dailytrust

Manjo Janar Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya na 7 da 15

Daga Maude Rabi’u Gwadabe

Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) shi ne mutum na biyu da ya mulki Najeriya a matsayin soja da kuma farar hula. Kuma shi ne na biyu a daɗewa a kan kujerar mulkin Najeriya.

Lokacin da ya yi mulkin soji ya yi aiki ba-sani ba-sabo, musamman wajen yaƙi da cin-hanci da rashawa, inda ya yi ta ɗaure tsofaffin ’yan siyasa da ’yan kwangila.

Sannnan ya tilasta wa kowa da kowa bin doka ƙarƙashin shirinsa na Yaƙi da Rashin Ɗa’a (WAI).

Bayan shekara guda da watanni soji suka yi masa juyin mulki, lamarin da ya sa wasu ke ganin da an ba shi dama da Najeriya ta ci gaba.

Don haka lokacin da mulki ya koma hannun farar hula a 1999, sai ’yan Arewa suka fara fatan Allah Ya dawo da shi kan mulki.

Sai dai sau uku yana ta faɗuwa a zaɓe daga 2003 zuwa 2011. Sai a zaɓen 2015 ya yi nasarar cin zave kuma ya yi tazarce a 2019.

A ƙarƙashin mulkinsa an shiga ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziki da ƙaruwar rashin tsaro da cin-hanci da rashawa.

Kuma da yake sai a shekarar 2023 ɗin nan ne yake kammala mulkinsa, kawo yanzu lokaci bai yi ba da za a iya tantance dalilan da suka sa ya yi faɗuwar baƙar tasa a idon al’umma ba.

Asali

An haifi Muhammadu Buhari ranar 17 ga Disamban 1942 a ƙauyen Dumurƙol da ke Daura a Jihar Katsina ta yanzu.

Mahaifinsa Harɗo Adamu Bafulatani ne, mahaifiyarsa Zulaiha kuma Bahaushiya ce.

Yana da shekara shida aka sa shi a makarantar firamare ta Daura. A 1953 Muhammadu Buhari ya shiga Makarantar Midil ta Katsina, inda bayan shekara biyu sai gwamnatin mulkin mallaka ta soke karantun Midil, ta koma tsarin cikakkiyar firamare.

Don haka, a 1955 Muhammadu Buhari ya zama cikin sahun farko na ɗaliban makarantar firamare ta Kankiya.

A 1956 ya kammala firamare, ya shiga makarantar sakandare ta Lardin Katsina, wacce daga baya aka sauya mata suna zuwa Kwalejin Gwamnati ta Katsina (*RYHUQPHQW &ROOHJH . Kafin ya kammala makarantar kuma sai da ya riƙe muƙamin shugaban ɗalibai.

Aikin soji

Muhammadu Buhari ya fara aikin soji a 1962 a Kwalejin Horar da Soji da ke Kaduna.

Daga nan ne aka tura shi Kwalejin Horar da Hafsoshin Soji ta Mons Officers Cadet School da ke Aldershot a Ingila.

A watan Janairun 1963 ya fito da anini guda, inda aka tura shi Bataliyar Sojin Qasa ta Biyu da ke Abeokuta.

Daga 1964 aka mayar da shi Legas a matsayin hafsa mai kula da harkokin sufuri.

Yana wannan aikin ne aka yi juyin mulkin farko a Janairun 1966, kuma yana cikin sojin da suka murƙushe wannan yunƙuri.

Bayan juyin mulki a watan Afrilun 1966 aka ƙara masa girma zuwa Laftanar, inda aka tura shi Abeokuta a matsayin hafsa mai kula da sufuri da kayan amfanin yau da kullum na Bataliyar.

Yana cikin sojojin da suka shirya juyin mulkin ɗaukar fansa na watan Yulin 1966.

Yaƙin Basasa

Muhammadu Buhari na daga cikin kwamandojin da suka fafata a Yaƙin Basasa a tsakanin Gwamnatin Tarayya da haramtacciyar ƙasar Biyafara.

Rundunarsu ce ta ƙwato Gakem da Ogoja da Ikom. Ana cikin yaƙin ne aka ƙara masa girma zuwa Kyaftin a Janairun 1968.

Daga Ikom Kyaftin Muhammadu Buhari ya jagoranci rundunar da ta ƙwato Abaomege da Eha-Amufu da Ogidi, inda daga nan suka dangana da Onitsha, suka ƙwato ta ƙarƙashin Birgediya Murtala Mohammed.

A 1973 ya je kwas a Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soji da ke Wellington a Indiya.

Bayan dawowarsa ya zama Daraktan Sufuri da Samar da Kayan Amfani na Rundunar Sojin Najeriya. Yana kan wannan muƙami ne ya zama Kanar.

Mulkin Soji

Kanar Muhammadu Buhari na daga cikin sojin da suka yi wa Janar Yakubu Gowon juyin mulki, inda suka maye gurbinsa da Birgediya Murtala Mohammed a watan Yulin 1975.

