Youtube: Taska mafi tsada da haxari a Intanet (2)

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281642489543648

BABBAN LABARI

Taska mai tsada Dandali ko shafi ko manhajar Youtube, taska ce mai ɗauke da mafi tsadar abubuwa na amfani a rayuwa duniya da Lahira. Kusan tun sa’ar da aka samar da wannan muhalli a Intanet nake amfani da shi har zuwa yau. Kuma na amfana sosai da wannan taska mai tsada. Ga kaɗan daga cikin fa’idojin da masu ziyara za su iya samu a wannan taska ta duniya mai cike da amfani: Jakar magori Shafin Youtube “Jakar magori” ne; komai kake so akwai a ciki. Idan ka ga ba ka samu ba, to ɗayan biyu: ko dai ba ka san inda za ka samo shi ba ne, ko kuma ba ka san me kake nema ba. Daga ilimin kimiyya da fasaha da sadarwa da likitanci da addini da al’ada da zamantakewa da motsa jiki da siyasa da kwamfuta da kanikanci, zuwa ilimin ƙasa da fannin sararin samaniya, zuwa yadda ake ƙera motoci da jiragen sama, da kasuwanci, har zuwa yadda ake gudanar da rayuwa. Duk kana iya samunsu a tsarin bidiyo a shafin Youtube. Ga kaɗan daga cikin shahararrun fannonin da ake samun ilimi mai tsada nan. Fannin kimiyya zalla Akwai tashoshi da yawa da ke yaɗa ilimomin da ke fannin kimiyya zalla da yawa. Daga kan ilimin sararin samaniya (Astronomy) zuwa ilimin falaki da ilimin likitanci da makamashi da muhalli da sinadarai da yadda ake haɗa magunguna a tsari na zamani, duk ana samu a Youtube. Fannin Kimiyyar Sadarwa Wannan na cikin fannonin da ilimi ya yawaita a cikinsu sosai a Youtube. Daga ilimi kan kwamfuta da wayar salula,da fasahar Intanet da yadda ake ginawa da tsarawa da kuma tafiyar da shafukan sadarwa, har zuwa kan tsari da yanayin sadarwa na duniya wanda kamfanonin wayar salula suke amfani da shi wajen aiwatar da sadarwa. Ba wannan kaɗai ba ma, masu ɗora waɗannan nau’o’in ilimomi shahararrun masana ne, waɗanda suka ci suka sha a wannan fanni a duniya. Siyasa da zamantakewa A ɓangaren siyasa da zamantakewa kuma akwai saƙonnin bidiyo da yawa. Tun daga kan siyasar duniya, zuwa siyasar ƙasashe, duk suna nan birjik. Kafofin yaɗa labaran cikin gida suna da tashoshi a kan Youtube, kuma suna hakaito mana kusan duk abin da ke faruwa a fagen siyasa da zamantakewa na ƙasar nan. Ta wannan shafi za ka san me ke faruwa a ƙasarka da ma sauran ƙasashen duniya. Tarihi A shafin Youtube akwai tsofaffin saƙonnin bidiyo masu ɗauke da abubuwan tarihi da suka wuce da daɗewa; wasu ma tun kafin a samar da fasahar Intanet a duniya. Wannan na cikin abin da ya sa wannan taska ta zama mai tsada. Galibin abubuwan da suka faru tsakanin shekara 50 zuwa 80 da suka gabata, duk kana iya samunsu a Youtube. Misali, bikin samun ’yancin kan Najeriya da aka yi da jawaban tsohon Firayi Ministan Najeriya, marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa da jawaban Firimiyan Arewa, marigayi Sardaunan Sakkwato da jawaban su marigayi Shugaban Qasa Shehu Shagari da su Abatcha, kai hatta juyin mulkin da aka yi a lokuta daban-daban, duk akwai bidiyo ɗauke da su a Youtube. Wannan hanya ce mai sauƙi wajen taskance tarihi a tsarin bidiyo. ’Yancin faɗin albarkacin baki Daga cikin fa’idar da ke tattare da Youtube akwai ba da damar faɗin albarkacin baki. Akwai jama’a da dama da suke wasu ƙasashe da ba su samun damar faɗin halin da suke ciki na gaskiya, sai ta hanyar Youtube. Waɗanda suke ƙasashe irin su Koriya ta Arewa da Iran da ƙasashe irin su Venuzuela da sauransu, kan yi amfani da tsarin sadarwa na Virtual Private Network (VPN), wajen ɗora saƙonnin bidiyo ga duniya kan haƙiƙanin halin da suke ciki. Nesa a kusa Shafin Youtube na bai wa mutane damar shirya taro kai-tsaye ta amfani da fasahar YoutubeLive, wanda ke ɗauke a shafin ko manhajar. Ta amfani da wannan fasaha, kana iya gayyatar mutane su halarci taro kai-tsaye; kana gabatar da jawabi suna bibiyarka, a ko’ina suke a duniya. Malamanmu kan yi amfani da wannan tsari wajen gabatar da karatuttukansu na mako ko wata ko muhadara. Wannan hanya ce mai sauƙi wajen ɗaukar ilimi. Bayan an gama shirin, nan take za a taskance bidiyon. Ko ba ka samu halarta a sa’ar da ake gabatar da shirin ba, kana iya kallon bidiyon a duk lokacin da ka samu dama. Abin da kake buƙata kawai shi ne kuɗin data. Faɗakarwa da ilimantarwa Ta hanyar Youtube malamai hamshaƙai daga ko’ina na sassan duniya suna gabatar da faɗakarwa ta hanyar karatuttuka da huɗubobi da nasihohi da kuma muhadarori da ake shiryawa a ƙasashensu. A ɓangarenmu nan, kusan dukkan manyan malamanmu na Najeriya, ba na Arewaci kaɗai ba, suna da tashoshi na musamman a shafin Youtube. Kuma ana ɗora karatunsu da huɗubobinsu da muhadarorin da suke gabatarwa. Ta wannan hanya za ka amfana da karatukan malaman da a baya sai dai ka ji sunayensu, ko ganinsu ba ka taɓa yi ba, amma yanzu ga su ware-wake kana ganinsu, kuma kana jin karatunsu kyauta. Ilimi a aikace A wannan kafa ne kaɗai za ka ga yadda ake koyawa ko karantar da ilimi a aikace, musamman kan abin da ya shafi Kimiyyar Fasahar Sadarwa na Zamani. Haka dukkan sauran fannonin rayuwa ma. Hatta ɓangaren ƙere-ƙere; haka za ka ga komai a aikace, yadda ake gudanar da shi. A ɓangaren addini ma akwai yadda ake koyar da wanka da alwala da sa likkafani ga mamaci da yadda ake taimama. Komai za ka gan shi a aikace ne, babu ƙwange. Waɗannan a taƙaice, su ne nau’oin abubuwan fa’ida da wannan shafi yake ɗauke da su.

ha-ng