dailytrust

Rantsar da sabon Shugaban Qasa Tinubu a gata

Kwanci-tashi ba wuya a wajen Allah yanzu ga shi gata Litinin ake bikin rantsar da sabon zavavven Shugaban Qasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki a gwamnatin tsakiya a matsayin Shugaban Qasa na biyar a wannan mulkin na dimokuraxiyya da qasar nan ta dawo a 1999, cikin yardar Allah ba tare da an samu katsandan ko kutse daga sojoji ba.

Tuni don samun nasara da tabbatar da matakan tsaro a yayin bikin daga yau an rufe wasu muhimman hanyoyi a Abuja, Babban Birnin Tarayya da ba za a buxe ba har sai ranar Talata bayan bikin rantsuwar. A ranar Litinin mai zuwa za a yi irin wannan biki a manyan biranen jihohi 28, don rantsar da sababbin zavavvun gwamnoni jihohi da waxanda suka sake lashe zaven zango karo na biyu na mulkinsu. Sauran gwamnonin jihohi takwas kuwa a lokata daban-daban ake yin zavensu bisa ga hukunce-hukuncen kotuna a baya.

Masana tattalin arziki da na siyasa da na zamantakewar xan Adam, sun tabbatar da cewa a cikin mulkinsa na shekara takwas Shugaban Qasa Muhammadu Buhari mai barin gado ya yi qoqarin vullowa da aiwatar da tsaretsaren tattalin arzikin qasa masu ximbin yawa, amma haqarsa ba ta cim ma ruwa ba wajen kawo qarshen wasu daga cikin matsalolin da ya gada ko waxanda suka faru a zamaninsa, waxanda gwamnati Tinubu za ta gada.

Akwai tarin irin waxannan matsaloli da suka haxa da tavarvarewar tsaro da kullum suke qara xaukar sabon salo da janye tallafin man fetur da ximbin basussukan cikin gida da waje da ake bin qasar nan da shirin sake fasalin wasu daga cikin takardun kuxin qasar nan. Sauran sun haxa da matsalar wutar lantarki da rashin aikin yi da qidayar jama’a da sauransu.

Dukkan waxannan matsaloli da na ambata a sama da waxanda ban iya ambata ba, za su zama matsalolin da Shugaban Qasa mai jiran gado Alhaji Bola Ahmed Tinubu zai gada daga gwamnatinsu ta APC daga waccan rana ta 29 ga wannan wata, da fatar kuma a waccan rana ’yan qasa za su ji daga jawabinsa inda gwamnatinsa za ta sa alqiblarta don samun sauqi ko kawo qarshen matsalolin baki xaya.

Don kuwa an ce wai daga irin mutanen da zai naxa ministoci da sauran muqarraban gwamnatinsa, Shugaba Tinubu yana da burin ganin cewa gwamnatinsa ta sha bamban da duk wata gwamnati da aka tava yi tunda aka fara wannan jamhuriyar, wajen inganta tattalin arziki da rayuwar jama’ar qasa.

Yanzu bari mu dawo kan wasu daga cikin waxancan matsaloli da Shugaba Tinubu zai gada. Alal misali, batun matsalar janye tallafin farashin man fetur, tsohuwar matsala ce da shugabanni ke xari-xari wajen tunkararta gaba-da-gaba, duk da irin matsin lambar da sukan samu daga Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) da wasu masana tattalin arzikin qasa na cikin gida da suka a kan cewa wasu ’yan tsiraru ke amfana da tallafin.

Gwamnatin Shugaba Buhari da ta gaji batun tallafin man fetur daga gwamnatin tsohon Shugaban Qasa Dokta Goodluck Jonathan, a bara ta sha alwashin cewa daga qarshen watan Yunin bana za ta janye tallafin har bashin Dalar Amurka miliyan 800, ta ciwo da sunan za ta raba wa mutum miliyan goma, masu qaramin qarfi a matsayin agajin janye tallafin man fetur xin.

Amma yanzu gwamnatin ta janye waccan aniya tana mai cewa ta bar batun hannun gwamnati mai shigowa. Hatta waccan bashin Dalar Amurka miliyan 800, za a miqa shi ga sabuwar gwamnatin don ta san na yi.

