Jimina

Taku: Amina Abdullahi

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281814288235488

DUNIYAR

ABarkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar ana lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘Jimina.’ Labarin ya yi nuni ne a kan illar zargi da kuma abin da ba a da tabbas a kai. A sha karatu lafiya. Suna cikin kwashe duwatsun, sai ga wata jimina ta zo ta haxiye babban dutsen lu’u-lu’un. Matan da xan maqerin suka shiga neman babban dutsen amma ba su samu ba. A gefensu akwai wani mutum yana zaune. Sai suka zarge shi da xaukar wannan dutsen lu’u-lu’un. Suka tara masa mutane sai suka fara dukansa. Yana cewa ba shi ya xauki lu’u-lu’un ba, amma mutanen suka qi yarda. Mutumin ya gaya musu kwai wata mata ta xauki akwatin kayan koli. Akwatin ya qunshi duwatsun gwal da lu’u-lu’u. Tana son ta kai wa wani maqeri ya qera mata abin wuya. A kan hanyarta, sai akwatin ya faxi kuma duwatsun lu’u-lu’ da na gwalagwalai suka zube. Maqerin na hango hakan sai ya aiki xansa ya je da gudu domin ya taya matar kwashe waxannan duwatsu. cewa ya ga wata jimina ta haxiye dutsen amma aka ci gaba da bugunsa. Har sai da wata tsohuwa ta zo ta dakatar da su daga dukansa. Ta ce a kamo jimina. Sannan aka kamo ta aka bai wa mai jimina kuxin jimina, ana fexe jimina, sai ga babban dutsen lu’u-lu’un a cikinta. Sai mutumin da ake zargi da sata ya ce a biya shi diyya kan dukan da aka yi masa. Haka matan nan ta xebi kuxi mai ximbin yawa ta bai wa mutumin.

ha-ng