dailytrust

[ Jarru da axafi (1)

Salihu Maqera simakera@dailytrust.com

Arubutunmu na baya, mun tavo abubuwan da suka shafi sunayen unguwannni da garuruwa da qasashe, waxanda suke da suna a Hausa kafin zuwan Turawa da harshen Ingilishi. Haka mun tavo yadda zamananci da qaqale-qaqale suka sa waxansu marubuta canja yadda ake rubuta sunayen daga Hausa zuwa yadda ake rubuta su da baqaqen Ingilishi. Kamar Aminu sai a rubuta Ameenu ko Jamil a rubuta Jameel da sauransu.

To yau cikin yardar Allah za mu duba wasu batutuwa biyu ne da suka shafi rubutun Hausa; wato Jarru da Axafi.

Waxannan abubuwa biyu wasu kalmomi ne da ake amfani da su yayin rubutu da Hausa don bambancewa ko sadarwa ko nuni ko zarfu yayin rubutu.

Jarruruka:

Jarruruka na nufin jam’in Jarru tilo ke nan, idan suka kai biyu zuwa sama ana kiransu Jarruruka, sun samo sunansu ne daga Harshen Larabci, amma akwai bambanci kan yadda Larabawa suke amfani da su da yadda ake amfani da su a Harshen Hausa.

Farfesa Hambali Junju (1981) ya faxi a cikin littafinsa Rayayyen Nahwun Hausa cewa Jarru su ne:

a da wa da ga da gare da da da daga da ban da da sai da cikin da wajen da saboda da garin da a kan/kan da a bakin da maimakon da bigiren/bagiren da gaban da bayan da qarqashin da bisan/bisa da tsammanin da tsakanin da tsakar/tsakan da zuwa.

Idan za mu sanya su a jumla sai mu rubuta su kamar haka:

Ya daxe a kasuwa ko a gona ko a makaranta.

A zuba wa gona taki, kuma a gaya wa Musa ya kai takin.

Zafin zuciya ke ga Audu Kande fushi gare ta.

Ni da kai, shi da ita.

Babu mai yi masa haka sai kai.

A kai musu amma ban da na Musa. Za mu zo saboda kai.

Ya faxi ne garin gudu.

Bai xauke shi a bakin komai ba. Duk abin da suke yi bayan sun gan ku ne.

Tsuntsun yana bisa itaciyar.

A duba bigiren sosai yana nan. Yana zaune a tsakanin qauyukan biyu ne.

Daga gidan zuwa wurin ba nisa. Faxakarwa:

Junju ya qara da cewa: Kalma da ana amfani da ita a halaye da dama misali:

1. da axafi ne kuma zarafi ne; misali: da in yi sata gwamma in mutu da yunwa.

2. da lamirin dangantaka ne; mutumin da ya zo.

3. da na bayyana mallaka; suna da kaya da yawa.

4. da na zuwa gabanin sunaye har a samu siffofi ko zarufa; da sauqi; da dama; da sannu; da wuri.

5. da na zuwa bayan fi’ilai a samu fi’ilan musabbabi; bayyanar da; jefar da; watsar da; mayar da; miqar da.

MAKARANTA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281977496992736

Media Trust Limited