dailytrust

…Dubban mutanen Sudan na neman mafaka a Chadi

Mutum dubu 60 zuwa dubu 90 ne Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Xinkin Duniya (UNCHR) ta ce sun gudu daga Sudan zuwa qasar Chadi bayan rikici ya varke a qasar a tsakiyar watan Afrilu.

Haka kuma Hukumar

UNCHR ta ce sama da mutum dubu 250 ne suka fice daga qasar da ke fama da rikicin shugabanci, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen mata ne da qananan yara, kuma ana sa ran adadin na iya qaruwa.

A wata ziyarar gani da ido da wani babban jami’in hukumar Raouf Mazou ya kai qasar Chadi ya ce, akwai buqatar samar wa ’yan gudun hijirar da ke isa Chadi matsugunai a yayin da damina ke shirin kankama.

A ranar Litinin ce aka cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin vangarori biyu na masu fafatawa a Sudan, sai dai babu tabbacin ko za su mutunta wannan yarjejeniyar kamar yadda aka gani a baya. Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa sun jiyo amon harbeharbe a sararin samaniyar birnin Khartoum, jim kaxan da fara aiki da yarjejeniyar.

TARE DA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281934547319776

Media Trust Limited