dailytrust

Gata Tinubu zai zama angon Najeriya na 16

Muhimman vangarorin da ke buqatar xaukin gaggawa daga gare shi

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Ayayin da gata Litinin, 29 ga Mayun ne za a rantsar da sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda zai karvi mulki daga Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, qwararru da masu ruwa-da-tsaki a muhimman sassan qasar nan sun nuna Shugaban Qasar na 16 alqiblar da ya kamata ya bi don kaiwa ga nasara.

Mutanen qasar nan na haba-haba Tinubu ya karvi mulki saboda alqawuran da ya xauka na magance ximbin matsalolin da suke addabar qasar nan.

Muhimman matsalolin da qwararru suka ce suna buqatar xaukin gaggawa daga Tinubu sun haxa da tsaro da tattalin arziki da lantarki/makamashi da hanyoyi da kiwon lafiya da ilimi da kuma noma.

Tsaro

Babban abin da masana suna buqaci Tinubu ya fara magancewa shi ne rashin tsaro, wanda ya qunshi ta’asar ’yan bindiga da garkuwa da mutane da ta’addanci da satar mai da yunqurin vallewa daga qasa da faxace-faxacen ’yan qungiyoyin asiri da rikicin manoma da makiyaya da rikicin qabilanci da damfarar Intanet da sauransu.

Kowace daga cikin shiyyoyin siyasa shida na qasar nan na fama da irin tata matsalar tsaron duk da tsoma sojoji a cikin lamarin a tsawon shekaru.

Misali wasu jihohi a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya suna fama da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga, yayin da Neja-Delta ke fama da varayin mai. Sannan bincike ya nuna har yanzu ’yan ta’adda na tafka varna a Arewa maso Gabas.

Cire tallafin mai da matsalar wutar lantarki Cire tallafin mai da matsalar wutar lantarki

Cire tallafin man fetur da rage farashi ko qara kuxinsa na cikin manyan matsalolin da suke jiran Tinubu. Yanzu dai ana sayar da lita xaya a kan Naira 190.

Gwamnatin Buhari ta kasa cire tallafi A vangaren wutar lantarki wajibi ne sabon Shugaban Qasar ya nemo hanyar qara qarfin wutar lantarki zuwa sama da megawatt 4,500 da aka fi samu a qasar nan wanda hakan ke kawo qaranci da ingancin wutar lantarki.

Gwamnatin Buhari a bayan nan ta faxaxa wani kwamiti don ya qunshi wakilan gwamnati mai zuwa kan batun cire tallafin mai a bayan Yuni mai zuwa waa xaya bayan Tinubu ya karvi mulki.

Gwamnatin Buhar ta ce ta kashe Naira tiriliyan shida kan bayar da tallafi a cikin wata 18, amma duk da haka ’yan Najeriya na fama da wahalar mai a sama da shekara xaya.

Masana sun ce abu ne mai wahala ga Tinubu ya ci gaba da bayar da tallafin alhali bai bayar da cikakken ’yanci ga vangaren fetur ba, inda a yanzu Kamfanin NNPC ne kaxai yake shigo da mai.

Sai dai akwai yiwuwar buxe matatar Xangote ta rage raxaxin da ake sha a fannin mai, bisa sa ran NNPC zai riqa sayen man daga matatar maimakon qasashen waje.

Bashin Naira tiriliyan 77

Wani babban qalubalen da Tinubu zai fuskanta shi ne na adadin bashin da ake bin Najeriya a ciki da wajenta wanda ya

Bola Ahmad Tinubu kai Naira tiriliyan77.

46.25 a cikin zango na 4 a bara, kuma bashin ya qaru daga Naira tiriliyan 44.06 daga zango na 3 a bara, kamar yadda Hukumar Qididdiga ta Qasa (NBS) ta fitar a rahotonta na kwata-kwata mai taken “Yawan bashin cikin gida da waje a qarshen bara.

Sai dai a yanzu Majalisar Dokoki ta Qasa ta amince a karvo bashin Naira tiriliyan 22 ta hannun Bankin CBN.

Kasafin Kuxin 2023 kuma an yi shi ne da givin kimanin Naira tiriliyan 10 wanda a qarshe zai iya yin tashin gwauron zabo, ya ninka zuwa kusan Naira tiriliyan 77 idan sabuwar gwamnati ta zo.

A kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta aro Naira biliyan 366 daga Bankin Duniya don sauqaqa illar da cire tallafin mai zai haifar, wanda a yanzu aka dakatar da shi.

Qidayar jama’a

A kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya amince da xage aikin qidayar 2023, wadda tun farko aka shirya gudanarwa a ranar 3 zuwa 7 ga Mayun nan, inda ya bar wa gwamnati mai jiran gado wuqa da naman tantance ranar da za a gudanar da aikin.

Wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar ta ce, Shugaban Qasa ya amince da xage ranar ce bayan taron Majalisar Zartarwa da ganawa da Shugaban Hukumar Qidaya ta Qasa da ayarinsa a Abuja.

Hukumar NPC da ke gudanar da qidayar, ta tabbatar akwai sauran na’urori da take buqata don gudanar da aikin, inda ta ce nan da ’yan kwanaki za a sayo wasu na’urorin.

Don haka, sabon Shugaban Qasa ne zai tantance lokacin da za a yi qidayar.

Lokaci na qarshe da aka yi qidayar jama’a a Najeriya shi ne a shekarar 2006, wanda ya nuna yawan al’ummar qasar nan ya kai miliyan 180.

Sai dai rahoton Yawan Jama’a na Majalisar Xinkin Duniya ya qiyasta cewa, adadin al’ummar Najeriya zai haura miliyan 223.8 nan da tsakiyar shekarar 2023 daga miliyan 216 a shekarar 2022.

