tata-vurza da kai-komo da aka yi, a qarshe kotun ta amince ba za ta riqa nuna zamanta kaitsaye a talabijin ba.

’Yan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da na Labour Party, Peter Obi ne suke qalubalantar sakamakon zaven da Hukumar INEC ta ce Bola Tinubu ne ya lashe, inda suka ce suna da hujjojin da suke nuna cewa an tafka maguxi a zaven.

Kotun sauraron qararrakin na da wata uku don kammala shari’ar, wanda daga nan za a tafi Kotun Qoli.

…Shugaban Amurka zai turo wakilai wajen rantsar da Tinubu

A wani labarin, Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai turo wakilan gwamnatinsa da za su halarci bikin rantsar da sabon Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Wata sanarwa a shafin gwamnatin Amurka a ranar Litinin, Biden ya ce tuni sun kafa ayarin mutum taraa qarqashin jagorancin Sakatariyar Raya Gidaje da Birane ta Amurka, Marcia L. Fudge da za su halarci bikin rantsuwar a Abuja, Babban Birnin Najeriya.

Wannan sanarwar tana zuwacne kwanaki kaxan bayan sukar da xan takarar Shugaban Qasa na PDP Atiku Abubakar ya yi wa qasar, bayan Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken ya taya Tinubu murnar cin zave.

Atiku ya ce, savanin matsayin da gwamnatin Amurka ta bayyana wa duniya kan zaven da ta ce tana sane da irin maguxin da aka tafka, bai kamata a ce ta amince da zaven ba wanda akasarin al’umma suka yarda yana cike da maguxi.

Baya ga wakilan Shugaban Amurkan, tsofaffin shugabannin qasashe da dama da shugabannin manyan qungiyoyin qasashen duniya da wakilansu da dama sun amsa gayyatar halartar bikin rantsuwar.

Kazalika tsohon Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta zai halarci bikin, inda zai gabatar da wata muqala a gobe a cikin shirye-shiryen rantsuwar.

Za a rantsar da Tinubu, tsohon Gwamnan Jihar Legas a matsayin Shugaban Najeriya na 16, a gata Litinin a Dandalin Eagle 6TXDUH da ke Abuja.

Tun jiya Alhamis aka fara gudanar da bikukuwa, inda Shugaba Buhari mai barin-gado ya ba Tinubu lambar girmamawa mafi girma ta Najeriya wato GCFR da ake ba Shugaban Qasa, sai Mataimakinsa Sanata Kashim Shettima wanda aka ba shi lambar da ke bi mata ta GCON.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281582360001504

Media Trust Limited