Na fi son talaka kyakkyawa - Farida Adamu

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281870122810336

DUNIYAR

Daga Elizabeth Fidelis da Muhammad Shu’aibu Na fi son talaka kyakkyawa a kan mai kuxi mummuna, don gaskiya wani mai kuxin in ka aure shi wahala za ka sha, saboda ba tare da kai ya yi kuxin ba, gwanda ka auri talaka kawai. Gara talaka - Esther Samuel Ina son talaka saboda talaka ya riga ya san halin da shi ya tashi, shi zai ba ki girmanki. Amma shi mai kuxi yana da lokacinsa, zai riqa juya ki, sai ya yi abin da ya ga dama da ke, kuma ba yadda za ki yi. Don haka ina ganin gara talaka.

ha-ng