dailytrust

Kwalliya

Hanyoyin magance kumburin idanu

Daga Amina Abdullahi

Kumburin idanu na faruwa ne galibi sakamakon yawan kuka ko yawan amfani da ido wajen karatu ko aiki a kan na’urar kamfuta. Wasu kuma kumburin idanunsu na da alaqa da wani canji da aka samu a jiki ko don yanayi walau qura ko rana. Wasu kuma nasu na faruwa ne saboda rashin barci ko cin abincin da ba ya xauke da sinadaran gyaran ido.

Ido na xaya daga cikin abubuwan da ake fara gani a fuska don haka ya kamata mu kula da idanuwanmu. Akwai hanyoyi da dama da suka kamata a bi don magance matsalolin kumburin ido kamar haka:

· Shan ruwa hanya ce mafi sauqi wajen magance kumburin ido domin, ruwa na wanke dauxa a ido. Yawan shan ruwa yana da kyau a sha ruwa aqalla kofi takwas zuwa goma a rana. Sannan kuma yana da kyau a rage cin gishiri.

· A samu cokulan qarfe kamar biyar zuwa shida a sa a firiji na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a ciresu, a dinga shafawa a kan kumburin ido har sai ido ya save.

· Ganyen shayi na magance kumburin ido; a jiqa ganyen shayi a ruwan xumi, sannan a cire a bari ya huce. Sai a kwanta a xora jiqaqqiyar jakar ganyen shayin a kan idanu a rufe idanu da qyalle mai tsafta. A bari ya tsaya a hakan na tsawon minti biyar zuwa goma sannan a cire.

· Wata hanyar magance kumburin ido ita ce; a samu gurji a yanka a sa a firiji na tsawon minti 10 sannan a cire a xora a kan idanuwan har sai sun huce.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281818583202784

Media Trust Limited