dailytrust

CBN ya shawarci ma’aikata da xaliban UniJos su rungumi e-naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shawarci ma’aikata da xaliban Jami’ar Jos (UniJos) su shiga a dama da su wajen amfani da kuxin Intanet (e-Naira) a harkokin mu’amala da kuxi nan gaba.

CBN ya ce duk wata harkar kuxi kamar biyan kuxin makaranta daga xalibai da albashin ma’aikata da kuma saye da sayarwa a harabobin makarantar za a iya yin su cikin sauqi ta hanyar eNaira.

Kwanturolar Reshen CBN na Jos, Misis Esther Tinat ta bayyana haka lokacin da ta jagoranci ayarin shugabannin banki zuwa kai ziyarar ban girma ga Shugaban Jami’ar Farfesa Tanko Ishaya a ofishinsa a ranar Litinin da ta gabata a mazaunin dindindin na jami’ar.

Misis Tinat ta ce, “eNaira, ita ce takardar kuxin Intanet ta Najeriya da Bankin CBN ya amince da ita kuma yake bayarwa. Tana aiki cikin gaggawa kuma ba matsala sannan tana sauqaqa saye da sayarwa da bayar da damarmaki ga masu sayen kaya har zuwa na qarshe.”

Ta ce, eNaira na bayar da damar biyan kuxi cikin sauqi ga masu sari idan aka kwatanta da amfani da takardun Naira na zahiri, kuma iri xaya ne da asusun bankuna da aka sani.

“Na zo nan ne don in qarfafa wa xaukacin mutanen jami’a su shiga tsarin eNaira wanda tsari ne na duniya mai sauqi. Yana sauqaqa wahalhalu ya rage vata lokaci da kashe kuxin da xalibai da jami’a suka haxuwa das u wajen mu’amala da takardun kuxi,” in ji ta.

A jawabin Shugaban Jami’ar Farfesa Tanko Ishaya ya bayyana CBN a matsayin babban aminin jami’ar kuma za ta jawo hankalin xalibai da ma’aikata don su ci gajiyar tsarin eNairar.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281663964380128

Media Trust Limited