dailytrust

Shin suka zai hana Rahama Sadau rawar gaban hantsi?

Daga Isiyaku Muhammed

Aqarshen mako ne aka yi bikin karrama jarumai da finafinai na Africa Magic 9LHZHUV’ Choice Awards (AMVCA9) a birnin Ikko a Jihar Legas.

Forudusa Abubakar Bashir Maishadda ne ya lashe furodusan vangaren fim xin cikin gida da fim xinsa na A’isha.

Da yake jawabi a wajen taron, Abubakar Maishadda wanda ya halarci taron sanye da shadda ya ce, “Alhamdulillah! Alhamdulillah!Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar lashe wannan kambu. Na sadaukar da wannan karramawa ga mahaifiyata, alhamdulillah.”

Sai dai a daidai lokacin da ake cikin wannan murna, sai hankalin mutane ya koma kan Rahama Sadau, musamman yanayin shigar da ta halarci taron da ita.

Rahama Sadau tana cikin masu gabatar da taron, inda ta sanya doguwar rigar da take xan nuna jikinta, sannan babu ko xan kwali a kanta.

Hakan ya sa mutane, musamman Hausawa masu bibiyar al’amuran nishaxi da waxanda ba sa bibiya yin ca a kan jarumar.

Wani mai suna Comed Daddale a Facebook cewa ya yi, “Abin da mutane ba su gane ba game da sha’anin Rahama Sadau ba shi ne, duk wannan shigar da take yi ta nuna tsiraicinta ita fa a nata ganin wataqila tana so ta burge qasashen waje ne domin kasuwarta ta havaka. Ku kuma yadda kuke qara kula ta kuna aibata ta, hakan na qara xaga tauraronta domin za su ce masu addini irin nata da qabilarta na nuna mata wariya sai su yi qoqari su qara jawo ta jikinsu. Kun ga shi ke nan burinta ya cika. Don haka ku yi sha’aninku ya fi maku ku bar ta kawai.”

Shi ma fitaccen marubuci, Abdullahi O Haruna Haruspice wanda shi ne Babban Editan Mujallar World Entourage Magazine sanya hoton jarumar da ya jawo ce-ce-ku-cen ya yi, sannan ya sanya wani hoton daban tana sanye da atamfa, sai ya ce, “Ina ma a ce wannan kyakkyawar haka ta yi shiga a taron $09&A, Wallahi da ta cinye taron ta hanyar bayyana kyawunta cikin sauqi da shiga mai sauqi ta atamfa, amma ina! Mun fi son shiga irin ta wasu ko da kuwa ba ta dace da jikinmu ba.

“Rahama Sadau kin san cewa ke kyakkyawa ce duk da cewa kina qoqarin vata kyawunki. Sai dai shigar ta xin ba mai nuna tsiraici ba ce, amma ina magana ne a kan yadda za ta fi kyau da ta sanya atamfa a taron.”

Wata mai suna Jiddah Maikano ta rubuta cewa, “Yanzu wata sakaryar haka za ta zo ta ce wannan ce abar koyinta. Wannan ai rashin hankali ne. Ta yaya mutum zai yi wannan shigar cikin hayyacinsa?

Haka a Tiwita yanayin shigar tata ya tayar da qura, inda aka riqa musayar yawu.

Ko a watan jiya jarumar ta jagoranci wani taron launuka da aka sanya wa suna ‘Arewa Color )HVWLYDO’ a Kaduna, wanda ya jawo mata maganganu, inda har ta kai ta fito ta bayyana cewa taron nishaxi ne kawai ba wani abu ba.

Aminiya ta lura wasu da dama sun yaba da yanayin yadda Abubakar Maishadda ya yi shiga irin ta Hausawa zuwa wajen taron.

Shin yau Rahama Sadau ta fara jawo ce-ce-ku-ce da shigarta?

Rahama Sadau ta daxe tana tayar da qura a Masana’antar Kannywood tun daga lokacin da ta yi waqa da mawaqi Classiq, inda aka dakatar da ita daga harkokin Kannywood, wanda wasu ke alaqantawa da farkon samun xaukakarta.

Aminiya ta rairayo wasu muhimman lokuta da jarumar ta tayar da qura a masana’antar

A shekarar 2015, jarumar ta fito fili ta wallafa a shafinta na

Instagram cewa jarumi Adam A. Zango ya cire ta ce a fim xinsa mai suna Duniya Makaranta

saboda ta qi amincewa da wata buqatarsa.

A lokacin ta yi rubutu mai zafi tare da amfani da munanan kalamai a kan jarumin wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai da rigima, domin a lokacin ta nuna cewa ba ta buqatarsa, domin tana da Ali Nuhu.

Hakan ya jefa Ali Nuhu cikin rigimar yayin da daga bisani ta goge rubutun, sannan ta ba shi haquri.

