dailytrust

NAFDAC ta kama mai Kamfanin Maganin Gargajiya a Ibadan

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Qasa (NAFDAC) ta rufe kamfanin magungunan gargajiya na At-Taqwah Herbal Product da ke Ibadan tare da kama wanda ya mallaki kamfanin mai suna Abdulrohim Muideen Ajao saboda zarginsa da sarrafa haramtattun magungunan da za su iya cutar da lafiyar mutane.

Ma’aikatan Hukumar NAFDAC da haxin gwiwar jami’an tsaro a qarqashin jagorancin

Daraktan Hukumar a Kudu maso Yamma, Misis Florence Ajayi ne suka rufe kamfanin da ke bayan Kwalejin Periscope a Unguwar Muslim a birnin Ibadan. Da take yi wa ’yan jarida bayani Misis Florence Ajayi ta ce hukumar ta yi nasarar kama wanda ya mallaki kamfani mai xakuna 8 da ake sarrafa haramtattun magunguna a cikinsu ne bayan samun labarin sirri daga wasu mazauna unguwar kan irin magungunan da ake sarrafawa.

Ta ce jahilci da son zuciya ne ke jefa mafi yawan masu kamfanonin maganin gargajiya sarrafa irin waxannan magunguna ta haramtacciyar hanya inda suke cutar da masu amfani da su. Ta ce wannan kame da suka yi ya kawo qarshen yin jabun magani a kamfanin.

Mai kamfanin, Abdulrohim Muideen Ajao ya nuna mamakin kamen da aka yi masa da kuma rufe kamfanin da ya ce ya shafe shekara 5 yana sarrafa magungunan hawan jini da maleriya da qarfin jiki da yake rarraba su zuwa sassan Kudu maso Yamma da garin Jos a Arewa.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281762748627936

Media Trust Limited