dailytrust

Zargin kisa: Kotu ta hana xaukar wani mataki a kan Doguwa

Daga Salim Umar Ibrahim, Kano da Abubakar Muhammad

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dakatar da xaukar mataki a kan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa.

Kotun da Mai shari’a Mohammad Yunusa ya jagoranta a ranar Litinin ta ce, tana da hurumin saurare tare da bayar da belin wanda ake tuhuma kan Naira miliyan 500.

Haka ta ce, zargin laifin kisan kai da wasu tuhume-tuhume da ake yi wa Doguwa da ke gaban babban alqalin Kano ya sava wa kundin tsarin mulki.

Da yake yanke hukunci a kan buqatar da Alhassan Doguwa ya gabatar na tabbatar da haqqinsa na xan Adam, Mai shari’a Yunusa ya ce, Babbar Kotun Majistare ba ta da hurumin yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa Doguwa.

Mai shari’a Yunusa ya bayar da misali da Sashe na 251 (1) wanda ya bai wa Babbar Kotun Tarayya damar sauraren qara a kan makami kamar yadda ke qunshe cikin tuhumar da ake yi wa Doguwa.

Alqalin ya qara da cewa, bayar da belin Doguwa ba yana nufin hana sauraren shari’a ba ne, amma dole ne a bi tsarin da ya dace.

Lauyan Doguwa, Nureini Jimoh (SAN) ya bayar da hujjar cewa, ’yan sanda sun tsare Doguwa ba bisa qa’ida ba, kuma sun take masa ’yancinsa kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Da yake nuna rashin gamsuwarsa kan belin Doguwa, xan sanda mai gabatar da qara, AB Saleh ya ce, matakin da Mai shari’a Yunusa ya xauka kamar akwai rashin bin qa’idojin kotu.

Amma da yake yanke hukunci a ranar Litinin, Mai shari’a Yunusa ya ce, tunda farko bai kamata a tasa qeyar Doguwa zuwa gidan gyaran hali ba saboda ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Kuma ba a bincike shi yadda ya kamata ba, inda ya ce bai kamata ’yan sanda su gurfanar da shi a gaban qaramar kotu ba, wanda hakan ya sava wa Kundin Tsarin Mulki.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281599539870688

Media Trust Limited