dailytrust

Yadda Hausawan Kalaba suka zama jigajigan kasuwanci a Kuros Riba

Daga Musa Kutama, Kalaba

Unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri a Jihar Kuros Riba xaya ce daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a jihar. Babbar cibiya ce da ake hada-hadar kasuwanci wadda ko runhu mutum ya riqo ya shigo unguwar komai dare zai samu abin da zai ci ba zai kwana da yunwa ba.

Ta fuskar kasuwanci ’yan Arewa mazauna Kuros Riba tun daga Bakassi zuwa Obanliku suna taka rawar gani kama daga sana’ar fawa da kiwo da harkar gwangwan da harkar goro da manja.

Hausawan sun yi ficen gaske a kasuwanci da qananan sana’o’i wanda ta haka ne ma sama da shekara 180 ake jin ’yan Arewa suka je jihar, kamar yadda Alhaji Qasimu Ali Haruna, Sarkin Hausawan Obudu ya shida wa Aminiya a ranar Lahadi.

Ya ce “Kakanninmu sun gaya mana cewa nan garin Obudu ne Hausawa suka fara yada zango sun kuma zauna a wani wuri yanzu da ake kira Gadar Raga fiye da shekara 180, kafin daga bisani a mayar da su mazauninsu na yanzu wato garin Obudu.”

Dangane da yadda ’yan Arewa mazauna Kalaba suke gudanar da harkokin kasuwanci goro da manja kuwa, ba qaramar gudunmawa suke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin jihar, kamar yadda wani babban jami’in gwammati ya shaida wa Aminiya: “Unguwar Hausawa a Kalaba tamkar ita ce Kasuwar Sabon Gari a Kano, ko Kasuwar Gombe ko ta Maiduguri saboda koyaushe ka zo za ka iske mutane kamar ba su yin barci.”

Alhaji Jamilu Jos na xaya daga cikin masu kasuwancin manja a Kalaba, ya shaida wa Aminiya bayani kan yadda ake yin manjan, inda ya ce “Akwai wanda ake samu a nan garin Kalaba da kuma qauyuka ana kawo mana muna saye. Kuma akwai wanda yake fitowa daga qasar Kamaru ta kan iyakar Najeriya da Kamaru musamman ta Bakassi. To idan aka kawo mukan saya sai a gyara shi mu kai kasuwannin Arewa irin su Jos da Kano da Gombe da sauran garuruwan Arewa.”

Xan kasuwar ya yi bayanin abin da ya bambanta manjan Najeriya na Kalaba da na Kamaru. Ya ce “Gaskiya na nan Najeriya yana da kyau sosai xanxanonsa ya bmnbanta da na Kamaru. Kuma jin qanshin kwakwa a cikin manjan wani abu ne mai daxi. Kuma wani abin da ya bambanta na Kamaru da na Najeriya shi ne, na Kamaru ya fi na Najeriya yawa. Akwai lokacin da namu yake yankewa wato na Kamarun yam aye gurbinsa, saboda ya fi na Najeriya ya wa, shi ma ana samun mai kyau.”

Alhaji Jamilu Jos ya ce sun xauki matakin ba sani, ba sabo don hukunta duk wanda aka samu yana amaja yana gauraya mara kyau da mai kyau ko haxa manja da ruwa.

Da ya juya kan qalubalen da harkar manja ke fama da shi, ya ce “Babbar matsalar da muke fuskanta ita ce ta hanya, musamman wajen kashe kuxi idan mun xora kaya zuwa Arewa, inda masu tsaron hanya suke takura mana. Don yanzu zan iya ce maka idan tirela ta tashi daga nan Kalaba kafin ta je Kano sai ta kashe kuxin da ya

kai Naira dubu 200 da direba zai riqa rabawa a hanya. Akwai inda za ka ga ’yan iskan gari ne suke sanya shinge a hanya da sunan karvar haraji ko jangali, sai an ba su Naira 5,000. Sojoji masu tare hanya sai an ba su Naira 5,000 zuwa 6,000, haka ’yan sanda Naira 5,000. Daga nan dai mutum na zai ya ta ba su, ba zai fara samun sauqi ba sai ya kai Jihar Benuwai ko Nasarawa. Ina tabbatar maka duk direban da zai tashi daga nan Kalaba kafin ya kai Arewa sai ya kashe sama da Naira dubu 200 ga jami’an tsaro a kan hanya da ’yan iskan gari.”

Masu kasuwancin sun fara xaukar matakai don samun sauqin kashe kuxi a qarqashin jagorancin Alhaji Xanlami Sale Rishi.

Alhaji Babangida Shehu

Alkanowiy Mariri da ke Kasuwar Goro a Unguwar Hausawa, Layin Bagobiri da wakilinmu ya iske suna aikin gyaran namijin goro ya shaida wa Aminiya yadda namijin goro yake da kuma alfanun kasuwancinsa. Ya ce, “Namijin goro nau’i biyu ne, akwai mai qwara, akwai mai qanana sannan ana samunsa yawanci a duk inda ake samun goro a jihohin Kudu maso Yamma da Jihar Kuros Riba.”

Alhaji Shehu Alkanowiy Mariri ya ci gaba da cewa “Namijin goro ya fi tsada don yanzu namijin goro yana ninka goro a kuxi saboda darajarsu ba xaya ba ce.”

Ya yi bayanin jihohin da suke kaiwa su sayar da suka haxa da Kano da Jigawa da Bauchi da Borno da Gombe da sauransu.

Ya ce kasuwancin goro ba su ’yan Arewa kaxai suke yin ta ba, hatta ’yan asalin jihar ma suna yi don a wurinsu ne ma suke saye su sayar.

Ya ce kasuwanci da gyaran goro na samar wa matasa ’yan Arewa da suka zo ci-rani aikin yi domin idan ana aikin goro mutum sama da biyar za a gani ana aikin da su kuma kowa zai samu abin da zai sa a aljihunsa.

Ya qara da cewa, “Mutum zai ci, ya sha har ma ya taimaki wani ko wasu. Allah Ya albarki kasuwanci ko sana’ar.”

A qarshe ya buqaci gwamnati ta duba lamarin su wajen rage matsalar masu quntata wa ’yan kasuwa idan sun xauki dukiyar su zuwa kasuwanci a Arewa musamman jami’an da ke aiki a shingayen duba ababen hawa da ke takura wa direbobi.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281767043595232

Media Trust Limited