Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana bakwai ta fara aiki a Sudan
2023-05-26T07:00:00.0000000Z
2023-05-26T07:00:00.0000000Z
Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281938842287072
TARE DA
Rahotanni daga Sudan sun ce, yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da aka cim ma ta soma aiki duk da cewa da fari an yi zargin vangarorin sun qi mutunta ta. A Khartoum, mazauna birnin sun ce ana ci gaba da kai hare-haren sama da tafka sabon rikici. Haka kuma a birane irin su Omdurman da Bahri, mutane sun ce suna jiyo qarar harbeharbe. An cim ma yarjejeniyar tsagaita wutar ce a zaman tattaunawa da Saudiyya da Amurka suke jagoranta wanda shi ne zama irin sa na farko tunda aka soma wannan yaqi mako biyar da suka gabata. Sa’o’i bayan yarjejeniyar ta soma aiki, Shugaban Sojin Sa-Kai na RSF, Janar Dagalo, ya fitar da wata sanarwa da ke kira ga sojojinsa su murqushe sojojin Sudan da suke yaqi da su, domin nasara a yaqin
ha-ng