dailytrust

Makon Qarancin Gani na Duniya

Wannan mako da muke ciki shi ne hukumomin lafiya na duniya suka ware domin faxakar da al’umma a kan matsalar qarancin gani ta myopia. Wannan matsala tana nufin rashin ganin abubuwa da ke nesa, amma mutum zai iya ganin abubuwan da ke kusa. Savanin xaya matsalar ’yar uwarta wadda ake cewa hypermyopia, wato matsalar rashin ganin kusa.

Ita wannan matsalar ta rashin iya hangen nesa ta fi matsalar rashin ganin kusa yawa, wato ta fi shafar al’umma fiye da rashin ganin kusa, domin an qiyasta cewa a duk mutum goma, mutum uku ba sa iya ganin nesa. Wato kashi 30 ke nan cikin 100 na al’umma ba sa iya ganin nesa.

Me ke jawo matsalar?

Akwai abubuwa da dama da kan iya jawo wannan matsala, tun daga gado zuwa qiba, zuwa tsufa da sauransu. Wato gado a nan ana nufin wanda iyayensa ko kakanninsa ke da matsalar zai iya samun matsalar shi ma. Qiba kuma kan iya sa qwayar ido ta qara girma har a kasa gani sosai, shi kuma tsufa na sa qwayar ido ita ma ta motse har abin ya shafi ganin mutum.

Yaya alamun matsalar suke?

Haka kawai mutum zai fara ganin cewa ba ya iya ganin nesa sosai garai, misali rubutun da ke nesa kamar na kan allo idan xalibi na kujerar baya a aji, sai dai ya ga abin da ke kusa. Kuma

Rashin iya hangen nesa

matsalar ana ganinta sosai a xalibai, har da qananan xalibai ’yan firamare, inda za su zo gida su ce ba sa iya ganin rubutu a aji.

Sa’annan sauran alamomin sun haxa da qaiqayin ido da ganin idanun suna yin ja. Sai ciwon kai idan aka daxe ana kallon wani abu kamar littafi ko talabijin.

Yaya za a magance ta?

Duk wanda yake jin irin waxannan alamu dole ya je asibitin ido a auna idon a gani ko matsalar ce ko kuma wani abu daban, domin akan iya samu ba haka ba ne wata matsala ce irinta, wadda wataqila ma ta fi wannan haxari, kamar hawan jinin ido na gilakoma wanda kan iya sa wa a rasa ganin gaba xaya.

Binciken lafiyar ido ko awon ido na lokaci zuwa lokaci ke nan yana da amfani matuqa domin gano manyan cututtukan idanu da za a iya magance su da wuri.

Matsalar rashin iya hangen nesa ana magance ta ce da tubarau ko tiyata. Amma mutane da dama sun fi karvar tubarau xin.

Amsoshin tambayoyi

Ina yawan cin xanyar albasa. Shin ko hakan na da alfanu? Kuma waxanne irin sinadarai ne da ita masu amfanin? Daga Zauro Abdullahi Amsa: Eh, qwarai albasa ai tana daga cikin ’ya’yan itatuwa masu alfanu ga jikin xan Adam domin tana da sinadarin sulfur wanda yake iya narka kitse a jikin mutum, ya kare shi daga bugun jini na zuciya da na qwaqwalwa. Sai dai xanya ta fi yawan wannan sinadari domin idan aka dafa ta raguwa yake. Shi ne ke ba albasa wannan warin don haka sai kana yi kana gyara bakinka sosai idan ka ci don shiga mutane.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281655374445536

Media Trust Limited