Muhimmancin inganta noma don samar da aikin yi ga matasa

Daga Yakubu Liman

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

Media Trust Limited

https://dailytrust.pressreader.com/article/282041921502176

TUNA BAYA

Yayin da ake shirin rantsar sabuwar gwamnatoci a wasu jihohi da kuma tarayya, babban abin da jama’a suke fata gwamnatocin su yi hanzarin yi shi ne maganin matsalar rashin aikin yi da ake ganin shi ke haddasa aikata manyan laifuffuka a qasar nan. Shugaba Muhammadu Buhari wanda wa’adin mulkinsa ke qarewa a makon gobe, yake qoqarin miqa mulki ga Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya yi alqawarin samar da aikin yi ga ximbin ’yan Najeriya a farkon kama mulkinsa, wanda hakan zai fitar da miliyoyin ’yan Najeriya musamman matasa daga qangin fatara. Sai dai maimakon cika wannan alqawari sai wasu ginshiqai da suke haifar da rashin aikin yi suka riqa faruwa, kamar rufe masana’antu da faxuwar darajar Naira, waxanda suka daqile buxi ko bunqasar harkar da za ta samar da gurbin aiki, in ban da harkar noma da kiwo ga masu jari. La’akari da haka ya zama wajibi sababbin gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi da qananan hukumom su mayar da hankali bayan kama ragamar mulki wajen samar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a ta hanyar samar da aikin yi ta amfani da harkar noma da raya karkara. Fitinar ’yan ta’adda ko ’yan bindiga da masu sace mutane a qasar nan musamman a Arewa ta kusa tsayar da harkar noma da sana’o’i ga xaixaikun mutane da kuma durqusar da samar da aikin yi baki xaya, hakan ba qaramin naqasu ba ne ga tattalin arzikin yankin da qasa baki xaya. Harkar noma a Arewa tun daga sharar gona da shuka zuwa girbi d alkinta amfani da gyara da kuma inganta shi domin sayarwa a kasuwanni don amfanin cikin gida da kuma fitar da shi waje, abu ne da ake yin sa shekara da shekaru, amma lamarin ya ja baya matuqa a yanzu saboda dalilai da yawa. Ba a Arewa kaxai ba, a duk yankuna da shiyyoyin Najeriya ba a rasa wani amfanin da ake noma shi, wanda tun daga shuka zuwa girbi, zuwa kai shi kasuwa da kuma fitar da shi, zuwa qasashen waje da ke samar da aikin da kuxin shiga ga jama’a. A shekarun baya an ci kasuwar amfanin gona irin su gyaxa da koko da qwarar manja a qasashen waje, yanzu kuma ga shinkafa da masara da rogo da man kaxe da citta da barkono da sauransu da za a iya fitar da su waje wanda hakan zai kawo wa qasar nan alfanu ta fuskar kuxin musaya da samar da aikin yi. Ya kamata sabbin gwamnatoci su yi amfani da wannan dama ta fitar da kayayyaki ta hanyar haxa hannu da ’yan kasuwa da manya da qananan kamfanoni wajen fito da tsarin da ya dace, wanda hakan baya ga kuxin shiga zai taimaka wajen samar da aikin yi. Koko da shi ake yi cakulati da kuma man koko na shafawa da kayan maqulashe. Daga qwarar manja ake samun man girki da jambaki da man gyaran gashi da ayis kirim da sabulan wanka da na wanki da sauransu. Kamar yadda ake samar da man girki daga man gyaxa da gurya da rixi bayan ga samar da magunguna da sauran kayan abinci.

ha-ng