Yara 19 sun mutu a gobarar makaranta a Guyana

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/281943137254368

TARE DA

Aqalla yara 19 ne gobara ta halaka a garin Mahdiya da ke tsakiyar qasar Guyana a daren Litinin da ta gabata. Jami’an qasar sun ce, gobarar ta varke ne a tsakiyar dare a xakunan kwanan xalibai, inda ta ritsa da xaliban. Jami’an agaji sun yi qoqarin kashe gobarar wadda ta auku a lokacin da ake fama da yanayi marar kyau. Ana zargin gobarar ta auku ne sakamakon maqarqashiya, sai dai ’yan sanda sun ce har yanzu ba a gano wanda yake da hannu a lamarin. Mutane da dama sun samu rauni a gobarar, inda aka kai wasu daga cikinsu zuwa birnin Georgetown, aka kafa cibiyar kiwon lafiya ta musamman. “Wannan babbar masifa ce. Abar tsoro da xaga hankali” in ji Shugaban Qasar Guyana Irfaan Ali. Kafar labarai ta AFP ta ruwaito Mista Ali yana cewa, baya ga rukunin ma’aikatan jinya biyu da aka tanada a filin jirgin sama, manyan asibitocin Georgetown biyu sun shirya “don kula da duk yaron da ke buqatar kulawa ta musamman .” Ministan Harkokin Cikin Gida, Mista Robeson Benn ya ziyarci inda gobarar ta auku kuma daga baya Firayi Minista da wasu jami’an gwamnati suka isa waurin. Guyana dai tana tsakanin qasashen Venezuela da Suriname ne a gavar ruwan Kudancin Amurka.

ha-ng