Shi kuma Murtala sai ya naɗa Buhari Gwamnan Mulkin Soji na Jihar Arewa maso Gabas, wacce ta ƙunshi jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe na yanzu.

Sai dai bayan wata shida Janar Murtala ya raba jihar zuwa Borno da Gongola da Bauchi. Don haka Kanar Buhari ya zama Gwamnan Mulkin Soji na Jihar Borno na farko a ranar 3 ga Fabrairun 1976.

Kwana 10 bayan ƙirƙiro sababbin jihohi wato 13 ga Fabrairun 1976 soji suka kashe Janar Murtala Mohammed a yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Don haka magajinsa, Janar Olusegun Obasanjo ya ɗauke Buhari daga Maiduguri ya naɗa shi Kwamishinan Tarayya wato Minista a yanzu a Ma’aikatar Albarkatun Man fetur.

A zamaninsa ne aka haɗe Ma’aikatar Man fetur da Kamfanin Fetur na Qasa wato NNOC aka samar da sabon Kamfanin NNPC, inda ya zama shugabansa na farko.

A 1977 ya zama Sakataren Soji na Majalisar Ƙoli ta Mulkin Sojin Najeriya kuma a watan Agustan 1978 aka ƙara masa girma zuwa Birgediya.

A watan Yunin 1979 lokacin da ake shirin miƙa mulki ga farar hula aka tura shi Kwalejin Horar da Dabarun Yaƙi ta Sojin Amurka da ke Jihar 3HQQV\OYDQLD inda ya kammala a Yunin 1980 zamanin mulkin Shugaban Qasa Alhaji Shehu Shagari.

Babban Kwamanda

A 1980 ya zama Babban Kwamanda wato GOC na Rundunar Sojin Najeriya ta Huɗu.

A 1981 kuma ya koma GOC a Rundunar Sojin Najeriya ta Biyu.

Daga nan kuma sai Rundunar Sojin Najeriya ta Uku daga Oktoban 1981 zuwa Disamban 1983.

A watan Maris 1983 Alhaji Shehu Shagari ya ɗaga darajarsa zuwa Manjo Janar.

A ranar 18 ga Afrilun 1983 kuma sojin Chadi suka kawo farmaki Najeriya har suka ƙwace wasu ƙananan tsibirai 18 da ke kan iyakarta da Chadi.

Nan da nan Manjo Janar Buhari ya rufe iyakar Najeriya da Chadi ba tare da izinin gwamnati ba.

Babban Hafsan Sojin Najeriya Leftanar Janar Muhammad Inuwa Wushishi da Shugaban Qasa Alhaji Shehu Shagari duk sun umarce shi da ya buɗe iyakar, amma ƙememe ya ƙi har sai da ya yi nasarar ƙwato gaba ɗaya yankunan da Chadi ta mamaye. Tun daga nan jami’an leƙen asiri na soji suke zargin akwai abin da ya taka.

Ilai kuwa ranar 31 ga Disamban 1983 soji suka kifar da gwamnatin Shagari, inda suka sanar da Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin sabon Shugaban Mulkin Sojin Najeriya.

Shugaban Mulkin Soji

Manjo Janar Muhammadu Buhari tare da Mataimakinsa Birgediya Tunde Idiagbon sun yi mulkin shekara guda da wata takwas kafin a kifar da gwamnatinsu.

Gwamnatin ta samar da dokokin da za su taimaka mata wurin gudanar da ayyukanta.

Waɗanda suka fi ƙaurin suna su ne doka ta Biyu da ta Huɗu.

Doka ta Biyu ita ce ta bai wa jami’an tsaro ikon kama duk wanda suke zargin yana barazana ga ɗorewar gwamnati.

Doka ta Huɗu kuma ta ba da ikon kama duk wanda ya ba da labarin ƙarya ko jita-jita game da gwamnati ko jami’anta.

Haka kuma gwamnatin mulkin soji ta Janar Buhari ta haramta yajin aiki da zanga-zanga.

Manjo Janar Muhammadu Buhari ya kama ’yan siyasa da ’yan kwangila fiye da 500 kuma kotunan soji da ya kafa sun yanke wa da yawansu hukuncin ɗaurin ɗaruruwan shekaru a kurkuku.

A ɓangaren tatalin arziki, Janar Muhammadu Buhari ya rage kuɗin da gwamnati ke ɓatarwa ta hanyar sallamar dubban ma’aikata, da dakatar da aiwatar da duk wani sabon aiki. Haka ya haramta wa gwamnatocin jihohi cin bashi, ya hana shigo da kaya daga ƙasashen waje, amma ya ba da ƙofar shigo da na’urori domin a kafa masana’antu a cikin gida.

Hakazalika, ya yi canjin kuɗi cikin gaggawa domin tilasta wa ɓarayin gwamnati su fito da kuɗin da suka ɓoye.

Sai dai tasirin canjin ya ƙare ne kan mawadatan da ba su saba harka da banki ba, inda da yawansu suka haɗu da karayar arziki.

