‘Yan sanda sun kama ‘yan qungiyar asiri da suka addabi Edo

Daga Abdurrahman Masagala, Benin

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281758453660640

DUNIYAR

Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo ta kama waxanda ake zargi ’yan qungiyar asiri ne da suka addabi mazauna garin Benin fadar jihar. A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun Kakakinta SP Chidi Nwabuzor, waxanda ake zargin su ne Bright Amadin mai shekara 34 da Brown Amadin mai shekara 29 da Stanley Omoregie mai shekara 27, kuma an kama su ne a lokacin da suke yi wa mutane qarfa-qarfa tare da tilastwa musu shiga sharholiyar murnar ranar haihuwarsu. Sanarwar ta ce an same su da miyagun makamai da suka haxa da bindiga mai sarrafa kanta da harsasai uku da adduna da gatari da tufafi masu xauke da alamar qungiyar mai suna manphite. “A ranar 11 ga Mayu, 2023, jami’in ’yan sandan farin kaya na IRRS ya samu labarin cewa wasu fitattun ’yan qungiyar asiri sun taru a wani wuri a birnin Benin domin kai farmaki kan wata qungiyar asiri da kuma tilasta wa waxanda ba su ji ba, ba su gani ba shiga sharholiyar murnar zagayowar ranar haihuwa da ’yan qungiyar ke yi. “Nan take ’yan sandan suka fara tattara bayanan asiri a qoqarinsu na daqile shirinsu, kuma a ranar 12 ga Mayun 2023 da misalin qarfe 2.30 na dare, ’yan sandan suka kama uku daga cikinsu a Unguwar Okabere, da ke kan titin Upper Sakponba birnin Benin,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ce, waxanda ake zargin sun amsa cewa su ’yan qungiyar asiri ne. Kuma ana ci gaba da qoqarin kamo wasu ’yan qungiyar da suka tsere, inda za a kai waxanda aka kama kotu nan ba da daxewa ba.

ha-ng