dailytrust

Amsoshin tambayoyi

Me ke kawo ciwon kansa ne ga mata?

Daga Baban Yusuf

Amsa: Wani malaminmu ya ce rashin sa’a ne kawai ke kawo ciwon kansa ko daji ga xan Adam. Domin a mata za ka ga ciwon daji na mama ya fi kama mata masu qiba waxanda ba su haihu da yawa suka shayar ba, amma kuma akwai mata masu qiba da dama da ba su haihu sun shayar ba, suna nan ba su da ciwon kansa, kuma su suka fi yawa. Sai ciwon kansa na bakin mahaifa wanda shi kuma qwayar cutar virus ta human papilloma virus ce ke kawo shi.

Da gaske ne mabiyiyar jariri na iya vallewa daga jikin mahaifa?

Daga Amina S. N.

Amsa: Eh da gaske ne. Wannan na faruwa sosai ga mata masu juna biyu masu hawan jini waxanda ba sa shan maganin rage hawan jinin. Bayan ciwon jijjiga matsalar tsinkewar mabiyiya daga jikin mahaifa ita ce ta fi shafar su. Alamun da za su ji kuwa su ne na ciwon ciki da murxewar ciki da zubar jini sosai ba qaqqautawa. Dole a je asibiti domin ceto rayuwar uwa da jariri idan irin wannan ta faru.

Ban da hawan jini kuma akwai bugu ko naushi a ciki da wasu maza kan yi wa mata masu juna biyu, shi ma zai iya sa wannan matsala, don haka su daina. Sai kuma buguwa a ciki kamar a wani haxari na abin hawa.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281651079478240

Media Trust Limited