A ranar 20 ga Maris na 1984 Gwamnatin mulkin soji ta Janar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar

da shirin ‘War Against Indiscipline’, wato Yaƙi da Rashin ɗa’a.

Dokar ta tilasta tsaftar muhalli da bin dokokin tuƙi da shiga layi wurin hawa motar haya da zuwa aiki a kan kari da kuma yaƙi da cin -hanci da rashawa.

A watan Afrilun 1984 ya rufe iyakokin Najeriya da ƙasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Benin. Wannan lokacin ne aka shiga halin matsi da yunwa da aka yi wa laƙabi da Buhariyya, amma bayan shekara guda ya haƙura ya buɗe iyakar saboda galabaita da al’umma suka yi ta jawo ƙaruwar aikata laifuffuka.

Yi masa juyin mulki

A ranar 27 ga Agustan 1985 Babban Hafsan Sojin Qasa na Najeriya Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Janar Buhari juyin mulki.

Da misalin ƙarfe biyun dare hafsoshin soji masu muƙamin Manjo-Manjo da suka haɗa da Abdulmumini Aminu da Lawan Gwadabe da John Madaki suka kutsa kai zuwa Fadar Shugaban Qasa ta Dodan Barracks, inda suka sanar da shi cewa, an yi masa juyin mulki kuma sun zo su kama shi.

Sai bayan shekara uku a cikin watan Disamban 1988 aka sake shi ya koma mahaifarsa Daura kafin daga baya ya koma gidansa da ke Kaduna.

Bayan ya koma gida ne ya saki uwargidansa Safinatu, inda ya maye gurbinta da A’isha Halilu, Bafulatanar Adamawa a watan Disamban 1989.

Bayan Janar Abacha ya zama Shugaban Mulkin Soji a Nuwamban 1993, sai ya kafa Asusun Rarar Man Fetur (PTF).

Janar Abacha ya naɗa Buhari shugaban wannan asusu wanda ya bunƙasa harkokin sufuri da kiwon lafiya da ilimi.

PTF a ƙarƙashin Buhari ta samar da ayyuka masu inganci ƙwarai wanda har yanzu ana amfana da wasunsu.

Jamhuriya ta Huɗu

A shekarar 2002 ’yan siyasar Arewa da ke adawa da Obasanjo musamman waɗanda suka ɗasa da Abacha suka nemi Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya fito takarar Shugaban Qasa.

A zaɓen 2003 ya yi takara a

Jam’iyyar ANPP, amma Shugaba Olusegun Obasanjo na PDP ya kayar da shi da ratar fiye da ƙuri’a miliyan 11.

A shekarar 2007 ya sake takara a ANPP, inda gwamnan jiharsu ta Katsina, Umaru Musa ’Yar’aduwa na Jam’iyyar PDP ya kayar da shi.

Sakamako ya nuna cewa, Buhari ya samu kaso 11 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa yayin da ’Yar’aduwa ya samu kaso 70 cikin 100.

Muhammadu Buhari ya fice daga Jam’iyyar NNPP, ya kafa tasa ta kansa mai suna CPC.

A zaɓen 2011 ma dai kwatawa aka sake yi domin kuwa Goodluck Jonathan na PDP ne ya yi nasara a kansa.

Bayan wannan zaɓe ne magoya bayansa suka yi ƙoneƙone da kashe-kashe domin nuna adawarsu da maguɗin da suke zargin an tafka masa.

Shi kuma ya yi iƙirarin cewa ba zai ƙara takarar Shugaban Qasa ba.

Amma duk da haka ’yan siyasa sun taushe shi bayan jam’iyyun adawa na ACN da ANPP da CPC tare da wani tsagi na APGA da PDP sun dunƙule sun kafa Jam’iyyar APC.

A zaɓen 2015 ya yi takara a ƙarƙashin APC, inda ya kada Shugaban Qasa Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP.

Wannan ne karo na farko a tarihin Najeriya da aka taɓa kada Shugaban Qasa mai ci a zaɓe.

Shugaban Qasa

Muhammadu Buhari ya samu shekara takwas a shugabancin Najeriya na farar hula bayan ya sake samun nasara a zaɓen 2019.

Ya sha fama da rashin lafiya musamman a farkon mulkinsa, abin da ya sa aka yi ta yi masa uzuri kan kasa cika alƙawuran da ya ɗauka.

Ya kassara Boko Haram, amma ’yan awaren Biyafra wato IPOB da masu garkuwa da mutane sun yi ƙarfi a zamaninsa

Haka ya rufe iyakakokin ƙasa domin bunƙasa aikin noma da sarrafa kayan abinci.

Sai dai hakan ya jefa tattalin arziki cikin halin matsi.

A zaɓen 2023 jam’iyyarsa ta APC ta yi nasara duk da dai ana ganin ya ɗauki wasu matakan yi mata zagon ƙasa.

TUNA BAYA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282024741632992

Media Trust Limited