dailytrust

Arewa ta mai da hankali kan Noma da kasuwanci maimakon siyasa — Audu Ogbe

Daga Yakubu Liman

Tsohon Ministan Noma da Raya Karkara kuma tsohon Shugaban Qungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), Cif Audu Ogbe ya yi kira ga ’yan Arewa kan su ajiye harkar siyasa su rungumi harkar noma ka’in-da-na’in a matsayin sana’a.

Tsohon Ministan ya ce siyasa kaxai ba ta kawo ci gaban kowace al’umma, kuma qungiyar ta damu matuqar kan qarancin harkokin samar da kuxi a Arewa.

Mista Ogbe ya faxi haka ne a jawabinsa na ban-kwana a matsayin Shugaban ACF a taron qungiyar da aka gudanar a makon jiya, don miqa wa sabon Shugban Qungiyar Mista Gabriel Aduku sakamakon qarewar wa’adinsa na shekara uku.

Mista Audu Ogbe ya bayyana takaicinsa kan yadda ’yan kasuwar Arewa sai sun yi tafiya zuwa Legas don yin kasuwanci saboda rashin ci gaban kasuwancin na manyan masana’antu a Arewa.

“Muna fama da koma-baya a fannin ilimi da harkokin tattalin arziki. Ba mu da bankuna domin kusan duk bankunanmu an sayar da su a shekarun 2003 zuwa 2005. Don haka yana da matuqar wahala ga xan kasuwa xan Arewa ya yi harka yadda ya kamata.

“Dole sai ya tafi Legas, saboda tsalle muke yi muna direwa a wuri xaya ta fuskar masana’antu. Idan kuwa ba mu da ci gaban masana’antu ba za mu samar da aikin yi ba. Harkar noma ta tavarvare saboda fitinar kashe-kashe da garkuwa da mutane.

“Dole ne mu dawo da martabarta na kasuwanci, siyasa kaxai ba ta ciyar da al’umma gaba, waxannan su ne matsalolinmu,” in ji shi.

Dattijon ya ce ya yi murna da abin da ya gani dangane da abubuwan ci gaban harkar noma a Sakkwato, ya ce za a yi irin wannan yunqurin a Jihar Kano.

“Yana da kyau mu ci gaba da inganta abubuwan da muke nomawa. A arewa muna noma citta da waken soya da zovo da sauransu, kamar yadda qasar Libiya take da gwanda, yanzu mun tasam ma zama qasa mafi girma da ke noman shinkafa a Nahiyar Afirka.

Mun riqe wannan matsayi a shekarar 2018 inda muka doke qasar Masar. Yanzu Masar ce ke neman mu kai mata shinkafa, za mu iya ciyar da su amma sai mun fitar da tsarin da ya dace. Amma harkokin siyasa sun sha gabanmu saboda da muhimmncin da muka ba su,” in ji Ogbe.

Tsohon ministan ya qare da cewa akwai wata rana da za ta zo da za a nemi wani babban manomin shinkafa ko mai sarrafa ta ya shiga siyasa ya qi.

A makon jiya mun ruwaito

cewa Mataimakin Shugaban Qasa Yemi Osinbajo ya buxe wani katafare aikin noman rani na Naira biliyan 27 a Jihar Kano.

Shirin noman ranin haxin gwiwa ne a tsakanin Gwamntin Tarayya da Bankin Duniya a qarqashin shirin TRIMiNG da

KRIS, inda aka fitar da hanyoyin ruwa da samar filayen noman rani mai faxin gaske.

Ana sa rai shirin zai samar wa manoma masu yawa filayen noman rani da kuma wasu qarin mutane da ake sa ran shirin zai taimaka su samu abin yi.

TUNA BAYA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282050511436768

Media Trust Limited