dailytrust

Ga masu qin qarin aure!

Nabeela Ibrahim Khaleel

Akwai wasu mata Musulmai da zaka ji suna cewa “gara mijina ya je ya yi zina da a ce ya yi mani kishiya!” Tir! Wane irin qasqanci ne muka kai da har irin wannan kalami zai iya fitowa daga bakin mace Musulma? Allah Ta’ala Ya shirye mu gaba xaya, amin. Wasu kuma kan tambaya: “Shin me ya sa aka halatta wa maza qarin aure amma ba a halatta shi ga mata ba? Raunin imaninmu ga hikimar Allah ya kai raunin da ba a tava ganin irinsa ba, da har ba mu ma ganin cewa laifi ne kuma bai dace ba, ba daidai ba ne sanya alamar tambaya a kan hukuncin Allah Maxaukakin Sarki?

Wasu matan da boko da wayewa suka yi masu yawa, kullum maganarsu xaya ce, cewa qarin aure ga maza kaxai ba adalci ba ne. Allah Maxaukakin Sarki Ya gafarta wa masu irin wannan furuci, domin magana ce ta shirka.

Wanda Ya halatta qarin aure kuma Ya kwaxaitar da yin sa Shi ne Allah Maxaukakin Sarki da kanSa. Don haka, duk abin da Shi Azza wa Jallah, a cikin babban adalcinSa da hikimarSa, Ya halatta kuma Ya kwaxaitar da shi, to wannan abin shi ne daidai kuma shi ne cikakken adalci. Faxar cewa qarin aure ba adalci ba ne kamar cewa ne Allah Maxaukakin Sarki ba mai adalci ba ne, Allah Maxaukakin Sarki Ya kiyaye harshenmu daga irin wannan savo, amin.

Mata Musulmi dole ne su fitar da hankalinsu daga kwatar tunanin irin na Turawan Yamma, su kai shi ga hikima da tsarkin hankalin Musulunci. Qarin aure ba cin mutuncin mata ba ne; alama ce ta girmamawa da darajtawa. Mata nawa ne za su zauna gwauraye inda an haramta qarin? Akwai vacin rai ga yadda ake yi wa matan da aka qara aure da su. Babban abin takaicin shi ne su kansu matan da suka zo a na biyu ko uku sai ka ga in mijinsu zai qara auren suna jayayya da tada jijiyar wuya. Wane irin tunani ne wannan? Abin da ke ya amfane ki, kike qoqarin hana wata ’yar uwarki Musulma ta amfana da shi?

Ina hankalinmu yake? Ina imaninmu ga hikimar Allah Maxaukakin Sarki take? Ina miqa wuyanmu ga dukkan umarnin Allah Maxaukakin Sarki? Ina qaunar junanmu take? Ina son wa ’yan uwanmu mata abin da muke so wa kanmu, wato iyali, soyayya da kwanciyar hankali? Ba a sanya mu a doron qasa don mu yi komai ba, face bauta wa Allah Maxaukakin Sarki, kuma dole mu yi bautar yadda Ya umarta ba bisa zavi da son ranmu ba.

An halatta mana kishi. Uwar

Muminai A’isha (RA) ta fi kowace kishi daga cikin Matan Manzon Allah (SAW), amma ba ta bari kishinta ya ruguza mata addini da imaninta ba. To me ya sa yake mana wahala yin irin wannan tsabtataccen kishi? Me ya sa ba za mu yi koyi da waɗannan kyawawan misalai ba a maimakon misalan matan Yamma waxanda ba su san su mutunta kansu ba balle har su mutunta wasu?

Ya ’yan uwa mata, ba wai lallai sai kun je kun sa mazanku su qara aure ba, amma ina maku nasihar da in qarin aure ya zo maku, to ku karve shi a matsayin kyakkyawa kuma halartaccen abu sannan ku ba mazanku goyon baya xari bisa xari.

Amma in kina da qarfin imani, to akwai alheri mai yawa wajen roqon mijinki ya taimaki wata ’yar uwa mabuqaciya ta hanyar aurenta. Ki yi tunanin ke ce mijinki ya mutu ko ya sake ki ga yara, ko ke ce kika daxe a gaban iyayenki ba ki samu mijin aure ba, ko kin daxe kina zawarci har kin fara fid da rai, ba za ki so wata ta share maki hawaye ba, ta ba ki dama ki auri mijinta?

Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne, ki tausaya wa irin waxannan mata. Idan sun auri mijinki ko mijin qawarki ko ’yar uwarki, kada ki zage su ko ki tsine musu, ki riqa yi masu kallon masu qwacen miji, kada ki riqa jin haushinsu, ki tozarta su ko yanke hulxa da su ko ki riqa quntata wa rayuwarsu. Sun bi umarnin Allah Maxaukaki ta hanyar cika rabin addininsu ne (aure) ba su je suna yawon banza ba. Duk wadda ta ji hakan bai yi mata daxi a rai ba to ta binciki imaninta.

Dole ne mu yarda da qarin aure a matsayin addinin Allah Maxaukakin Sarki kuma a matsayin kyakkyawan tafarki abin bi. Allah Maxaukakin Sarki Ya shiryar da mu baki xaya wajen karvar hukuncinSa, Allah Ya ba mu qarfin halin bin wannan addini mai girma da aiki da shi gaba xayansa, kuma Allah Ya qara mana qarfin imani da yaqi da son zuciyarmu, amin.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281728388889568

Media Trust Limited