dailytrust

Zaven Turkiyya: Erdogan ya kama hanyar nasara

(RFI)

Ga dukkan alamu Shugaban Turkiyya Recep Xayyib Erdogan ya kama hanyar samun nasara a zaven zagaye na biyu da za a gudanar a qasar a jibi Lahadi, bayan Mista Dinan Ogan, wanda ya zo na uku a zagayen farko na zaven ya sanar da goyon bayansa ga Shugaban.

A wani taron manema labarai da Ogan ya kira a Ankara ne ya sanar da matsayarsa tare da neman xaukacin magoya bayansa su zavi Erdogan a zagaye na biyu na zaven da za a gudanar a jibi Lahadi, matakin da ke nuna yiwuwar Shugaba Erdogan na iya samun nasara lura da cewa dama ya samu kashi 49.3 na yawan quri’un da aka kaxa maimakon kashi 50 da ake buqatar xan takara ya samu.

Recep Tayyib Erdogan wanda ke shugabancin Turkiyya tun shekarar 2003 na buqatar rinjayen quri’u kafin ya yi nasara a zaven da zai ba shi damar zaman Shugaban Qasa a karo na biyar, wanda hakan zai ba shi damar sake jan ragamar qasar zuwa shekara biyar a nan gaba.

Janyewar ta Ogan za ta taimaka wa Erdogan a zagaye na biyu na zaven da ke tafe wanda shi ne irin sa na farko a tarihi da mutanen qasar Turkiyya ke kaxa quri’a a zagaye na biyu na zaven Shugaban Qasa.

Erdogan yana fuskantar qalubale daga babban mai adawa da shi, wato Mista Kemal Kilicdaroglu wanda ya samu kashi 45 na yawan quri’un da aka kaxa, kuma hakan ne ya sa ake ganin Kemal a matsayin babban mai barazana ga Erdogan da jam’iyyarsa ta masu Kishin Addinin Musulunci.

TARE DA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281951727188960

Media Trust Limited