dailytrust

Cutar Kwalara: Mutanen Afirka ta Kudu sun kori Magajin Gari daga asibiti

Fusatattun mutane a Afirka ta Kudu sun kori wani Magajin Gari daga wani asibiti a Arewacin Pretotia bisa zargin sa da gaza samar da ruwan sha mai tsabta, a daidai lokacin da cutar Kwalara ta halaka mutum 15 a garin Gauteng mai ximbin jama’a.

Ana tunanin Magajin Garin Birnin Tshwane, Mista Cilliers Brink ya gana da jami’an gwamnati don duba halin da ake ciki game da varkewar cutar Kwalara a yankin.

Sai dai qura ta tashi a wajen asibitin Jubilee District Hospital a ranar Litinin, yayin da fusatattun mutanen garin suka tunkare shi suna buqatar tsabtataccen ruwan sha, kamar yadda kafafen labarai na qasar suka ruwaito.

Mutanen sun yi kwanton vauna a bayan wasu motoci a wajen asibitin, inda suka tilasta wa Magajin Garin barin harabar. Sun zarge shi da rashin xaukar kiwon lafiyarsu da muhimmanci.

A ranar Lahadi ce Sashen Kula da Lafiya na Gauteng ya bayyana varkewar cutar Kwalara a garin Hammanskraal, a Arewa da Pretoria.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar Kwalara ta varke a qasashen Afirka 15 ciki har da Afirka ta Kudu.

Sauran qasashen sun haxa da Jamhuriyar Dimokuraxiyyar Kwango (DRC) da Eswatini da 0R]DPELTXH da Kenya da Zimbabwe, inda ta ce qasar Malawi ce ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar.

TARE DA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281921662417888

Media Trust Limited