Haka batun qidayar jama’a, qidayar da qasashen duniya kan yi don sanin irin tanadetanaden da ya kamata su yi wa ’yan qasa walau a fannin ilimi ko kiwon lafiya ko samar da ruwan sha da makamantan muhimman buqatu. Bisa ga tsarin Majalisar Xinkin Duniya, ya kamata qasashe su riqa gudanar da qidayar jama’arsu bayan kowace shekara goma. Mu yau shekara 17 ke nan har da xoriya ba mu yi qidayar jama’armu ba, tun wadda aka yi a shekarar 2006.

Hukumar Qidaya ta Qasa ta shirya gudanar da qidayar jama’a a ranar 3 zuwa 7 ga wannan wata, sai kawai da rana-kata Shugaba Bahari, bayan wata ganawa da ya yi da wasu daga cikin ministocinsa da shugabannin hukumar qidayar, ya ba da shelar xage gudanar da shirin qidayar har sai sabuwar gwamnati ta shigo.

Sai batun matsalar rashin aikin yi, wadda ta zama wata babbar matsala da ta addabi musamman matasan qasar nan. Hukumar Qididdiga ta Qasa (NBS) a cikin rahotanta, ta tabbatar da cewa a shekarar 2022, yawan marasa aikin yi ya kai kashi 33 cikin 100.

Shi kuwa Kamfanin KPMG cewa ya yi rashin aikin yi ya qaru da kashi 37.7 cikin 100 a shekarar 2022, ya qara da cewa nan da xan wani lokaci zai iya qaruwa zuwa kashi 40 cikin 100, bisa ga qaruwar da masu neman aikin suke yi a kullum.

Matsalar canja takardun kuxin qasar nan na Naira 200 da 500 da 1,000 da Babban Bankin Qasar nan ya yi tsakanin 15 ga Disamban bara zuwa 31 ga Janairun bana ma ta qara kawo koma bayan tattalin arzikin qasar nan, al’amarin da ya kai matsayin sai da cinikayya ta gagara.

Qarshe dai qarar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar a Kotun Qoli ita ta kawo qarshen wa’adin 31 ga Janairun da Babban Bankin ya gitta na ranar qarshe ta canjin kuxin, bayan da Kotun Qolin ta yanke hukuncin a ci gaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun kuxin kafaxa-da-kafaxa, har zuwa ranar 31 ga Disamba mai zuwa. Abin jira a gani shi ne irin yadda sabon Shugaban Qasa zai vullo wa wannan muhimmin batu.

Akwai kuma batun tavarvarewar tsaro kama daga rikicin Boko Haram da ya gallabi jihohin Arewa maso Gabas yau sama da shekara 12, zuwa rikicin ’yan bindiga da masu satar mutane don neman kuxin fansa da yanzu ya xan lafa a shiyoyin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, amma kuma yake qara shiga cikin sauran shiyoyin Kudancin qasar nan, baya ga tashe-tashen hankali na ’yan haramtacciyar qungiyar aware ta Biyafara (IPOB) da ake fama da shi a Kudu maso Gabas.

Tavarvarewar tsaro da ya gallabi jihohin Arewa ya sa wasu ’yan Arewa a lokacin kamfen suka riqa kamfen xin sai a zavi xan Arewa a matsayin Shugaban Qasa saboda fargabar da suke da ita ta cewa tunda Shugaba Bahari xan Arewa ya kasa shawo kan matsalolin tsaro a Arewa, to yaushe xan Kudu in ya ci zave zai iya shawo kan matsalar.

Alqalami dai ya riga ya bushe, ga sabon Shugaban Qasa Tinubu za a rantsar da shi, ’yan qasa kuma sun zuba idanu wajen ganin yadda zai tunkari waxannan matsaloli na tattalin arziki da na zamantakewa da yadda zai shawo kansu.

Jama’ar qasa a irin wannan lokaci sai mu ci gaba da addu’o’in kada Allah Ya ci gaba da jarrabarmu da waxannan matsaloli, ta yadda ba za mu dawo muna cewa gwamma gwamnatin Buhari ba. Amin summa amin da fatar a yi bukukuwa lafiya.

TUNA BAYA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282037626534880

Media Trust Limited