dailytrust

Qurunqus Alhaji Mudi Sipikin ya fexe biri har bindinsa

Daga Kwamared Ibrahim Abdu Zango Kwamared Ibrahim Abdu Zango, Shugaban Kano Unity Forum, Kano. 08175472298

Na ji wata waqa ta musamman wacce marigayi Alhaji Mudi Sipikin Darma ya yi wa manyan sarakunan Kano. Wato marigayi Sarki Alhaji Abdullahi Bayero da ababuwan alheri da ya yi wa Masarautar Kanon Dabo. Alhaji Mudi Sipikin ya zayyana abubuwan kirki masu yawan gaske da suka haxa da harkar asibiti da gina kurkuku da masallatai da sauran abubuwa na ci gaban Kano. Kuma har gobe za a ci gaba da morar waxannan abubuwa da Sarki Alhaji Abdullahi Bayero ya yi a zamaninsa, domin ba ’yan siyasa ba ne irin na yanzu, saboda wasu ma ba a yi cikinsu ba; lokacin Turawa ne, ba su yin baqin ciki ci gaban jama’a kamar yanzu. Sarki Alhaji shi ne dai mahaifin sarakuna masu albarka waxanda muka gan su ra’ayal aini. Sarki Alhaji Allah Ya ji qansa, Sarki ne mai tausayin jama’a wanda bai ci zali ba, kuma Sarki ne mai ilimi da fatar kawo abubuwan alheri ga zamani irin na wancan lokaci, Allah Ya ji qan wannan Sarki wanda ya yi qoqari sosai wajen ganin an yi komai cikin tsarin addinin Musulunci.

Bayan rasuwar wannan bawan Allah sai aka naxa xansa Alhaji Muhammadu Sanusi a 1953, kuma shi ma wannan bawan Allah ya yi qoqari wajen raya addinin Musulunci sosaisosai kuma ya yi shekara 10 yana mulki daga 1953 zuwa 1963. Lokacin da guguwar siyasa ta kawo qarshen mulkinsa kowa ya san rawar da Sarki Sanusi ya taka domin kyautata wa wannan qasa, amma an ga yadda ta kaya, aka yi yadda aka yi ya rubuta takarda ya bar mulkin kuma maqiya suka ji kunya. Wannan shi ne illar shiga siyasa wacce Mai alfarma Alhaji Ibrahim Dasuqi Sarkin Musulmi na 18 ya guji a sa sarakuna a cikin harkokin siyasa.

Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuqi Allah Ya ji qansa lokacin wani kwamiti da aka kafa kuma shi ne shugaban kwamitin ya ce, shigar da sarakuna harkar siyasa zai tava mutuncinsu sosai da sosai, domin za a zo zamanin da xan talakansu zai yi tsallen baxake a kansu. Kodayake lokacin NPC Sa Ahmadu Bello Sardauna jinin Shehu Usman ne, amma a lokacin aka tuve Sarki Muhammadu Sanusi, domin a nuna cewa har wancan lokaci Sakkwato ce ke tabbatar da waye zai zama Sarkin Kano, wannan tarihi ne kawai ba wai ta da zaune-tsaye ba. Haka dai ya faru ko da ba shi ba ne ra’ayin Sa Ahmadu Bello Sardauna ba.

To bayan an sauke Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi a 1963, sai aka naxa wani bawan Allah xan uwa ga Sarki Alhaji, wato Muhammadu Inuwa, Allah Ya ji qan Sarki mai sauqin kai da fara’a ga talakawansa. Sarkin Kano Muhammadu Inuwa ya yi wata shida kacal lokacin da ya koma ga Mahaliccinmu Allah Ta’ala. Ya rasu lokacin da jama’ar Kano suke buqatarsa. Bayan komawar Malam Muhammadu Inuwa ga Ubangijinsa, sai aka naxa Alhaji Ado Abdullahi Bayero, wanda kowa ya ga rawar da ya taka wajen kyautata wa addinin Musulunci da raya qasa ta kowane fanni. Alhaji Ado Abdullahi Bayero ya yi iya iyawarsa ta janyo talaka a jikinsa kowa ya gani kususan ta naxa waxanda ko kusa ba su gaji sarauta ba, amma saboda so da qauna a yau sun zama hakimai da dagatai. Wannan alfarma ce ta musamman ga ire-iren waxancan bayin Allah. Shekara fiye da 50 Alhaji Ado Bayero ya yi yana mulki ban tava jin wani ya yi kuka da mulkinsa ba, duk da Kano tana da yawa da faxin gaske har yau xin nan!

Allah cikin ikonSa Allah Ya yi wa wannan shahararren Sarki baiwa babba ta qaunar jama’a sosai da sosai, kuma ya bar duniya cikin farin ciki, muna roqa masa Allah Ya saka shi cikin Aljannar Firdausi, amin summa amin. Ka ga malam gidan Sarautar Kano ba su gaji ka-cena-ce ba, wacce jama’ar gari za su ji, saboda haka ne muke kira ga ma’abota haxa faxan ka-cena-ce su yi wa Allah su kauce wa kawo hargitsi cikin ni’imar da Allah Ya yi wa al’ummar Kano. Xan qwairo ya ce kowav vata ya sani kowag gyara ya sani: ka ga ashe suna neman kawo cikas ga masarautun Kano suna yi ne kawai domin su vata wa jama’ar Kano. Shi kuma Malam Ibrahim Ado Kurawa ya yi tsokaci a kan xan uwan Gwamna wanda aka naxa hakimi, to yaya kuma Hakimin Madobi shi kuma qanin Ganduje ne? Don Allah a bar jama’ar Kano su ji da abin da yake ci musu tuwo a qwarya. Sarakuna iyayen jama’a ne kada a tava martabarsu. Don Allah a bar su cikin kamala.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281797108366304

Media Trust Limited