Waqa da Classiq

A shekarar 2016 kuma aka ga wani bidiyon waqa, inda aka ga jarumar suna waqa tare da mawaqin Ingilishi, &ODVVLT, inda ya riqa riqe ta da rungume ta a waqar.

Bidiyon ya jawo maganganu, inda aka riqa cewa hakan ya sava wa addinin Musulunci da al’adar Bahaushe.

Saboda bidiyon ne a ranar 26 ga Oktoba na shekarar 2016, Qungiyar MOPPAN ta dakatar da jarumar daga harkokin fim baki xaya.

Daga baya ta nemi afuwa, sannan Hukumar Tace Finafinai ta Kano, qarqashin Isma’ila Na’abba Afakallah ta yafe mata.

Murnar bikin haihuwarta da buxe wajen hutu na Sadauz Home

A shekarar 2019 kuma, jarumar ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta tare da buxe wajen hutu a Kaduna.

Wannan wajen hutu, wanda ke kan Titin Ravah a Unguwar Sarki, Kaduna ya qunshi wajen cin abinci da na wanke kai na mata da wajen aski da wajen shan Shisha da sauransu.

Bikin buxe wajen ya zo ne kwanakin kaxan bayan bikin murnar cikarta shekara 26, wanda bikin ya jawo ce-ceku-ce a shafukan sada zumunta, musamman batun buxe wajen shan Shisha da suturar da ta sanya a wajen bikin.

A nan ma ta sa wasu hotuna da ke nuna sassan jikinta tare da mawaki Classiq suna tikar rawa, wanda hakan ya jawo ce-ceku-ce matuqa.

A wannan lokaci, wasu jarumai sun nesanta kansu, tare da yin tir da abin da ta yi.

Sanya hotuna masu nuna jiki

A shekarar 2020 kuma, jarumar ta jawo ce-ce-ku-cen da ya fi kowane zafi, bayan ta saki wasu hotuna da suka nuna jikinta, inda a qasar hoton wani ya yi rubutun vatanci ga Manzon Allah, sannan aka ci mutuncin Musulunci.

Wannan karon lamarin ya fi zafi, musamman ganin yadda kusan duk Masana’antar Kannywood suka nesanta kansu da ita, wasu ma har tsinuwa suka yi.

A lokacin Qungiyar MOPPAN ta sake dakatar da ita daga harkokin fim, inda ta ce dama ko a wancan lokaci, ba ta yafe mata ba.

A lokacin kusan dukkan masu ruwa-da-tsaki a masana’antar sun caccake ta, ciki har da uban gidanta, Ali Nuhu, inda suka barranta kansu da ita, wanda aka yi tunanin wataqila qarshenta ya zo a Kannywood.

Aminiya ta ruwaito yadda hankalin jarumar ya tashi a lokacin, wanda hakan ya sa ta fito a wani faifan bidiyo tana kuka, inda a ciki ta nemi afuwar jama’a tana mai cewa, “Ni Musulma ce. Ban saka waxannan hotuna domin abin da ya faru, ya faru ba.

“Ba zan tava yin abin da zai tava Musulunci ko Annabi Muhammad (S.A.W) ba.

“Kuma dama muna wani irin lokaci ne yanzu wanda ake neman wata gava da za a ci mutuncin Musulunci, sai kuma qaddarar ta faxa a kan hotona.

“Ni ba mahaukaciya ba ce, ba ni da dalilin amincewa da abin wannan mutum ya rubuta a qasar hotona; amma dai qaddara ta riga fata.

“Duk abin da ya faru, ya faru ne a dalilina. Ina mai ba xaukacin al’umma haquri. Don Allah a yi haquri.”

Kushe bai damun Rahama Sadau-Muhsin Ibrahim

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami’ar Cologne da ke Jamus, wanda fitaccen masani a kan harkokin Kannywood, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Fitattu ba za su iya rayuwa ba ba tare da ana magana a kansu ba. Wannan ya sa Rahama Sadau wataqila kawai ta riqa yin dariya idan tana karanta jawaban da kuke yi a game da ita. Ko kun yabe ta, ko kun kushe ta, ba shi ba ne, kawai ku yi magana a kanta shi ne zai sa a riqa yawan jin ta. Wannan yana qara xaga tauraronta.

“Wataqila da a ce Rahama ba ta jawo ce-ce-ku-ce da ba ta samu shahara da arziki haka ba. Wato da a ce mun yi banza da ita, da wasu suna mata kallo daban ne.

“Amma ko kun yarda ko ba ku yarda ba, jarumar ta samu nasara matuqa a Kannywood da gaba da masana’antar. Za ta daxe ba a manta da ita ba. Ni kaina na so a ce ban ce komai ba game da wannan batu na shigarta, amma ina!”

WATA SABUWA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281676849282016

Media Trust Limited