dailytrust

Asalin Hausawa (9)

[Waxari Waxari Tare Tare da da IbIrbarhaihmimMMalaulmumfafsahsihi mfashi@yahoo.com mfashi@yahoo.com (MAIMAITAWA)

Ya zuwa yanzu tambayoyi da yawa na san sun fara karakaina a zukatun masu karatu, musamman ganin cewa an fita daga fagen da aka saba da shi na nazarin tarihi da tarihihi da kuma bayanan kunne-ya-girmi-kaka da tarihin-tarihi, an koma cikin fagen kimiyya domin samun haske. Yin haka shi ne abin da ya fi komai dacewa a halin yanzu, ba don komai ba sai ganin cewa yanzu binciken sanin asali ya wuce batun haƙar kufai da bibiyar littattafai da takardun da aka ajiye tun tale-tale, an koma ga batun abin da Allah Ya ajiye a jikin halittarsa ta asali, wato ƙwayar halitta.

Ƙila tambayar da wasu za su fara yi ba ta wuce yaya aka yi Hausawa suka samu shiga cikin wannan fagen nazari da bai gama game duniya ba, musamman dangane da neman sanin asali? Amsar dai ba mai wahalarwa ba ce in aka yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a wannan fage a duniyar nazarin asalin ’yan Adam.

Tun a shekarar 2007, a lokacin da na kai ziyarar bincike a Ingila na ci karo da wannan sabon fage na nazarin ƙwayar halitta domin gano asalin ’yan Adam na National Geographic Society da aka ƙaddamar a Amurka a 1888, tare da haɗin gwiwar Genographic Project da aka soma gudanarwa a shekarar 2005, shi ma a Amurka, suka soma. A daidai wannan lokaci na karanci lamarin da kyau, na kuma fahimci cewa bincike ne da zai agaza wajen gane yadda al’ummar duniya ta samo asali daga tushe guda da kuma yadda al’ummar ta hayayyafa yau zuwa sama da mutum biliyan bakwai a doron ƙasa.

Ganin irin yadda aka tsara batun, ya sa a shekarar 2016 na kai ziyara birnin Washington da ke Amurka, hedikwatar National Geographic da kuma Genographic Project, inda aka ɗebi yawu daga cikin bakina, na kasance ni ne na dubu 779 da 696 daga cikin al’umma daga sassan duniya da suka amince su shiga cikin wannan tsari na binciken asalin ’yan Adam, domin a fitar da wani ɓangare na asalin Hausawa daga ahalina.

A shekarar 2018 kuma an sake ɗibar yawun nawa domin ƙara tabbatar da abubuwan da aka ci karo da su a can baya. Masana kimiyyar ƙwayar halitta sun bi diddigin dubban ’ya’yan ƙwayoyin halittar daga wannan yawu nawa, ta haka suka fasalta yadda zuriyar ahalina ta kasance cikin tarihi, suka kuma nuna yadda kakannin-kakannina suka yi tattaki a doron ƙasa a tsawon zamani, ta ɓangaren mahaifina.

Abu na farko da aka gani daga cikin wannan nazari shi ne, ni da sauran Hausawa ba mu da ko ɗigon jinin Turawa a rayuwarmu, ke nan kakanninkakannina da kuma sauran Hausawa ba su yi auratayya da Neanderthal ba, waɗanda suke ɗauke da kaso mafi tsoka na ƙwayar halittar al’ummar yankin Turai.

Tun asali masanan ƙwayar halittar sun riga sun fito da wata bishiya ta asalin dukkan ’yan Adam a yau, inda suka nuna duk wani ɗan Adam da ke shaƙar iska yana da reshe a jikin wannan bishiya.

Daga cikin ƙwayar halittata da aka yi nazari aka gano reshen da nake kai, wanda yake kuma reshe ne na Hausawan wannan zamani. Daga wannan dogon nazari an fitar mani da bayani gamsasshe da ya bayyana kakannina, aƙalla hula shida a baya. Wannan bincike shi ne ya nuna abin da ke ƙunshe cikin ƙwayar halittata ta asali da kuma yadda ta gwamutsu da wasu daga baya a tsawon dubban shekaru.

Kamar yadda muka gani a bayanan baya, ni da sauran ’yan uwana Hausawa al’umma ce da ke zaune yanzu a sassan Yammaci da Tsakiyar Afirka, amma domin a san asalin ’yan uwana da kuma sauran Hausawa an gwada ƙwayar halittata da ta wasu da ke cikin bankin ƙwayoyin halittu da ke ajiye a ɗakunan binciken da ke can Amurka. An yi haka ne domin a fahimci su wa ke da irin tawa ƙwayar halittar, domin ta haka ne za a gane ’yan uwana da na sauran Hausawa.

Sai dai a lura binciken ba yana nufin cewa duk ƙwayar halittar da ta yi kama da tawa ’yan uwa muke ba ko kuma ’yan uwan Hausawa ba ne, kamanci ne na lissafin asali, wanda zai iya kaiwa ga dangantaka ta ƙuƙut ko kuma raragefe.

Ya zuwa yanzu me ya rage a yi domin ƙara tabbatar da wannan bincike? Kamar yadda masanan suka yi nuni sai an sake samun wasu daga cikin al’ummar Hausawa sun shiga cikin wannan tsari na bincike, tattare da sauran ’yan uwa da aka bari a can baya a lokacin yawon duniya da tattaki na Hausawa a doron ƙasa a tsawon zamani.

Ma’ana, a samu wasu daga cikin al’ummar Asiya da Saudiyya da al’ummar Siwa da wasu mazaje daga Kudancin Masar da Yahudawan Afirka da wasu daga al’ummar ƙasar Aljeriya da Maroko da Sudan da Libya da Nijar da Chadi da Mali da Muriteniya da Kamaru da Habasha da qasar Afirka ta Tsakiya, tsundum a cikin wannan nazari.

Yin haka zai ƙara haskaka turbobin da kakannina da na Hausawa suka bi a lokacin da suke bisa hanyar zuwa inda suke a yanzu, ta ɓangaren uba. Duk lokacin da aka samu irina daga sassan duniya suka shiga wannan tukunyar bincike, to za a ƙara samun haske game da asalin Hausawa fiye da wanda ake da shi a halin yanzu. Ke nan idan har muna son mu san inda dangantaka ta ƙuƙut ta kasance tsakaninmu da sauran al’ummar sassan duniya sai an yi abubuwa uku.

Na farko a ƙara miqa wannan binciken da aka yi wa ƙwayar tawa halittar ga masu binciken ƙwaƙwaf na Science (kimiyya) don su kamanta da sake kwatantawa da nasu bankin ƙwayar halittun.

Na biyu, a samu ’yan sa-kai daga Hausawa da madangantan Hausawa daga sassan duniya daban-daban da za su shiga wannan tsari na binciken ƙwayar halitta don sanin asalin Hausawa, ana kuma buƙatar aƙalla mutum 3,000 kafin a ci dunun binciken.

Na uku, a kuma kalli ɓangaren uwa ko mahafiya, a ga yadda shi kuma ya malƙayo cikin tarihin, domin ta haka ne za a ga hoton asalin nawa da sauran al’ummar Hausawa fiye da wanda muke da shi a yanzu.

TUNA BAYA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282033331567584

Media Trust Limited