So nake in tabbatar na gudu ko ina nan!

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281689734183904

WATA SABUWA

Wani mahaukaci ne ya gudu daga gidan mahaukata, bayan ya koma gida sai ya xauki wayarsa ya kirawo lambar masu tsaron gidan mahaukatan. Sai wani ma’aikaci ya xaga wayar. Sai mahaukacin ya ce Malam don Allah ka duba min xaki na biyar ka ga akwai mutum a ciki. Sai ya ce to. Bayan ya duba ya kirawo wayar ya ce babu kowa a ciki. Sai mahaukacin ya ce Alhamdulillah! Sai mutumin ya ce amma Malam me ya sa ka tambaya? Sai mahaukacin ya ce ba komai dama so nake in tabbatar da na gudu ko ina nan a gidan mahaukatan.

ha-ng