Shugaban ’yan adawar Senegal ya qi halartar shari’ar fyaxe

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281930252352480

TARE DA

Shari’ar zargin fyaxen da ake yi wa Shugaban ’Yan Adawar qasar Senegal ta ci gaba, sai dai shugaban Ousmane Sonko ya sake qaurace wa halartar shari’ar. Kafar labarai ta AFP ta ce, jami’an tsaro sun ta yin sintiri a Dakar Babban Birnin qasar saboda tsoron yiwuwar tayar da qayar baya daga magoya bayansa. Mista Sonko dai yana da farin jini musamman a tsakanin matasa. Xan siyasar mai shekara 48 ya ce, shari’ar tasa wadda aka faro a makon jiya bi-ta-daqullin siyasa ce kawai don a hana shi tsayawa takarar Shugaban Qasa a zaven baxi. Haka kuma, ya musanta cin zarafin wata mace da take aiki a gidan tausa ko yi mata barazanar kisa. Tsohon jami’in karvar harajin ya fito ne daga kudancin birnin Ziguinchor, inda yake Magajin Gari. Masu zanga-zanga sun tare hanyar zuwa gidansa domin hana yunqurin kama shi.

ha-ng