dailytrust

Yadda ’yan sa-kai suka yi wa Fulani makiyaya kisan gilla a Oyo

Daga Abbas Xalibi, Abeokuta

Aranar Juma’a 12 ga Mayun 2023 ne al’ummar Fulani makiyaya da ke zaune a garin Iganna da ke Qaramar Hukumar Iwajowa a Jihar Oyo suka wayi gari cikin firgici, bayan wani mummunan harin da aka kai masu wanda ya yi salwantar rayukan mutum 11 ciki har da mata masu ciki uku d masu shayarwa huxu da yara qanana da magidanta uku.

Mamuda Yusuf shi ne Sarkin Samarin Fulani na Jihar Oyo, kuma xaya daga cikin shugabanin Fulanin da lamarin ya rutsa da su a Iganna, ya shaida wa Aminiya cewa, matsalar ta samo asali ne biyo bayan wani ƙirƙirarren labari da aka yi ta yayatawa a garin Iganna cewa Fulani makiyaya sun sassari wani manomi. “Kuma binciken da muka yi babu wani manomi da aka sara, domin sun qi su bayyana inda yake, kuma ba su kai wa ’yan sanda rahoto ba, don haka ’yan sanda ba su da bayanin komai a kan qagaggen labarin da suka shirya.

“A yammacin Alhamis 11 ga Mayun 2023 ne wasu ’yan qungiyar sa-kai (bijilante) suka zo suka same ni, suka ce an sassari wani manomi a gona, sai na tambaye su ko sun shaida wanda ya sari manomin? Sai suka ce a’a. Sai na ce su yi haquri zan gayyato xaukacin jama’armu sai mu haxu a gidan Sarkin garin, a tattauna a fito da wanda ya aikata laifin. A lokacin sun shaida min an kai wanda aka ji wa raunin wani asibiti.

“Nan take na tafi fadar Sarkin garin na shaida masa halin da ake ciki tare da ba shi tabbacin zan gayyato jama’armu zuwa fadarsa domin a lalubo waxanda ake zargin. Bayan gari ya waye a ranar Juma’a na yi ta shela domin jama’armu su hallara, sai dai matsalar a ranar ake cin kasuwar dabobbi ta mako-mako a garin Iseyin, kuma hakan ya sa yawancin mutanenmu sun riga sun tafi cin kasuwar.

“Ko da na fito za ni fadar sai na gamu da mutumin farko da maharan suka kashe wato Alhaji Umaru, a kan hanya na tsaya wajen mai tsire na saya, har ya ce min shi

ma zai ci, na raba biyu na ba shi, nan na bar shi a wajen, bayan na faxa masa cewa na nufi fada, ya ce min zai je gida ya fito yanzu ya same ni a can kuma za su taho tare da wasu mutane.

“Da na isa fadar ina sauraron zuwansu, sai aka kira ni ta waya cewa maharba da ’yan bijilante sun kai hari a gidajenmu. Na fito daga fadar Kabesi na nufi gida, a kan hanyata gawar Alhaji Umaru da na bar shi wajen mai tsire na fara gani yashe a gefen hanya cikin jini. Daga baya kuma

na iske gawar mutum biyu magidanta a gefen hanya.

“Ina qarasawa gidajenmu sai na ga duk an qone su, na iske gawar mata masu tsohon ciki uku, xaya daga cikinsu ma na san ran a ranar za ta haihu, sannan sun kashe wasu mata huxu masu shayarwa, sun kuma kashe yaro xan shekara biyu tare da jikkata mutum 7 da yanzu suke asibiti, sai yarinya xaya da ta vace har yanzu ba a ganta ba, sannan an qone mana gidaje 72,” in ji shi.

Mamuda Yusuf ya ce, sama da mako biyu da faruwar lamarin, ’yan sanda ba su kama kowa ba, bayan waxanda suka yi aika-aikar a bayyane suke, “A gaban jami’an tsaro ma, wani Basarake a garin wanda ake kira Balogun na Iganna ya yi iqirarin cewa sun hallaka Fulanin ne saboda sun sari manominsu, kuma ya ce wannan abin da suka yi somin-tavi ne.

“Mu fatarmu duk mai hannu a wannan aika-aika a kama shi a hukunta shi daidai da laifinsa, domin hakan ne zai kare aukuwar haka a nan gaba,” in ji shi.

Wakilin Aminiya ya tuntuvi basaraken da Fulani da suka zarge shi da kalaman tunzura jama’a wato Balogun na Iganna, Karim Oyideran, inda ya musanta zargin, ya ce ba ya da labarin Fulani makiyaya sun sari wani manomi a yankin.

“Na ji an ce an kai hari a matsugunin Fulani, sai na nufi wajen tare da wasu maharba, sai muka tarar an sanya wa gidajen Fulanin wuta,” in ji shi.

Hakazalika wakilinmu ya tuntuvi Sakataren Yaxa Labarai na Gwamnan Jihar Oyo, Taiwo Adisa, wanda ya shaida masa cewa, zuwa lokacin ’yan sanda ba su ba su adadin mutanen da aka kashe ko aka jikkata a rikicin ba. “Gwamna ya samu labarin rikicin wanda aka faxa masa ya samo asali ne kan sarar wani manomi waxanda wasu kuma suka kai harin ramuwar gayya. Gwamna ya je wajen bayan faruwar lamarin da kwana xaya domin jajanta masu, ya kuma bai wa jami’an tsaro umarnin tabbatar da tsaro a yankin tare da kamo masu hannu a lamarin. Har yanzu ’yan sanda ba su ba mu sakamakon bincikensu a kan lamarin ba,” in ji shi.

Da wakilin Aminiya ya tuntuvi Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ’yan sanda na bincike a kai. “Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Adebowale Williams ya bai wa mataimakinsa mai kula da sashin miyagun laifuffuka umarnin ya binciki lamarin,” in ji shi.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281736978824160

Media Trust Limited