dailytrust

Shin ko Manchester City za ta lashe Gasar Zakarun Turai bana?

Daga Isiyaku Muhammed

Amakon jiya ne Qungiyar Manchester City ta lashe kofin Firimiya ta Ingila bayan Qungiyar Nottingham Forest ta doke Qungiyar Arsenal da ci xaya mai ban haushi, qwallon da xan Najeriya Taiwo Awoniyi ya jefa a ragar Arsenal a gidanta.

Wannan nasarar ce ta ba Qungiyar Man City damar lashe gasar Firimiyar Ingila karo na shida, sannan shi ne kofi na 12 da Pep Guardiola a zamansa a qungiyar, sannan yana shirin lashe biyu; na qalubale da zai buga wasan qarshe da Qungiyar Man United a ranar 3 ga Yuni a filin wasa na Wembley da na Zakarun Turai da za su buga da Qungiyar Inter Milan da za a buga a ranar 10 ga Yuni.

A wasa 35 da Man City ta buga a bana, ta samu nasara a 27, inda ta zura qwallo 92, sannan ta samu maki 85.

Haka kuma da wannan nasarar, Man City ta lashe kofin Firimiya na Ingila sau uku ke nan a jere, wanda a tarihin gasar qungiyoyi huxu ne kawai suka tava irin haka, sai yanzu qungiyar ta zama ta biyar.

Qungiyoyin su ne; Huddersfield Town (1924 zuwa 1926) da Arsenal (1933 zuwa 1935) da Liverpool (1982 zuwa 1984) da Manchester United (1999 zuwa 2001 da 2007 zuwa 2009).

Sai dai a kullum ana jifan qungiyar da magana xaya; sun daxe suna lashe Firimiya ta Ingila tun kafin zuwan Guardiola, yaushe za su lashe Gasar Zakarun Turai?

Masu sharhi a kan harkokin qwallon qafa suna cewa dama asali an kawo Guardiola ne domin lashe Gasar Zakarun Turai ba don Firimiya ba domin ko kafin zuwansa qungiyar ta lashe Firimiya ba xaya ba ba biyu ba.

Da yake jawabi bayan lashe Gasar Firimiya ta bana, Pep Guardiola ya ce lashe Gasar Zakarun Turai ne kaxai zai xaga darajar qungiyar sama da yadda take a yanzu.

Ya ce, “Wannan qungiya da ’yan wasan da muke da su a yanzu masu qoqari ne sosai, kuma qungiyar na tashe matuqa. Amma ni ma na amince cewa idan muna so mu nuna matuqar bajinta, dole sai mun lashe Gasar Zakarun Turai kamar yadda mutane suke faxa wanda hakan ne zai sa qungiyar ta shiga cikin sa’o’inta na duniya.”

“Za mu ci gaba da fafutikar lashe Gasar Firimiyar Ingila. A kakar baxi da qarfinmu za mu shiga domin ba za mu gajiya ba. Ko a kakar bara a wasan kusa da qarshe aka cire mu a Gasar Zakarun Turai, sannan bana muka sake zage damtse, ga shi bana mun kai wasan qarshe. Dukkan qungiya mai nagarta ba ta gajiya da neman nasara. Don haka muna neman qari ne.”

Wannan nasarori da qungiyar take samu ana alaqanta su da magance matsalarsu ta kakar bara ta rashin nagartaccen xan wasan gaba, wanda suka samu bayan xauko Erling Haaland.

Aminiya ta ruwaito a farkon kakar bana, inda a wasan farko da Manchester City ta buga, ta doke Qungiyar West Ham da ci 2-0.

Sai dai abin da ya fi jan

hankalin mutane shi ne yadda matashin xan wasan, Erling Haaland ya kasance shi ne ya zura qwallo biyun a wasan.

Magoya bayan qungiyar sun je kallon wasan ne da zullumi, ganin fitaccen xan wasan ya gaza a wasansa na farko, inda Qungiyar Liverpool ta doke Manchester City a wasan Kofin Community Shield, wanda hakan ya sa wasu suke tunanin ko an yi sayen tumun-dare ne.

Sai dai wannan lokaci ne xan wasan yake ta ’yar gala-gala da gololin qungiyoyin Firimiya, inda a bana ya zura qwallo 52 a wasa 49 da ya buga.

Daga cikin qwallayen da ya zura, akwai qwallo 36 da ya zura a Firimiya, sannan ya zura qwallo 12 a Gasar Zakarun Turai duk da cewa ba a kammala gasannin biyu ba.

Dama xan wasan da Mbappe ne dama ake tunanin za su maye gurbin Messi da Ronaldo nan da xan lokaci kaxan ganin yadda suke jan zarensu a yanzu.

A kakar bara, xan wasan ya zura qwallo 62 a wasa 67 da ya buga a Qungiyar Dortmund ta qasar Jamus, wanda hakan ke nuna bajintarsa.

Matashin xan wasa ne da ya qware wajen jefa qwallo a raga, sannan qungiyar Man City a qarqashin jagorancin Pep Guardiola tana nuna qwarewa wajen taka leda da nemo hanyoyin zura qwallaye, amma a lokuta da dama a varnatar.

WASANNI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282076281240544

Media Trust Limited