Sake fasalin Naira

A watan Oktoban 2022, CBN ya sanar da sake fasalin wasu takardun Naira. Babban Bankin ya sake fasalin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000, lamarin da ya jefa al’umma cikin wahalhalu.Babban Bankin ya qudiri aniyar sake fasalin kuxi ne kafin zaven Shugaban Qasa na 2023, inda har ta kai xan takarar Shugaban Qasa na Jam’iyyar APC a lokacin, Bola Tinubu ya zargi wasu masu riqe da madafun iko da amfani da sake fasalin Nairar da kuma qarancin man fetur wajen kawo wa burinsa na son zama Shugaban Qasa cikas.

Duk da an kawo qarshen matsalar, amma za a xauki tsawon lokaci ba manta ba.. Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin matakin da gwamnatin Tinubu za ta xauki a kan wa’adin ranar 31 ga Disamba na daina amfani da tsofaffin kuxin kamar yadda Kotun Koli ta yanke hukunci.

Rashin aikin yi

A cewar Hukumar Qididdiga ta Qasa, rashin aikin yi a Najeriya ya kai kashi 33 cikin 100.

Sai dai Kamfanin Binciken Kuxi na KPMG ya ce, rashin aikin yi a Najeriya ya qaru zuwa kashi 37.7 cikin 100 a shekarar 2022 kuma zai iya qaruwa zuwa kashi 40.6 cikin 100, saboda qaruwar da ake samu ta masu neman aiki.

Duk da cewa gwamnati mai ci ta vullo da tsare-tsare daban-daban na inganta kasuwanci da sana’o’in hannu, kamar shirin N-Power da shirin qarfafa wa ’yan kasuwa da sauransu, babban tasirin da ake sa ran zai yi ga ci gaban tattalin arzikin bai taka kara ya karya ba.

Don haka, sabuwar gwamnati tana iya samar wa al’ummarta ayyukan yi cikin qanqanin lokaci don rage raxaxin talauci da daqile shiga ayyukan manyan laifuka.

Inganta noma

Qwararu a wananan fanni sun bayyana cewa, Shugaban Qasa mai jiran gado yana buqatar ya mayar da hankali kan abubuwa shida da suka zama qalubale ga noma kuma suka hana harkar kaiwa ga ci a qasar nan.

Abubuwan da zai tunkara sun haxa da shawo kan matsalar taki da kuma rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya. Haka kuma dole ne a samar wa manoma hanyar samun kuxi da kuma qara inganta kayayyakin noman rani da samun qaruwar kayan aikin gona na zamani.

Manoma da masu ruwa da tsaki sun amince cewa, waxanan abubuwa su ne suka zame wa ci gaban ayyukan gona tarnaqi tare da mayanr da hannun agogo baya.

Kabiru Ibrahim shi ne Shugaban Qungiyar Manoma ta Qasa AFAN ya bayyana cewa, akwai buqatar a qarfafa wa manoma gwiwa kan yin noma a gabaxayan shekara ta hanyar zuba jari a harkar noman rani da kuma samar da kayan aikin noman. T haka ne kawai gwmanati mai jiran gado za ta samu kai wa gaci a vangaren aikin gona.

“’Ya kamata gwmanati mai shigowa ta mayar da hankali wajen gano irin qarfi da kuma abin da kowane yanki na faxin qasar nan zai iya samarwa. Haka kuma ta yi qoqarin rage musu kuxin duk wasu kayayaykin noma da suke buqata”

Dukkanin qabilun da ke yankuna shida na faxin qasar nan ya kamata su zauna su kimanta kawunansu don gano hanyar da za su bi wajen ganin an riqa samar da kayyayakin aikin noma. Hakan zai sa manoma su san ana yi da su a shekarun farko an mulkinsa.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Qungiyar Manoman Dankali ta Qasa Cif Dan Okafor ya bayyana cewa, akwai buqatar gwamnatin ta mayar da hankali kan harkar tsaro da wutar lantarki da harkar noman rani da samar da hanyoyi a karkara da samar da tsarin inshora ga manoma.

Shi kuwa wani masanin tattalin arziki mai suna Mista Dele Adebisi ya bayayan cewa, dole gwamnati mai zuwa ta duba hanyoyin da za a tabbatar cewa manoma sun samu kayan noma, inda ya ce samuwar isassun kayan aiki zai janyo raguwar kuxin da ake kashewa a harka noma.

Aikin titin Kaduna zuwa Abuja

Wani muhimmin aiki shi ne aikin Kaduna zuwa Abuja, wanda asali ya fara ne daga Abuja zuwa Kano. A ranar Talata da ta gabata ce Shugaba Buhari ya qaddamar da vangaren aikin na Kaduna zuwa Kano, inda ya gadar da qarasa aikin na Kaduna zuwa Abuja ga sabuwar gwamnati.

Aminiya ta ruwaito cewa, aikin na tafiya sosai a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda a kusan kullum ma’aikan suke aiki ba-ji-bagani.

Titin jirgin qasa Kaduna zuwa Kano

A watan Yulin 2021 ne aka qaddamar da aikin titin jirgin daga Kaduna zuwa Kano, sannan akwai vangaren aikin titin jirgin qasan Abuja-Kaduna-Kano da ba a kammala ba. Shi ma wannan aikin yana cikin ayyukan da ke buqatar kulawar gaggawar sabuwar gwamnati.

An samu qarin bayani daga Sunday M. Ogwu da Simon E. Sunday da Ojoma Akor da Vincent Yusuf da Chidimma C. Okeke da Idowu Isamotu da Muideen Olaniyi da kuma Faruk Shuaibu.

FRONT PAGE

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281505050590176

Media Trust Limited